22/12/2025
A jiya ne kuma Allah Ya sake yi mana ni’ima, inda wasu daga cikin ɗaliban makarantar mu ta Zaid bn Thabit, Arkilla State Low-Cost, s**a sake haddace Alƙur’ani, sati uku kenan bayan wasu biyun sun haddace.
Wannan ni’ima ta zo ne daidai lokacin da wannan makaranta ke cika shekaru uku da kafuwa. A halin yanzu, adadin ɗaliban da s**a haddace Alƙur’ani ya kai bakwai, yayin da wasu da dama kuma suke kan hanya, in shaa Allah.
Allah muke roƙo Ya sanya wa waɗannan ɗalibai albarka, Ya basu ikon kiyaye wannan Littafi Mai girma, kuma Ya sanya shi sanadin tsirarmu a duniya da lahira.