Malamin Aji

Malamin Aji Domin bada shawarwari akan Lafiya da Zamantakewa. For adverts and promotions, kindly contact us on WhatsApp: 07048758353
(1)

Idan ma’aurata sun yi shekara 3 da aure kuma suna yin jima’i ba tare da amfani da hanyar hana ɗaukar ciki ba amma ba a s...
31/08/2026

Idan ma’aurata sun yi shekara 3 da aure kuma suna yin jima’i ba tare da amfani da hanyar hana ɗaukar ciki ba amma ba a samu ciki ba, ana iya ɗaukar hakan a matsayin matsalar rashin haihuwa (infertility), kuma bai kamata a ci gaba da jira kawai ba. Ya kamata su fara cikakken bincike a wurin likitan mata ko fertility specialist.

Muhimmin abu shi ne a binciki miji da mata tare, domin matsalar na iya kasancewa daga ɓangaren namiji, mace, ko kuma duka biyun.

A wajen miji, daga cikin gwaje-gwajen farko akwai:

Semen Analysis domin duba yawan s***m, motsinsu da sauran ingancinsu.
Likita na iya ƙara gwajin hormones ko scrotal ultrasound idan SFA ya nuna matsala.
A wajen mata, ana iya duba:

Shin tana yin ovulation, wato fitar ƙwai?
Pelvic ultrasound domin duba mahaifa da ovaries.
Hormonal tests kamar TSH da prolactin, sannan sauran hormones gwargwadon ranar al’ada.
A duba ko fallopian tubes suna buɗe, musamman ta hanyar HSG, idan likita ya ga ya dace.
Wasu lokuta ana binciken mahaifa da sauran abubuwan da za su iya hana ciki.
Ba zai dace su ɗauka cewa matsalar daga mace ce kawai ko namiji kawai ba. Kuma bai kamata su dogara da maganin gargajiya ko supplements kawai ba tare da sanin ainihin dalili ba.

A shekara 3 ba tare da samun ciki ba, shawarar da ta fi dacewa ita ce ku je tare wajen Gynecologist/Fertility specialist su fara tsarin bincike. Da zarar an gano dalili, sai a san ko ana bukatar magani, gyaran matsalar hormones, tiyata idan akwai wani abu kamar varicocele ko matsalar tubes, ko kuma wasu hanyoyin taimakon haihuwa.

Kuma ku tuna: shekara 3 da rashin ciki ba yana nufin ba za ku taɓa samun haihuwa ba. Akwai dalilai da yawa masu magani, amma mataki na farko shi ne a gano ainihin dalilin.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

Har yanzu kana kashe kuɗi sosai wajen siyan data?

A StrongMB, zaka samu 1GB daga ₦300 kacal.

🎁 ₦200 Welcome Bonus
🎁 Saka MALAMINAJI a Invitation Code

🌐 Website 👇
https://strongmb.ng/malaminaji

📲 App 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.strongmb.app&referrer=MALAMINAJI

StrongMB — Data mai araha, babu ɓata lokaci.

Tambayar farko: ƙanƙantar kan nono (ni**le) ba lallai yana nufin akwai matsala ba. Girman nono da girman ni**le abubuwa ...
30/08/2026

Tambayar farko: ƙanƙantar kan nono (ni**le) ba lallai yana nufin akwai matsala ba. Girman nono da girman ni**le abubuwa biyu ne daban. Mace na iya kasancewa da manyan nonuwa amma ni**les ɗinta ƙanana. Haka kuma ni**le na iya canzawa ko ɗan fito wa a lokuta daban-daban saboda sanyi, taɓawa, motsawar jiki ko canjin hormones.

Lokacin pregnancy da bayan haihuwa kuma, hormones na iya sa nonuwa da ni**les su canza girma ko launi, sannan su ƙara fitowa. Amma ba lallai sai sun canza sosai ba. Idan nonon yana lafiya kuma babu ƙulli, ciwo mai ɗorewa ko wani ruwa/jini da yake fita ba tare da dalili ba, ƙanƙantar ni**le kaɗai ba matsala ba ce.

Game da tambayarka ta biyu, mace ba lallai sai ta yi ej*******on ko kuma ta fitar da wani ruwa domin a ce ta ji daɗin saduwa ko ta kai or**sm. Haka kuma jikewar farji na iya bambanta daga lokaci zuwa lokaci, kuma ba duk mace ce take jika sosai a kowane lokaci ba.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne idan tana jin daɗi ko kuma tana jin bushewa da zafi yayin saduwa. Idan tana jin bushewa ko ciwo, yana da kyau a ƙara lokacin wasanni da motsa sha’awa kafin saduwa, sannan idan ya zama dole za a iya amfani da water-based lubricant.

Game da ɗaukar ciki kuwa, rashin jikewa ko rashin ej*******on nata ba bazai hana ciki ba. Domin ciki yana samuwa ne idan maniyyin namiji mai ɗauke da s***m ya shiga farji sannan s***m ya kai ga ƙwai a lokacin da mace ke ovulation.

Saboda haka mace za ta iya ɗaukar ciki ko da ba ta ji or**sm ba, ba ta yi ej*******on ba, ko kuma ba ta ji jikewa sosai ba.

Amma tunda kana cewa tana jin kamar tana kaiwa or**sm ne bayan kun gama kuma kana fita daga jikinta, hakan ma yana iya faruwa. Wasu mata suna buƙatar motsawa ta wasu hanyoyi ko kuma suna kaiwa or**sm a hankali bayan an gama saduwa. Ba lallai hakan yana nuna matsala ba.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

🔥 1GB a ₦300 kacal!

Me yasa zaka siya a ₦600+ alhali zaka samu mafi arha a StrongMB?

🎁 ₦200 Welcome Bonus
🎁 Saka MALAMINAJI a Invitation Code domin ƙarin bonus

🌐 Website 👇
https://strongmb.ng/malaminaji

📲 App 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.strongmb.app&referrer=MALAMINAJI

StrongMB — Data mai araha, saurin aiki

29/08/2026

INA SON NAYI YI ƘARIN BAYANI GAME DA SAKONNIN NEMAN TAIMAKO DA WASU KUKE TURO MIN

KARANTA GABA DAYA.

Bayan posting ɗin da nayi na wata mata da gobara ta shafa, ina ta samun saƙonni marasa adadi, musamman daga bangaren mata, inda mutane da yawa suke turo min matsalolinsu suna roƙona da nayi musu posting domin a taimaka musu.

Ina matuƙar fahimtar halin da wasu daga cikinku suke ciki, kuma na san mutum ba zai so ya fito ya bayyana matsalarsa a gaban jama’a ba sai idan abubuwa sun kai shi wani matsayi. Don haka ba wai bana yarda da ku ko kuma ina ganin duk wanda ya turo min saƙon neman taimako ƙarya yake ba. A mafi yawan lokuta, duk wanda yake neman taimako akwai wata matsala da yake fuskanta.

Amma ina son a fahimci cewa, ba zai yiwu kullum shafi na ya zama wajen da aikinsa kawai shi ne neman taimako ga mutane ba. Na daɗe ina karɓar irin waɗannan saƙonni tun kafin posting ɗin da kuka gani, amma akwai dalilai da yawa da yasa bana iya yi wa kowa posting.

Ko ita ma wacce kuka ga nayiwa posting ɗin, akwai abubuwan da na duba kafin na yanke shawarar yi mata. Wannan ba yana nufin na fi yarda da ita fiye da sauran mutane ba, sai dai akwai abubuwan da s**a sa na ga ya dace a wannan lokacin.

Kuma wani abu da ya kamata a fahimta shi ne, wani lokaci mutum na iya kasancewa yana cikin matsala ta daban, amma saboda yana ganin idan ya faɗi wata matsala daban za ta fi sa mutane tausaya masa ko su taimaka masa, sai ya kawo wannan a matsayin dalilin neman taimako. Misali, mutum yana cikin matsananciyar yunwa, amma sai ya ce rashin lafiya ce ta sa yake neman taimako. Wannan ba yana nufin matsalar tasa ba ta da muhimmanci ba, saboda haka duk da kaga yana neman taimakon to gaske akwai abunda yake damun sa saidai ya sakaya ta wata sigar.

Saboda haka, ba wai bana son taimakawa ba ne, kuma ba wai ba zan iya yi muku posting ba ne. Sai dai kuma ba zan iya mayar da shafi na ya zama wajen da kullum aikinsa shi ne karɓar saƙonnin neman taimako da yin posting ɗinsu ba.

Gaskiya waɗanda s**a turo min saƙonni suna da yawa sosai. Don haka ku yi haƙuri da ni. Daga lokaci zuwa lokaci zan duba wasu daga cikin saƙonnin, kuma idan na ga wanda halinsa ya taɓa zuciyata ko kuma akwai wani dalilin da ya sa na ga ya dace a yi masa posting, zan iya yi masa, amma bazaiyu kullum ba.

Idan mutum yana cikin wani hali kuma emergency to akwai sahafuka na wasu influencers da suke wannan aikin sosai zasu zuwa chan domin ayi musu.

Ku kuma masu hali da Allah Ya h**e muku, idan kuka ga wani mutum yana cikin matsala kuma kuna da ikon taimaka masa, kada ku yi ƙasa a gwiwa wajen taimakawa. Tabbas anyi kokari akan waccan matar da tayi gobara.y Kuma ba tunda yaunzu an sha samun wadanda su da kansu suke fada mun idan akwai masu bukatar wani taimaiko akan wani bangare da s**an fada to a fada musu, kamar misali wanda ya tura 100k yace a rabawa mutum 5 a lokacin anyi hakan kuma aka tura masa shaidar an bawa wannan mutanen, to akwai irin su sai dai ace Allah ya saka musu.

Allah kara mana lafiya Ya biya mana dukkan bukatunmu, Ya yaye mana damuwarmu, Ya sauƙaƙawa waɗanda ke cikin ƙunci, Ya kuma sa mu kasance cikin waɗanda ke taimakon junansu. Amin.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

Babban abin da yakan jawo matsanancin ciwon mara lokacin period shi ne ƙara yawan wani sinadari mai suna prostaglandins ...
29/08/2026

Babban abin da yakan jawo matsanancin ciwon mara lokacin period shi ne ƙara yawan wani sinadari mai suna prostaglandins a lokacin haila. Wannan sinadari yana sa mahaifa ta riƙa matsewa domin fitar da jinin haila, kuma idan matsewar ta yi ƙarfi sai ciwon mara ya yi yawa. Wannan shi ake kira primary dysmenorrhea.

Amma idan ciwon ya yi tsanani sosai, ya fara ne bayan shekaru da dama ba tare da irin wannan matsalar ba, ko yana ƙara tsananta daga wata zuwa wata, akwai wasu cututtuka da ya kamata a bincika kamar endometriosis, adenomyosis, fibroids, ko pelvic infection.

Idan ciwon yana hana ta yin ayyukanta na yau da kullum, yana sa ta kasa zuwa aiki/makaranta, ko magungunan rage ciwo ba sa taimakawa, ya dace ta ga likitan mata domin a gano dalilin.

A gida, heat pad ko kwalbar ruwan ɗumi a ƙasan ciki na iya rage ciwo. Ana kuma amfani da magungunan NSAIDs kamar ibuprofen ga wadda ba ta da ciki, ulcer, kidney disease ko wani dalilin da zai hana amfani da su.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

Shin har yanzu kana siyan Data 1GB a ₦600+?

A StrongMB, zaka samu 1GB daga ₦300 kacal — mai arha, mai sauri, kuma mai inganci.

🎁 Da zarar kayi register zaka samu:
• ₦200 Welcome Bonus
• Ƙarin bonus idan ka saka MALAMINAJI a wajen Invitation Code

🚫 Babu cajin ₦50 idan ka saka kuɗi ta wannan link.

🌐 Website:
https://strongmb.ng/malaminaji

📲 App:
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.strongmb.app&referrer=MALAMINAJI

StrongMB — Data mai araha, saurin aiki, babu ɓata lokaci.

Duk me bukatar taimakon ta ga information dinta nan
28/08/2026

Duk me bukatar taimakon ta ga information dinta nan

Akwai wasu abubuwa da mutane s**a saba faɗa game da nonon mace amma ba duka suke da hujjar kimiyya ba.1. Shin yawan taɓa...
26/08/2026

Akwai wasu abubuwa da mutane s**a saba faɗa game da nonon mace amma ba duka suke da hujjar kimiyya ba.

1. Shin yawan taɓa nono ne yake sa ya zube?

Yawan taɓa nono ko tsotsa ba shi ne babban dalilin da ke sa nono ya zube ba, ko mace budurwa ce ko matar aure.

Abubuwan da s**a fi iya sa nono ya sauya ko ya zube sun haɗa da:

shekaru da tsufar fata;

gado/genetics;

girman nono;

pregnancy da sauyin girman nono;

yawan ƙaruwa da rage kiba;

wasu sauye-sauyen hormones.

Don haka ba daidai ba ne a ce idan budurwa nononta ya zube to tabbas yawan taɓa nonon ne ya jawo.

2. Shin duk nonon mace dole sai yana da taushi?

A’a. Nono yana da haɗin fat, glandular tissue da sauran tissues, saboda haka taushinsa yana iya bambanta daga mace zuwa mace.

Wasu nonuwa suna da taushi sosai, wasu kuma suna ɗan dauri ko firm. Hakan na iya zama normal. Haka kuma, nono guda ɗaya na iya ji daban da ɗayan.

3. Shin idan nono ya zube ne yake zama ba shi da taushi?

Zubewar nono da taushinsa abubuwa biyu ne daban. Nono na iya zubewa amma ya kasance mai taushi, haka kuma wanda bai zube ba yana iya kasancewa firm.

A takaice: taɓa nono ba shi ne yake sa nono ya zube ba, kuma babu wani doka cewa duk nonon mace dole sai yana da taushi iri ɗaya. Girma, siffa, taushi da yadda nono yake ji sun bambanta daga mace zuwa mace kuma suna iya canzawa da hormones.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

Jinin al’ada yana fitowa ne daga mahaifa, amma ba wai jinin yana zama a cikin mahaifa ba.A duk wata, bangon cikin mahaif...
24/08/2026

Jinin al’ada yana fitowa ne daga mahaifa, amma ba wai jinin yana zama a cikin mahaifa ba.

A duk wata, bangon cikin mahaifa (endometrium) yana kauri domin ya shirya karɓar ciki. Idan ciki bai samu ba, sinadaran hormones suna raguwa, sai wannan bangon ya rushe ya fita ta bakin mahaifa (cervix) sannan ta farji. Wannan shi ne jinin al’ada.

Saboda haka, asalin jinin al’ada yana da alaƙa da bangon mahaifa, sannan yana bi ta cervix zuwa farji ya fito waje.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

Shin har yanzu kana siyan Data 1GB a ₦600+?

A StrongMB, zaka samu 1GB daga ₦300 kacal — mai arha, mai sauri, kuma mai inganci.

🎁 Da zarar kayi register zaka samu:
• ₦200 Welcome Bonus
• Ƙarin bonus idan ka saka MALAMINAJI a wajen Invitation Code

🚫 Babu cajin ₦50 idan ka saka kuɗi ta wannan link.

🌐 Website:
https://strongmb.ng/malaminaji

📲 App:
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.strongmb.app&referrer=MALAMINAJI

StrongMB — Data mai araha, saurin aiki, babu ɓata lokaci.

23/08/2026

Masu wasa gaban su sun yawaita, kuma da gaske suke yi. Mene yake kawo hakan ne kuma ta yaya za a magance faruwar hakan?

Update
23/08/2026

Update

Anya da gaske kake kuwa, ta yaya mutum zaiyi ma********on har sau 50 🤔
23/08/2026

Anya da gaske kake kuwa, ta yaya mutum zaiyi ma********on har sau 50 🤔

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Malamin Aji posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share