Caliphate Ambassadors Initiative

Caliphate Ambassadors Initiative It is a group that struggled to demonstrate the significant role Islam played in the establishment a
(1)

18/10/2025

Kasa Yaronka Private School inda ake biyan kuɗaɗe masu yawa kaman haka:

1- Kowani term sai kabiya mashi School fees aƙalla ₦10000 zuwa 15000

2- Kuɗin Uniform, Games Wear, Jakka, Takalmi, Sucks suma aƙalla zasu iya kaiwa ₦25000

3- Bayan kowani shekara sai kacanza mashi Text Books da aƙalla kuɗinsu zekai kimanin ₦15000

4- Kullun sai ka kashe mashi kusan ₦1500 zuwa 2000 A lunch box ɗinshi kuɗin indomie, ƙwai da bobo.

5- Akowace Rana sai kabiya mashi kuɗin mashin aƙalla ₦500 ko 600

6- Sannan kuma duk shekara sai biya kuɗin graduation gown aƙalla ₦2000 ko ₦30000

7- Idan akayi hutu kuma kaɗaukar mashi lesson Teacher wanda aƙalla kana biyanshi ₦15000 ko 20000

Amma common ₦1500 kuɗin Islamiyya dazaka biyama yaronka domin yasamu ilimin ADDINI sai kadinga kwarmato kana miyagun maganganu kana ciwa mallaman islamiya sun cika son kudin ko in anyi magana ire irenku ne gaba gaba wajen cika baki akan lamarin ADDINI.

Duk Wanda Ze Koyar Dakai Alqur'ani a Duniyar Nan Baka Da Kamar Shi
Ya Allah Ka Sakawa Malaman Mu Da Gidan Aljannah🤲

SABUWAR ANNOBA 🔥Akwai wasu MATA MASIHIRTA dake ƙwanƙwasa GIDA-GIDA (a lokacin da Maza s**a fita kasuwa / Aiki) matuƙar k...
30/07/2025

SABUWAR ANNOBA 🔥

Akwai wasu MATA MASIHIRTA dake ƙwanƙwasa GIDA-GIDA (a lokacin da Maza s**a fita kasuwa / Aiki) matuƙar kika buɗewa ɗayan su ƙofar GIDANki zata Umurce ki da kuje cikin GIDAn ki TATTARO mata duk wani abu ABU DA TAKE SO ba tare da kin mata GARDAMA ba.

:

💥Mu ƙara riƙo da Sunnah (Addu'oin Neman Tsarin ALLAH) waɗanda ANNABIMUHAMMAD (Sallahu Alayhi wa Sallam) ya koyar da mu (Safe da Marece) 💯📌

💥Mu tilastawa IYALAN mu a kowane irin HALI suke sai sun yi Azkar (SAFE DA MARECE)

💥 Daga ƙarshe a duk lokacin da za'a buɗe ƙofar gida idan anyi Sallama to a tabbatar an karanta ɗaya daga cikin waɗanan Addu'oin:💥

34
اللَّهُمَّ إِنِّي أَعْوذُ بِكَ مِنَ الهَمِّ وَ الْحَزَنِ، وَالعَجْزِ وَالْكَسَلِ، والبُخْلِ والْجُبْنِ، وضَلَعِ الدَّيْنِ وغَلَبَةِ الرِّجَالِ
(Bukhari)
36.
حَسْبُنَا اللَّهُ وَنِعْمَ الوَكِيلُ
(Bukhari)

38.
اللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ الأَحْزَابَ، اللَّهُمَّ اهْزِ مْهُمْ وَزَلْزِلْهُمْ
(Muslim)
39.
اللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ
(Muslim)
104.
أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ
(Muslim)

💥Kada a manta da Basmala da Isti'aza💥

🫆Dukkanin waɗanan Addu'oin suna a littafin Hisnul Muslim a duba a waɗanan lambobin In Sha Allah za'a samu🫆

Wasu zasu kalli wannan Labarin tamkar Almarah (sai lokacin da abun yazo kusa da su) azo ana NADAMA.

ALLAH ya ƙara kare mu da Al-ummar dukkanin ANNABI MUHAMMAD (Sallahu Alayhi wa Sallam) 💚Alfarmar Dukkanin Sunaye da Siffofin ALLAH Kyawawa💚 AMEEN 🤲🏻

Tsaya ka karanta DON GIRMAN ALLAH 🤲🏻Assalamu Alaykum wa RahmatulLah.Farantawa ALAH ta hanyar Farantawa BayinSa (JalLah J...
24/07/2025

Tsaya ka karanta DON GIRMAN ALLAH 🤲🏻

Assalamu Alaykum wa RahmatulLah.

Farantawa ALAH ta hanyar Farantawa BayinSa (JalLah Jalalu)

Ƴan uwa wanan wata Boyar ALLAH ce da ake kyautata zaton ƴar Shiyar GUIWA nan Jahar SOKOTO tana buƙatar taimakon mu.

- Mu taimaka mu yaɗa wanan post ko ALLAH yasa ƴan Uwanta / Makusantan ta su gani su kawo ɗauki.

A halin yanzu tana zaune a garin WURNO LGA Sokoto.

Duk da halin da wanan Boyar ALLAH take ciki SAM BATA ZAMA cikin ƙazamta ko ruwa bata sha sai PURE WATER (masu tsafta) balantana Abinci maras Inganci.

MAGANA ma idan anyi mata sai ta gadama take amsawa, ana kyautata zaton ALJANNU ne ke magana a madadin ta.

Alhamdulillah duk an samu wasu zaratan BAYIN ALLAH (ƴan sa kai) Jimi-Jimi suna kula da motsinta.

09063676758
08056582550
07061646273
09033552548

Muna roƙo don GIRMAN ALLAH wanda duk yaga wanan post ya yaɗa ko ALLAH yasa ƴan uwanta su gani.

Allah Ubangiji ya zama gatanta ya yaye mata dukkanin Damuwarta.

15/06/2025

Kira da Jankunne akan: Faɗan da ya ɓarke tsakanin ƙasar Iran 🇮🇷 da kuma Israel 🇮🇱

Duk da bamu tare da ƙasar Iran 🇮🇷 a Aƙida, amma muna yi masu Fatan samun GAGARUMAR NASARA akan ƙasar Israel 🇮🇱

Allah ya baiwa Iran 🇮🇷 nasara Ameen

04/06/2025

*JADAWALIN YADDA ZA KA RIBACI RANAR ARFA,
GA SHI NAN KAMAR HAKAN :-

1. Bayan Ka yi barci a kan lokaci
2. Ka tashi Ka samu falalar sahur
3. Ka yi addu'a kafin alfijir ya keto
4. Ka yi Istigfari Ka nemi tuba
5. Ka halarci sallar Asuba cikin jam'i
6. Ka zauna bayan salla kana azkar
7. Ka daure cikin Ibada har Rana ta hudo
8. Ka tashi Ka yi raka'a biyu Ka samu ladan Hajji da Umra
9. Ka Dan kishingida don samun karfin yin Ibada a wannan yini
10. Kana tashi Ka yi sallar Walaha, raka'a 4/6/8
11. Nau'anta salon Ibadarka;
yi salla
yi karatun Kur'ani
yi kabbara
yi addu'a
yi zikirai
12. Jeka sallar Azahar Ka yi "Sunan Rawatib" kafin salla da bayan salla
13. Samu lokaci Ka Kara karanta AlKur'ani
14. Ka yawaita Hailala "La'ilaha Illal Lahi Wahdahu La Sharika Lahu Lahul Mulku wa Lahul Hamdu wa Huwa ala Kulli Shai'in Kadir"
15. Halarci salla La'asar a jam'i,
16. Yi Azkar din yamma
17. Yi karatun Kur'ani har zuwa yamma likis
18. Koma ga addu'a, roki duniya da Lahira, Kada Ka roki duniya kadai
19. Yi addu'ar Ka zama cikin 'yantattun wannan yini
20. Ka kaskantar da kanka ga Allah, Kada ka yi zaton ka sha gaban wasu a wajen Allah don ibadarka
21. Yi buda Baki Ka Kara da addu'o'i ga kanka/iyalanka/yanuwanka/ Musulmi/ kasarka

Allah Ya karba mana kadan, Ya ba mu Mai yawa Ya Kareem.

🔵BAMU TALLAFIN SADAKAR FATUN KU NA LAYYA, DOMIN JADDADA ADDININ MUSULUNCI A KARKARA🔵  Haƙiƙa  sadaka tana ƙara kusanci a...
30/05/2025

🔵BAMU TALLAFIN SADAKAR FATUN KU NA LAYYA, DOMIN JADDADA ADDININ MUSULUNCI A KARKARA🔵

Haƙiƙa sadaka tana ƙara kusanci a gurin Allah (Subhanahu wa Ta'ala)

Muna neman tallafin sadakar fatun Layya, domin ƙara Inganta Shiraruwan mu na Daƙile mumunar manufar Kafurai da suke fafutukar canjawa ƴanƴan uwan mu Musulmi Addini zuwa Kafurci, Musamman a ƙauyukan mu (Karkara).

Babbar manufar mu, ƙara Jadda Addinin musulunci ga Al-ummar mu, akan koyarwar Mujaddadi Shehu Ɗan Fodiyo.

Ku taimaka ku bada naku tallafin, tare da turawa Masoyanku domin su su ribaci wanna aikin. 😊

Annabi Muhammad (Sallallahu alayhi wa Sallam) yace:
"مَنْ دَلَّ عَلَى خَيْرٍ فَلَهُ مِثْلُ أَجْرِ فَاعِلِهِ..."
Ma'ana:

Duk wanda ya taimaka aka aikata wani Alkhayri"
~Muslim.

Allah ya bamu ikon bada namu Tallafin domin neman yardar Allah 🤲🏻

28/05/2025
11/05/2025

Kasance Mai Bayar da (Alkhayri) Maimakon Wanda ake Baiwa Kyauta / Sadaƙa...

An ruwaito daga Abdullahi Ɗan Abbas yace:

"Yana daga cikin Sadaƙa UMURNI da Alkhayri, da HANI daga Munana, da GUSAR da damuwar wani, harma da kawar da wani Abun cutarwa a Hanya".

Allah ka sa mu kasance masu Amfanarwa ba masu Amfanuwa kaɗai ba AMEEN.

Barka da Safiya ☕️
MIJIN MACCE 🧕 🧕

27/03/2025

Address

Fodio Road
Sokoto

Telephone

+2347065649698

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Caliphate Ambassadors Initiative posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Caliphate Ambassadors Initiative:

Share