16/09/2026
Jagororin Ƙungiyar Masu Buƙata Ta Musamman mai taken suna Coalition of Katsina State Disability Group, ƙarƙashin jagorancin Hon. Umar Jibril Bindawa (S.A. to the Governor on Disabled Matters, Katsina State), sun kawo ziyarar ban-girma da girmamawa ga Shugaban Shirin Ci gaban Al’umma (CDP), Assoc. Prof. Kamaluddeen Kabir.
A yayin ziyarar, jagororin ƙungiyar sun yaba da ƙoƙari da jajircewar shugaban wajen tabbatar da cewa saƙon Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, yana isa ga al’umma, musamman waɗanda ke ƙasa daga tushe.
Haka kuma, sun yaba da yadda Shirin Ci gaban Al’umma (CDP) ke ba mutane masu buƙata ta musamman muhimmanci a cikin ayyukansa, tare da tabbatar da cewa suna amfana da kayayyaki da tallafin da ake rabawa.
A ƙarshe, jagororin ƙungiyar sun miƙa wa Shugaban CDP, Assoc. Prof. Kamaluddeen Kabir, lambar yabo ta girmamawa bisa ƙoƙarinsa, jajircewarsa da gudummawar da yake bayarwa wajen gudanar da ayyukan ci gaba a faɗin Jihar Katsina.