Mu Sada Zumunchi Multi-purpose Association Kwanni

Mu Sada Zumunchi Multi-purpose Association Kwanni Mu sada zumunchi multi-purpose Association kwanni.Domin taimak**a Marayu, tsofaffi da Zawarawa marasa karfi a cikin wannan anguwar da kewayenta

Mu Sada Zumunci Multipurpose Association, Kwanni paid a courtesy visit to the Director General of Media and Publicity, G...
30/07/2026

Mu Sada Zumunci Multipurpose Association, Kwanni paid a courtesy visit to the Director General of Media and Publicity, Government House Sokoto, Alhaji Abubakar Bawa, during which the association presented him with an Award of Appreciation in recognition of his outstanding support, generosity, and invaluable contributions to the activities and development of the association.

In his response, Alhaji Abubakar Bawa expressed his sincere appreciation for the honour bestowed upon him. He thanked Mu Sada Zumunci Multipurpose Association, Kwanni for the recognition and reaffirmed his commitment to continue contributing his quota towards the growth and progress of the association, as well as the overall development of the Kwanni community.

27/05/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.

A madadin daukacin mambobin Mu Sada Zumunci Multipurpose Association Kwanni, muna mika sakon taya murnar babbar Sallah ta Eid-el-Kabir ga al’ummar Musulmi baki daya.

Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya sanya wannan lokaci mai albarka na sadaukarwa, kauna, haɗin kai da biyayya gare Shi ya kawo zaman lafiya, cigaba da albarka ga gidajenmu, al’ummarmu da kasa baki daya.

Muna matuƙar yaba da irin jajircewa, goyon baya da gudummawar da dukkan mambobin kungiyar suke bayarwa wajen cigaba, haɗin kai da nasarar Mu Sada Zumunci Multipurpose Association Kwanni. Haƙiƙa haɗin kai da zumuncin da ke tsakaninmu na ƙara ƙarfafa dankon soyayya da ‘yan uwantaka.

Yayin da muke gudanar da wannan biki mai albarka, muna rokon Allah (SWT) ya karɓi ibadunmu da layyukanmu, ya saka mana da alkhairi mai yawa, sannan ya sa mu sake samun irin wannan lokaci cikin ƙoshin lafiya, zaman lafiya da wadata.

Barka da Sallah!

22/04/2026

Inna lillahi wa Inna lillahin raju'um😭 ubangiji ya jarrabci daya Daga cikin mombobin wnn gidan namu da gobara waton Mu'azu Abubakar p.r.o 1, a shagonshi dake kan titin bye pass inda dukkanin shagon ya kone ba abinda aka fita dashi muna rokon Allah ya mayarmasa da mafificin alheri yasa wnn ya zamo sanadin arziki ne amin kuma Allah ya tsare gaba

14/03/2026

Jafar AbubakarKasimu BelloSambo Ibrahim ChindoMu Sada Zumunchi Multi-purpose Association KwanniMuazu Abubakar SadaLadan BelloMuhammad Mustafa MuhammadZayyanu Alhassan AbubakarZayyanu BunuZaruku Abdullahi SokotoAbdulrazaq Lawal AliyuAbu Huzaifa Attahiru MainiyoProf. Isa Ali Pantami support organizationAzzubayr Sada AbubakarZayyanu AbubakarUmar A SokotoAbdullahi MusaAliyu Aliyu MustaphaAll Median Tv { AMT}MU SADA ZUMUNCI MULTIPURPOSE ASSOCIATION, KWANNI
Kungiyar Mu Sada Zumunci Multipurpose Association, Kwanni ta sanar da nasarar kammala shirin rabon kayan sawa da wasu kayayyakin masarufi ga marasa galihu a yankin Kwanni.
An gudanar da wannan shiri ne a ranar Asabar, 7 ga watan Maris, 2026, a Sakatariyar kungiyar, inda aka rabawa marayu, zawarawa, tsofaffi da malamai kayan sawa da sauran kayayyakin tallafi. Jimillar mutane sama da 650 ne s**a amfana da wannan shiri.
Shirin rabon kayayyakin ya kasance wani bangare na shirye-shiryen tallafin watan Ramadan na shekarar 1447AH / 2026, wanda kungiyar ke gudanarwa domin rage wa marasa karfi radadin rayuwa tare da kara inganta jin kai, hadin kai da zumunci a tsakanin al’umma.
Wadanda s**a amfana da tallafin sun fito daga sassa daban-daban na yankin Kwanni da kewaye a Jihar Sokoto. A yayin gudanar da shirin, an yi addu’o’i tare da kalaman godiya daga wadanda s**a amfana, inda s**a nuna matukar jin dadinsu da godiya ga wannan karamci da kulawa da kungiyar ta nuna musu.
An samu nasarar gudanar da wannan shiri ne ta hanyar hadin gwiwa da goyon bayan mambobin kungiyar, masu aikin sa kai da kuma masu fatan alheri, wadanda s**a bayar da gudummawa ta hanyoyi daban-daban domin tabbatar da nasarar wannan aiki na alheri.
Kungiyar tana mika cikakkiyar godiya ga wadannan mutane da s**a bayar da gudummawa ta kudi, kaya da addu’a domin ganin wannan shiri ya tabbata:
1.Alh. Abubakar Bawa – DG Media and Publicity, Government House Sokoto
2.Alh. Aliyu Umar – CEO, AUG Steel and General Enterprises
3.Alh. Murtala Brown
4.Prof. Murtala B. Abubakar
5.Alh. Abba Mai Burodi
6.Alh. Umar Hussaini
7.Alh. Auwalu Dan Haja
8.Kabiru Haruna
9.Ibrahim Sani
10.Nafi’u Malami
11.Babangida Alti
12.Alh. Ibrahim Martaba
13.Badamasi Bello (Small Head)
Kungiyar kuma tana yaba kwazo da sadaukarwar mambobin kwamitin zartarwa, dukkan mambobin kungiyar, da kwamitin tara kudade, wadanda s**a yi aiki tukuru domin ganin wannan shiri ya gudana cikin nasara.
Kungiyar Mu Sada

Assalamu Alaikum Amadadin daukacin membobin wannan kungiya mai albarka na gayyatar yan' uwa, abokan arziki da masu fatar...
06/03/2026

Assalamu Alaikum
Amadadin daukacin membobin wannan kungiya mai albarka na gayyatar yan' uwa, abokan arziki da masu fatar alkhairi domin halartar bukin kaddamar da rabon suturar sawa da kayan abinci ga marayu,zaurawa da tsofaffi a shiyar kwanni da kewaye.
Wuri: A harabar sakatariyal kungiya dake kusa ga ofishin marafan kwanni
Ranar: Assabar 7 ga watan Maris na shekarar 2026 / 18 ga watan Ramadan 1447AH
Lokaci: 10:00am

Azo lafiya.

06/03/2026

Assalamu Alaikum
Amadadin daukacin membobin wannan kungiya mai albarka na gayyatar yan' uwa, abokan arziki da masu fatar alkhairi domin halartar bukin kaddamar da rabon suturar sawa da kayan abinci ga marayu,zaurawa da tsofaffi a shiyar kwanni da kewaye.
Wuri: A harabar sakatariyal kungiya dake kusa ga ofishin marafan kwanni
Ranar: Assabar 7 ga watan Maris na shekarar 2026 / 18 ga watan Ramadan 1447AH
Lokaci: 10:00am na safe Allah ya bada ikon halarta Amin

Azo lafiya.

06/03/2026

Assalamu Alaikum
Amadadin daukacin membobin wannan kungiya mai albarka na gayyatar yan' uwa, abokan arziki da masu fatar alkhairi domin halartar bukin kaddamar da rabon suturar sawa da kayan abinci ga marayu,zaurawa da tsofaffi a shiyar kwanni da kewaye.
Wuri: A harabar sakatariyal kungiya dake kusa ga ofishin marafan kwanni
Ranar: Assabar 7 ga watan Maris na shekarar 2026 / 18 ga watan Ramadan 1447AH
Lokaci: 10:00am

Azo lafiya.

Muazu abubakar sada p.s1

19/02/2026

Falalar Taimakon Talakawa da Miskinai da Marayu da Zawarawa da Masu Rauni a Watan Ramadan

Watan Ramadan wata makaranta ce ta tausayi, jin ƙai da rabauta. A cikinsa ne zuciya ke laushi, imani ke ƙaruwa, kuma alheri ke ninkuwa. Daga cikin manyan ibadodin da ake ƙarfafawa a wannan wata, akwai taimakon talakawa da miskinai da marayu da zawarawa da masu rauni cikin al'umma. Wannan aiki yana haɗa ibadar zuciya da ta dukiya, yana kuma ƙara dankon zumunci a cikin al’umma.

Kusaka sadakan Ku na Watan Ramadan a asusun marayun

Allah Maɗaukaki Ya yabi masu ciyarwa saboda Shi, ba don yabo ko sakayya ba. Ya ce:

“Kuma suna ciyar da abinci, duk da suna son sa, ga miskini da maraya da fursuna. Suna cewa: ‘Muna ciyar da ku ne saboda neman yardar Allah; ba ma son wata sakayya ko godiya daga gare ku.’”
Al-Qur’an (Suratul Insān 76:8–9)

Haka kuma Allah Ya haɗa bayar da dukiya ga masu buƙata cikin ma’anar nagarta ta gaskiya:

“…kuma ya bayar da dukiya duk da ƙaunarta, ga dangi da marayu da miskinai…”
Al-Qur’an (Suratul Baqarah 2:177)

Wadannan ayoyi suna nuna cewa ciyarwa da tallafa wa masu rauni ba kawai alheri ba ne, hanya ce ta samun yardar Allah da tsarkake zuciya daga rowa da son kai.

Annabi ﷺ ya kasance mafi yawan kyauta, kuma ya fi ƙara kyauta a Ramadan. An ruwaito daga Ibn Abbas cewa:

“Manzon Allah ﷺ ya kasance mafi kyautar mutane, kuma ya fi kasancewa mai kyauta a watan Ramadan…”
Sahih al-Bukhari

Haka kuma ya ce:

“Ni da mai kula da maraya muna cikin Aljanna k**ar haka,” ya kuma haɗa yatsunsa biyu yana mai kwatance.
Sahih al-Bukhari

Game da zawarawa da miskinai kuwa, Annabi ﷺ ya ce:

“Mai kula da zawarawa da miskinai k**ar mai jihadi ne a tafarkin Allah, ko k**ar mai tsayuwar dare da mai azumi ba ya yankewa.”
Sahih Muslim
Wannan lada mai girma yana nuna matsayi da darajar wannan ibada a wajen Allah, musamman a wata da ake ninka lada k**ar Ramadan.

28/01/2026

Mu Sada Zumunchi Multipurpose Association kwanni, na mika godiyarsu ta musamman ga yan uwa dake bayar da tasu gudun muwa ta kudi ko suturar sawa ga marayu don ganin an share musu hawaye a wannan watan mai k**awa, Allah yasa k**a kowa da alherinsa yasa muyi tarraya a cikin lada Amin

Address

Kwanni Area Sokoto, Aliyu Jode Road Near Marafan Kwanni Office
Sokoto

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mu Sada Zumunchi Multi-purpose Association Kwanni posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share