Al-Mahdi Scouts Nigeria

Al-Mahdi Scouts Nigeria Kasshafatu Imamil Mahdi (ATF) [Al-mahdi scouts] is a scout organisation in islamic movement under the leadership of sheikh Ibraheem Yaqoob Zakzaky(h) nigeria.

AL-MAHDI CUB SCOUTS SUN GUDANAR DA INTIZAR DAY 2026 A KANOMembobin Al-Mahdi Cub Scouts na yankin Kano sun gudanar da bik...
17/09/2026

AL-MAHDI CUB SCOUTS SUN GUDANAR DA INTIZAR DAY 2026 A KANO

Membobin Al-Mahdi Cub Scouts na yankin Kano sun gudanar da bikin Intizar Day 2026, domin tunawa da fara Imamancin Imam Muhammad Al-Mahdi (ATFS), tare da yaye wasu daga cikin mambobinta daga Cub Scouts zuwa Boy Scouts.

Taron ya mayar da hankali kan muhimmancin Intizar, tarbiyya, shiryawa da gina al’umma, tare da jaddada muhimmiyar gudunmawar iyaye wajen tarbiyyar yara.

Yaye mambobin zuwa Boy Scouts ya nuna ci gaba zuwa sabon mataki mai dauke da karin nauyi da alkawari.

— Al-Mahdi Scouts Nigeria

A ranar Lahadin da ta gabata 13th September , 2026, Bangaren Al-Mahdi Cub Scouts na garin Zaria, Wanda shine sashin kana...
16/09/2026

A ranar Lahadin da ta gabata 13th September , 2026, Bangaren Al-Mahdi Cub Scouts na garin Zaria, Wanda shine sashin kananan Yara na Al-Mahdi Scouts Nigeria s**a gudanar da taron tunawa da ranar fara Imamancin Sahibul Asr Al-Mahdi (A.S)

Taron Wanda ya dauki tsawon kwanaki biyu ana gudanarwa, Wanda tun a farko an gudanar da wasu abubuwa domin nishadantar da Yara da kuma abubuwan da suke Kara kusanta bayin zuwa ga Allah (T) da hanyoyin Wanda ya kamata Mai jiran Intizar ya kasance Yana dabbakawa.

-Al-Mahdi Scouts Nigeria

A ranar Talatar da ta gabata 8th September , 2026, Bangaren Al-Mahdi Cub Scouts na garin Yola, Wanda shine sashin kanana...
15/09/2026

A ranar Talatar da ta gabata 8th September , 2026, Bangaren Al-Mahdi Cub Scouts na garin Yola, Wanda shine sashin kananan Yara na Al-Mahdi Scouts Nigeria s**a gudanar da taron tunawa da ranar fara Imamancin Sahibul Asr Al-Mahdi (A.S)

Taron Wanda ya dauki tsawon kwanaki biyu ana gudanarwa, Wanda tun a farko an gudanar da wasu abubuwa domin nishadantar da Yara da kuma abubuwan da suke Kara kusanta bayin zuwa ga Allah (T) da hanyoyin Wanda ya kamata Mai jiran Intizar ya kasance Yana dabbakawa.

-Al-Mahdi Scouts Nigeria

RASULUL AKRAM TROOP (AL-MAHDI SCOUTS NIGERIA)A ranar Juma'ar da ta gabata 29th ga watan Rabi'ul Auwal na shekarar 1448 M...
14/09/2026

RASULUL AKRAM TROOP (AL-MAHDI SCOUTS NIGERIA)

A ranar Juma'ar da ta gabata 29th ga watan Rabi'ul Auwal na shekarar 1448 Membobin Al-Mahdi Scouts Nigeria daga Rasulul Akram Troop (R01), Sayyada Khadija Patrol, sun gudanar da Mauludun Manzon Rahma (S) wanda s**a saba gabatarwa duk shekara wannan shi ne karo na 4.

Mahalarta taron sun hada da Members da PTA na Al-Mahdi Scouts, sannan an samu halartar Sha'iri da kuma Babban Baƙo Mai Jawabi.

Daga cikin abubuwan da s**a gudana a wurin Taron:
Bayan buɗe Taro da Addu'a an saurari karatun Al-Qur'ani mai Girma daga bakin Patrol Members, Ziyarar Manzo (S) daga Nesa da kuma Scouts Promise kamar yadda aka saba. An gudanar Inter Patrol Game inda aka yi Tambaya da amsa akan rayuwar manzo (S) a tsakanin Patrol 5, bayan nan sai aka gabatar da Poem Presentation akan: (Imam Mahdi (ATFS), Jagora (H), da kuma raunana Al'ummar Palestine).

An tuna da Shahidan Al-Mahdi Scouts a matsayin sashi na taron daga nan sai aka saurari Waƙe Na Annabi (S) da Ahlul Bayt (AS) bayan sauraron Waƙe daga Shairi Mal. Munzali sai aka saurari jawabi daga bakon da aka gayyata.

An gabatar da karramawa ga masu sunan Manzo (S), da iyayen sa da nufin girmamawa ga Manzo (S).

-Al-Mahdi Scouts Nigeria
/2026
(7)

Yan Al-Mahdi Cub Scouts Zaria A yayin shirye-shiryen bikin Intizar Day 2026, ’yan Al-Mahdi Cub Scouts Zaria, sun gudanar...
13/09/2026

Yan Al-Mahdi Cub Scouts Zaria

A yayin shirye-shiryen bikin Intizar Day 2026, ’yan Al-Mahdi Cub Scouts Zaria, sun gudanar da wasanni (Games) da kuma ziyarar Shahidai a muhallin Darur-Rahma.

Ziyarar ya kasance wata dama ta koyar da yara muhimmancin tunawa da sadaukarwar Shahidai.

-Al-Mahdi Scouts Nigeria

Al-Mahdi CUB SCOUTS ZARIAMambobin Al-Mahdi Cub Scouts na Zaria sun gudanar da excursion a yayin da s**a fara gudanar da ...
11/09/2026

Al-Mahdi CUB SCOUTS ZARIA

Mambobin Al-Mahdi Cub Scouts na Zaria sun gudanar da excursion a yayin da s**a fara gudanar da bikin Intizar Day 2026, zuwa gidan rediyo, inda yaran s**a samu damar ganin yadda harkar rediyo da shirye-shiryen watsa labarai ke gudana.

Wannan ziyara ta ba yaran damar kara fahimtar aikin kafafen yaɗa labarai, tare da koyon sabbin abubuwa cikin yanayi na nishaɗi da ilimi.

-Al-Mahdi Scouts Nigeria

08/09/2026

Bangaren yayen Yan Al-Mahdi Cub Scouts Nigeria Wanda aka gudanar a ranar tunawa da Imamancin Imam Mahdi (ATF)

-Al-Mahdi Scouts Nigeria

AL-MAHDI CUB SCOUTS SUN GUDANAR DA BIKIN INTIZAR DAY, TARE DA YAYE WASU MEMBOBINTA ZUWA BOY SCOUTS A Potiskum, Gombe da ...
08/09/2026

AL-MAHDI CUB SCOUTS SUN GUDANAR DA BIKIN INTIZAR DAY, TARE DA YAYE WASU MEMBOBINTA ZUWA BOY SCOUTS

A Potiskum, Gombe da Bauchi, Al-Mahdi Cub Scouts Nigeria ta gudanar da bikin Intizar Day, wato ranar tunawa da fara Imamancin Imam Muhammad Al-Mahdi (ATFS), tare da bikin yaye wasu daga cikin mambobinta daga matakin Cub Scouts zuwa Boy Scouts.

An gudanar da bukukuwan a Potiskum, Gombe da Bauchi, inda mambobin kungiyar da sauran mahalarta s**a samu halarta domin tunawa da wannan rana tare da kara fahimtar muhimmancin Intizar, tarbiyya da shiryawa domin gina al’umma mai nagarta.

A yayin taron, an jaddada cewa Intizar ba iya jira ba ne, illa wani shiri ne na mutum ta hanyar kyawawan dabi’u, neman ilimi, aiki da kuma hidimar al’umma.

Sannan bikin yaye mambobin zuwa Boy Scouts kuma ya kasance wani muhimmin bangare na taron, inda aka nuna ci gaban mambobin daga matakin farko zuwa wani sabon mataki mai dauke da karin nauyi.

Bikin ya gudana cikin nasara a wadannan yankunan guda uku, tare da nuna muhimmancin bai wa yara tarbiyya da damar koyon yin hidima tun daga kananan shekaru.

— Al-Mahdi Cub Scouts Nigeria

INTIZAR DAY 2026 – DAY 3A yau, rana ta uku (Day 3) na bikin Intizar Day 2026, Al-Mahdi Cub Scouts Nigeria sun gudanar da...
05/09/2026

INTIZAR DAY 2026 – DAY 3

A yau, rana ta uku (Day 3) na bikin Intizar Day 2026, Al-Mahdi Cub Scouts Nigeria sun gudanar da wani shiri na musamman na Yaumul-Taklifi, domin karramawa da faranta ran yaran da s**a kai shekarun fara Taklifi.

A yayin shirin, yaran sun samu dama ta musamman wajen koyon darussa masu muhimmanci kan sabbin nauye-nauyen addini da s**a hau kansu, tare da fahimtar muhimmancin biyayya ga Allah (SWT) da kiyaye dokokin addini.

Haka kuma, an gudanar da karatun Al-Qur’ani mai girma da addu’o’i, sannan yaran s**a kai ziyara makabarta, domin tunawa da wanda s**a rasu da kuma yin addu’a a gare su.

— Al-Mahdi Scouts Nigeria





MUHIMMIYAR SANARWA Al-Mahdi Scouts Nigeria.Na farin cikin sanar da daukacin al'umma gaba daya musamman masu hulda da kaf...
05/09/2026

MUHIMMIYAR SANARWA

Al-Mahdi Scouts Nigeria.

Na farin cikin sanar da daukacin al'umma gaba daya musamman masu hulda da kafofin sada zumunta (social media),

Zuwa yanzu kasshafatul Imamil Mahdi (A.S) ta bude sabon account din Tiktok, Wanda za'a iya samun sahihan abubuwan da s**a shafe ta kai tsaye.

Wannan shine shafi na musamman da Lajnar ta bude.

Sannan ana Kira da dukkanin masu hulda da kafofin sada zumunta din cewa duk wani (Page) da yake Tiktok idan ba wannan bane bamu da masaniya dashi.

Ku biyo mu ta wannan link din da yake kasa domin samun ingatattun abubuwan da s**a shafe mu.

https://www.tiktok.com/?_r=1&_t=ZS-99TkfdV13qf

Sanarwa daga
Media team
Al-Mahdi Scouts Nigeria

16 Followers, 0 Following, 23 Likes - Watch awesome short videos created by kasshafal_Mahdi

Address

No. 1 Darur Rahma Dembo S/gari Zaria
Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-Mahdi Scouts Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share