19/06/2025
ASSALAMU ALAIKUM.
Barkanmu da safiya, da fatan kowa ya tashi lafiya.
Muna sanar da ɗaukacin al’umma cewa an samu wasu da ke amfani da sunan Anguwan Fullani Palladan Youth Development Association (A-PYDA) wajen ziyartar ma’aikatu da wasu hukumomi domin biyan wasu buƙatun kansu, ba tare da izini ko sanin shugabannin kungiyar ba.
Muna so a tabbatar da cewa waɗanda ke yin hakan ba da yawun kungiyar suke ba, kuma ba da amincewar mambobin A-PYDA suke ba. Saboda haka, duk wata ma’aikata ko hukuma da ta karɓe su, ko ta yi musu wata alƙawari, ta sani cewa ta yi masu ne, amma ba dai kungiya ba.
A nata bangaren, shugabannin kungiyar za su ɗauki duk matakin da ya dace kan wannan abu domin kare martabar kungiyar.
A ƙarshe, muna sanar da jama’a cewa duk wani rubutu ko saƙo da bai fito kai tsaye daga wannan shafin ba, to ba daga kungiyar A-PYDA ya fito ba.
Mun gode .
Shugabancin A-PYDA