02/08/2026
Gamayyar Sokoto Heritage Reloaded Initiative da Crystal Muslim Organization Sun Taya Sabon Dallatun Sokoto Murna
A yau ne gamayyar Sokoto Heritage ReloadedI da Crystal Muslim Organization s**a kai ziyarar taya murna ga sabon Dallatun Sokoto, Alhaji Murtala Abdulkadir Dan Iya, a gidansa bayan nadin sarautar da Mai Martaba Sarkin Musulmi ya yi masa.
Da yake jawabi a madadin kungiyoyin biyu, Hon. Nuruddeen Muhammad Mahe ya bayyana cewa nadin Alhaji Murtala Abdulkadir Dan Iya a matsayin Dallatun Sokoto wani babban ci gaba ne ga Jihar Sokoto, la’akari da irin ayyukan alheri, taimakon jama’a da hidimar ci gaban al’umma da yake gudanarwa.
Ya kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba sabon Dallatun Sokoto ikon sauke nauyin wannan sarauta cikin adalci da hikima, Ya kuma kare shi daga dukkan wani sharri.
A nasa jawabin, Mai Girma Dallatun Sokoto, Alhaji Murtala Abdulkadir Dan Iya, ya nuna matuƙar godiyarsa ga gamayyar kungiyoyin bisa wannan ziyarar taya murna, tare da addu’ar Allah Ya saka musu da alheri, Ya kuma ba su ƙarfin ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da hidimar al’umma.
A yayin ziyarar, an miƙa kyauta ta musamman ga Mai Girma Dallatun Sokoto, sannan aka gudanar da addu’o’i na musamman domin neman Allah Ya yi masa jagora, Ya ba shi lafiya, tsawon rai da nasara wajen gudanar da sabon nauyin da aka ɗora masa.