Sokoto Women Zakat and Waqf Initiative

Sokoto Women Zakat and Waqf Initiative Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sokoto Women Zakat and Waqf Initiative, Non-Governmental Organization (NGO), IET Sokoto, Kalambaina Road, Sokoto, Sokoto.

KUNGIYAR SOKOTO WOMEN ZAKAT AND WAQF INITIATIVE  TA KADDAMAR DA RIJIYOYI GUDA UKKU GA  AL'UMMA Alhamdulillah! Alhamdulil...
30/07/2026

KUNGIYAR SOKOTO WOMEN ZAKAT AND WAQF INITIATIVE TA KADDAMAR DA RIJIYOYI GUDA UKKU GA AL'UMMA

Alhamdulillah! Alhamdulillah!

A yau, Kungiyar Sokoto Women Zakat and Waqf Initiative (SOKWOZAWI) ta sake cimma wani babban nasara a cikin ayyukanta na jinƙai, inda ta yi nasarar kaddamar da rijiyoyi uku da aka kammala domin samar wa al'umma ruwan sha mai tsafta da sauƙin samu.

An gina kuma an kaddamar da rijiyoyin ne a wurare kamar haka:

- Gidan Jariri
- Mabera Bayan GGC
- Unguwar Rogo – Makarantar Ibn Taymiyyah Islamiyya

Bikin kaddamarwar ya samu halartar Shugabannin Kungiyar, mambobin kungiyar, shugabannin al'umma, wadanda s**a amfana da aikin, masu sa kai da sauran masu fatan alheri, domin shaidar kammala wannan muhimmin aikin ci gaban al'umma.

Samar da tsaftataccen ruwan sha yana daga cikin manyan bukatun al'umma. Wadannan rijiyoyi za su taimaka matuka wajen rage wahalar neman ruwa, musamman ga mata da yara, tare da inganta tsafta da muhalli, kare lafiya, tallafa wa rayuwar yau da kullum da kuma bunkasa walwalar iyalai a yankunan da s**a amfana.

Da take jawabi a wajen taron, Shugabar Kungiyar Malama Amina Musa Sakaba ta sake jaddada kudirin kungiyar na ci gaba da aiwatar da ayyukan jinƙai ta hanyar amfani da Zakkah da Waqafi, domin samar da ayyukan ci gaba masu dorewa da ke magance matsalolin al'umma, musamman masu rauni da marasa galihu.

Ta kuma bayyana cewa zuwa yanzu kungiyar ta gina rijiyoyi sama da ashirin (20) a sassa daban-daban na Jihar Sokoto, inda ta kashe fiye da Naira miliyan goma (₦10,000,000) wajen samar da tsaftataccen ruwan sha ga dubban al'ummar jihar Sakkwato.

Wadanda s**a amfana da wannan aiki sun bayyana matuƙar godiyarsu ga kungiyar, masu bayar da gudummawa, abokan hulɗa da duk wadanda s**a ba da tasu gudummawa wajen ganin an kammala wannan aiki cikin nasara. Sun kuma yi addu'ar Allah (SWT) Ya saka wa kowa da kowa da alkhairi, Ya sanya wannan aiki cikin mizanin kyawawan ayyukansu.

Kaddamar da wadannan rijiyoyi uku na kara tabbatar da jajircewar Sokoto Women Zakat and Waqf Initiative wajen inganta rayuwar al'umma, samar da tsaftataccen ruwan sha da kuma ci gaba mai dorewa a fadin Jihar Sokoto.

Muna roƙon Allah (SWT) Ya karɓi wannan aiki a matsayin Sadaka Jariya, Ya albarkaci duk masu bayar da gudummawa, abokan hulɗa, masu sa kai da masu tallafawa wannan ayyukan, Ya kuma ci gaba da ba Kungiyar Sokoto Women Zakat and Waqf Initiative ikon gudanar da irin waɗannan ayyukan alheri domin amfanin al'umma.
Ameeeeeen
Ameeeeeen.
Ameeeeeen

Reported by
Aminu Bello Isah
Admin secretary Sokoto Women Zakat and Waqf Initiative

10/07/2026
10/07/2026
SOKOTO WOMEN ZAKAT AND WAQF INITIATIVE RAHOTON KADDAMAR DA GONAR MARAYU TA WAQAFI DA SHUKA ITATUWAN WAQAFI A ranar Asaba...
29/06/2026

SOKOTO WOMEN ZAKAT AND WAQF INITIATIVE
RAHOTON KADDAMAR DA GONAR MARAYU TA WAQAFI DA SHUKA ITATUWAN WAQAFI

A ranar Asabar, 27 ga Yuni, 2026, kungiyar Sokoto Women Zakat and Waqf Initiative ta gudanar da bikin kaddamar da Gonar Marayu ta Waqafi da Shuka Itatuwan Waqafi a Wajeki District, Barkeji Village, Wamakko Local Government Area, Sokoto State.

An fara taron da addu'a, wanda Malama Maryam Dalha ta Jagoranta. sannan aka karanta Al-Qur'ani Mai Girma daga bakin Hajiya Huraira Isah Illo, tare da jawaban maraba daga mai tsare tsaren ƙungiya Hajiya Kulu Ahmad.
Shugabar kungiyar, Malama Amina Musa Sakaba, ta bayyana cewa wannan shiri an kirkiro shi ne domin samar da hanyar samun kudaden shiga mai dorewa don tallafa wa marayu ta hanyar tsarin Sadaqah Jariyah. Ta kuma yi kira ga Al'umma dasu taimaka wurin ganin anyi shingen wannan Gonar.

Babban bako, Mai Girma Sadaukin Sakkwato, kuma Shugan Hukumar Zakka da Waqafi ta Jahar Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki ya gabatar da jawabi mai cike da hikima wanda ya ratsa zukatan mahalarta taron. Ya yi cikakken bayani kan muhimmancin yin Waqafi, musamman dasa itatuwa, yana mai jaddada cewa amfaninsu yana ci gaba har tsawon shekaru masu yawa, wanda ke sanya mai yin waqafi ya ci gaba da samun lada bayan rasuwarsa. Ya kuma yi kira ga al'umma da su rungumi wannan kyakkyawan aiki domin cigaban addini da al'umma. A ƙarshe, ya yi addu'ar Allah Ya sanya albarka a wannan gona ta waqafi, Ya sanya ta zama sanadin tsira garemu da marayu da sauran al'umma gaba daya.

A nasa jawabin, Mai Girma Magajin Barkeji ya bayyana matuƙar farin cikinsa da wannan gagarumin shiri da matan Jihar Sakkwato da s**a kawo. Ya yabawa kungiyar bisa hangen nesanta da kokarinta na tallafa wa marayu ta hanyar da za ta dore. Haka kuma ya yi alkawarin cewa masarautarsa za ta kula da gonar yadda ya kamata, sannan ya ba da gudummawar bulu dari (100 blocks) domin yin shingen (fencing) gonar.

Bayan jawabban, an gudanar da aikin dasa itatuwan waqafi inda aka shukka itace 55 da ke bada yaya kamar su Mangoro, Dabino, Guiba, tare da addu'ar neman albarkar Allah ga wannan shiri. Taron ya samu halartar manyan baki, shugabannin al'umma, malamai, mata da matasa daga sassa daban daban na Jihar Sakkwato.

An kammala taron cikin nasara da kyakkyawan fata cewa wannan Gonar Marayu ta Waqafi za ta kasance wata muhimmin hanya ta samar da tallafi mai dorewa ga marayu, tare da ƙarfafa al'ummar jihar su rungumi waqafi da ayyukan Sadaqah Jariyah domin samun lada mai ɗorewa.
Anrufe taron da addu'o'i na musamman daga bakin Malama Hafsat Ismail

Aminu Bello Isah
Admin Secretary
Sokoto Women Zakat and Waqf Initiative

Our Next Activity on Saturday 27 June 2026 Insha Allah
26/06/2026

Our Next Activity on Saturday 27 June 2026 Insha Allah

Saudakun Na Farko A Daular Usmaniyya.Jazakallahu Khair.Al'umma Na godiya
29/05/2026

Saudakun Na Farko A Daular Usmaniyya.
Jazakallahu Khair.
Al'umma Na godiya

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Ina mika sakon taya murnar Babbar Sallah ga daukacin mambobin Sokoto Women Z...
26/05/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Ina mika sakon taya murnar Babbar Sallah ga daukacin mambobin Sokoto Women Zakat and Waqf Initiative, abokan hulda, masu ruwa da tsaki da daukacin al’ummar Musulmi.

Muna addu’ar Allah Ya karbi ibadunmu, Ya sanya wannan lokaci na Eid Kabir ya zama sanadiyyar zaman lafiya, albarka, ci gaba da hadin kai a tsakaninmu.

Muna matukar godiya da irin goyon baya, sadaukarwa da jajircewar da kuke nunawa wajen tallafawa ayyukan alkhairi da kungiyar ke gudanarwa domin cigaban mata da al’umma baki daya.

Allah Ya maimaita mana cikin koshin lafiya da yalwar arziki.

Eid Mubarak!

Malama Amina Musa Sakaba
Shugabar Kungiya
Sokoto Women Zakat and Waqf Initiative

Address

IET Sokoto, Kalambaina Road, Sokoto
Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sokoto Women Zakat and Waqf Initiative posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share