02/04/2026
Copied
*MUHIMMIN SAƘO DAGA NDLEA*
Iyaye masu daraja,
Idan kuna da ‘ya’ya matasa, musamman waɗanda ke cikin shekarun balaga, ku fara lura da harshensu.
Musamman ‘ya’ya mata, idan kuka fara ganin canjin launi a harshensu akai-akai kamar shuɗi, rawaya, kore ko lemu (orange), ku sani cewa suna iya shiga shan wani miyagun ƙwayoyi mai suna Molly.
Molly tana sa mutum jin daɗi da annashuwa fiye da kima, tana iya sa mutum yin dariya ba tare da dalili ba, kamar wani irin hauka na wucin gadi.
Idan tasirin Molly ya bayyana, duk wanda ya taɓa yarinyar da ta sha wannan ƙwaya zai iya yin lalata da ita cikin sauƙi.
A yanzu haka, makarantu da tituna sun zama wuraren da ake yawan amfani da Molly.
Abin takaici, wasu ‘yan mata ma sun maida sayar da ita a matsayin kasuwanci.
Molly (M**A) ƙwaya ce haramtacciya, kuma farashinta ba shi da ƙayyadadden tsari.
A wani rahoto, an ce a shekarar 2022 ana sayar da kashi ɗaya na Molly a Najeriya da kusan ₦25,000.
A yau kuma, ta fi sauƙin samu a tituna da makarantu da farashin ₦2,000, ₦5,000, ko ₦10,000.
Hanyoyin amfani da ita sun haɗa da:
Wasu suna lasawa kamar Vitamin C
Wasu suna maida ita gari su ɗora a harshe a hankali
Wasu kuma suna narkar da ita a cikin ruwa
A halin yanzu tana daya daga cikin kwayoyin da ke lalata rayuwar matasa maza da mata.
Abin da ya fi muni shi ne, idan jiki ya saba da Molly, mutum zai fara neman wasu ƙwayoyi kamar Barky ko Crack domin ƙara ƙarfi, kuma kafin a ankara, yaron zai lalace gaba ɗaya.
Mu haɗa kai mu ɗaga murya domin yaƙi da wannan matsala.
Za mu iya rage ta, kuma za mu iya taimaka wa wasu su fita daga wannan hali.
Na gode, Allah Ya ci gaba da albarkace mu, Ya kuma shiryar da matasanmu.
SHAN MIYAGUN ƘWAYOYI MATSALA CE DA TA ZAMA RUWAN DARE A CIKIN AL'UMMARMU A YAU; MU TASHI MU YAKE TA TUN GABANIN TA IDA KASHE MATASANMU.