Atta'awun youth association aya RC no:174712

Atta'awun youth association aya RC no:174712 Is a community organization initiated to cater for orphans, widows, less privilege and youths.

*TARIHIN KAI YARA MAKARANTU –* *_Atta'awun Youth Association (A.Y.A.)_* Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.A wa...
09/19/2026

*TARIHIN KAI YARA MAKARANTU –* *_Atta'awun Youth Association (A.Y.A.)_*

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

A watan *Satumbar, *shekarar 2019,* Atta'awun Youth Association (A.Y.A.) ta fara shirin kai *yara marayu, marasa galihu, da matasa* makaranta domin cika daya daga cikin manyan manufofin kungiyar na tallafawa ilimi.

A farkon wannan shiri, an kai yara *13 zuwa matakan Nursery, Primary, da Secondary School.*

Daga nan, kungiyar ta ci gaba da bude shirin daukar yara tare da kaisu makarantu daban-daban har zuwa *shekarar 2023, wato tsawon shekaru hudu (4)* ana gudanar da wannan aiki cikin nasara.

A halin yanzu, kungiyar tana da *Biodata na dalibai 72,* ciki har da daliban Secondary da kuma matasan da ke karatu a manyan makarantu ( *Tertiary Institutions).*

In Sha Allahu, a wannan shekarar ma za mu ci gaba da wannan shiri na tallafawa yara da matasa. Kungiyar ta dauki kudurin cigaba da kai *yara da matasa* makarantu bayan an kammala tantance su.

Nan gaba kadan, za mu gabatar muku da:

* Sunayen daliban da aka zaba.

* Sunayen makarantunsu.

* Ajujuwansu.

* Da kuma hotunansu.

Muna rokonku ku yi mana *Like, Comment, da Share domin jin ra'ayoyinku* da kuma isar da wannan aikin alkhairi ga sauran al'umma.

Mungode da goyon bayanku. *Atta'awun Youth Association (A.Y.A.)*

BARKA DA DAWOWA HUTUN KARATUAssalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.Alhamdulillah, muna muku barka da wannan loka...
09/16/2026

BARKA DA DAWOWA HUTUN KARATU

Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.

Alhamdulillah, muna muku barka da wannan lokaci mai albarka, tare da barkanmu da dawowa daga hutun karatu na dogon zango.

Kungiyar Atta'awun Youth Association (A.Y.A.) na farin cikin sanar da ku cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na ci gaban al'umma, musamman wajen kula da marayu, marasa galihu, da iyayen marayu, tare da ba da fifiko ga harkokin karatunsu da sauran bukatun rayuwarsu domin inganta rayuwar al'umma.

In shaa Allah, za mu ci gaba da kawo muku rahotannin ayyukanmu ta hanyar hotuna da bidiyo domin ku ga irin ayyukan da ake gudanarwa.

Muna roƙon ku da ku kasance tare da mu ta hanyar Like, Comment, da Share, tare da bayyana mana ra'ayoyinku da shawarwarinku domin ƙara inganta ayyukanmu.

Allah Ya saka da alheri. Atta'awun Youth Association (A.Y.A.)

SAƘON GODIYAA madadin daukacin mambobin Atta'awun Youth Association (A.Y.A.), ina miƙa godiya ta musamman ga dukkan waɗa...
08/07/2026

SAƘON GODIYA

A madadin daukacin mambobin Atta'awun Youth Association (A.Y.A.), ina miƙa godiya ta musamman ga dukkan waɗanda s**a halarci taronmu, tare da waɗanda s**a yi mana fatan alheri da addu'o'i. Allah Ya saka wa kowa da mafificin alheri.

Ina kuma miƙa godiya ta musamman ga Usman Umar Ali, wanda ya jagoranci kwamitin shirya wannan karatu cikin himma da jajircewa.

Haka nan muna godiya ga Zakari Abdullahi bisa kulawar da ya yi wajen ɗaukar bidiyo da adana muhimman abubuwan da s**a gudana, da kuma Khalid Adam, wanda ya gabatar da shirin cikin ƙwarewa da hikima.

Muna kuma miƙa godiya da jinjina ga Alaramma Sabitu tare da sauran Alarammomi, Malama Kaltume tare da sauran malamai, da kuma ɗalibai maza da mata, bisa gudummawar da s**a bayar wajen ganin wannan shiri ya gudana cikin nasara.

Muna roƙon Allah (SWT) Ya karɓi addu'o'inmu baki ɗaya, Ya saka wa kowa da alheri, Ya ƙara mana haɗin kai, ƙauna da ɗorewar zumunci.

Mun gode ƙwarai. Jazakumullahu Khairan.

Hashim Aliyu
Shugaban Ƙungiya
Atta'awun Youth Association (A.Y.A.)

08/06/2026

*ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUH*
*
*GAYYATA ZUWA SAUKAR AL-ƘUR'ANI MAI GIRMA**

Kungiyar Atta'awun Youth Association (A.Y.A.) tana farin cikin gayyatar daukacin al'umma zuwa wajen *Saukar Al-Ƙur'ani Mai Girma* wanda ta shirya domin neman taimako da nassarar Allah wajen fara aikin *ginin makarantarta,* tare da roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya ba wa *ƙasarmu zaman lafiya, tsaro, haɗin kai da ci gaba* .

Rana: Juma'a 7 August, 2026
Lokaci: Karfe 4:00 na yamma (4:00PM)
Wuri: Masjidu Sunnah, Sabon Layi, Ƙasan Kwari.

Muna roƙon Allah Ya sa wannan taro ya zama sanadin alheri, Ya karɓi addu'o'inmu, Ya ba da nasara ga wannan aikin alheri, Ya kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasarmu.

Allah Ya saka da alheri. Muna sa ran halartar ku.

*HIJRAH NEW YEAR MESSAGE 1448 AH*  *Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.* All praise is due to Allah (SWT), the...
06/16/2026

*HIJRAH NEW YEAR MESSAGE 1448 AH*

*Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.*

All praise is due to Allah (SWT), the Lord of the worlds, who in His infinite mercy has granted us the opportunity to witness the beginning of a *new Hijrah year, 1448 AH.* We thank Him for His countless blessings, protection, guidance, and the successes He has enabled us to achieve throughout the past year.

As we welcome this *new Islamic year,* the leadership, members, and beneficiaries of *Atta'awun Youth Association (AYA)* extend our heartfelt appreciation to all our members for their dedication, commitment, and unwavering support towards the growth and development of the association. Your sacrifices, time, and efforts have contributed immensely to the success of our humanitarian, educational, and community development activities.

We also express our profound gratitude to our *esteemed donors, supporters, partners, and well-wishers*whose generosity has enabled us to reach many vulnerable individuals and families within our communities. Your contributions have brought hope to widows, orphans, students, and the less privileged, and we pray that Allah (SWT) rewards you abundantly.

Special appreciation goes to all those who promote and support our activities through various social media platforms. Your encouragement, constructive feedback, and efforts in sharing our messages have helped us expand our reach and strengthen our impact.

The *Hijrah of our beloved PROPHET MUHAMMAD (SAW)* teaches us valuable lessons of faith, sacrifice, perseverance, unity, and reliance upon Allah. As we enter this new year, let us renew our commitment to serving humanity, strengthening our brotherhood, promoting education, and supporting those in need.

We pray that *ALLAH (SWT)* makes the year 1448 AH a year of peace, prosperity, good health, success, and countless blessings for all our members, donors, supporters, and the entire Muslim Ummah. May He accept our acts of worship, forgive us all

*SAKON GODIYA NA EID AL-ADHA 2026* Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.Dukkan godiya ta tabbata ga Allah (SWT) ...
05/30/2026

*SAKON GODIYA NA EID AL-ADHA 2026*

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah (SWT) wanda cikin rahamarsa Ya ba mu damar shaida da gudanar da bukukuwan *Eid Al-Adha* na wannan shekara. Muna roƙon Allah Ya karɓi ibadunmu da sadaukarwarmu baki ɗaya.

Ina miƙa godiya ta musamman ga dukkan mambobin wannan ƙungiya, musamman mambobin *EXCOS*, bisa jajircewa, sadaukarwa da haɗin kai da s**a nuna wajen tabbatar da cewa dukkan ayyukan wannan shiri sun gudana cikin nasara da tsari.

Haka kuma muna miƙa godiya ta musamman ga *TURKISH EMBASSY* da dukkan ma'aikatanta bisa tallafi da goyon bayan da s**a bayar wajen gudanar da aikin yankan layya na bana da aka gudanar a Bauchi, Nigeria.

Muna kuma gode wa dukkan *iyayen marayu (Widows)* da s**a nuna haƙuri, biyayya da haɗin kai yayin rabon naman layya. Allah Ya saka musu da alheri kuma Ya sanya wannan taimako ya zama sanadin albarka a rayuwarsu.

*Allah (SWT)* Ya saka wa kowa da mafificin alheri, Ya ƙara haɗin kai da ɗorewar zumunci a tsakaninmu, Ya kuma karɓi ibadunmu baki ɗaya.

REMINDERS! REMINDERS!! REMINDERS!!!Ga wadanda ke nesa Kuma Suna da burin Saka nasu jarin:4650644855atta'awun youth assoc...
05/26/2026

REMINDERS! REMINDERS!! REMINDERS!!!
Ga wadanda ke nesa Kuma Suna da burin Saka nasu jarin:

4650644855
atta'awun youth association
monie point

Ga wadanda ke nesa Kuma Suna da burin Saka nasu jarin:4650644855atta'awun youth association monie point
05/17/2026

Ga wadanda ke nesa Kuma Suna da burin Saka nasu jarin:

4650644855
atta'awun youth association
monie point

Address

Los Angeles, CA

Telephone

+2347030748715

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Atta'awun youth association aya RC no:174712 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Atta'awun youth association aya RC no:174712:

Shortcuts

Share