08/09/2025
SHIN KO KUNA LARA DA IRIN YADDA MATAN DA KUKA SAKI, SUKE WAHALA DA DAWAINIYA DA YA'YANKU WADANDA SUKE RIKE DASU?
Dayawa daga Cikin Zawarawan da Auren su ya mutu, suna shiga tasko da wahalhalu daban-daban wajen Kula da Yaran dasu s**a haifa a gidajen Auren su kafin su fito.
Wasu su kan dauki dogon lokaci basuyi Aure ba, saboda jin tsoron Halin da Yayan su zasu shiga idan s**ayi Auren.
Wasu kuma zasu fuskanci Tsangwama da Cikin Zarafi a gidajen su da na yan'uwan su duk adalilin Yaran da s**a fito tare dasu bayan mutuwar Auren su.
Shin wane taimako ko tausayawa kuke yiwa Matan da kuka saki, kuka barsu da yara suna reno?
Shin bai kamata wadannan bayin Allah su sami tausayawa da taimakon ku ba?
A gaskiya, da yawa daga cikin mata da auren ya Mutu s**an shiga cikin mawuyacin hali wajen kula da yaran da aka haifa.
Wasu lokuta ma, iyaye maza s**an kau da kai daga nauyin da ya rataya a wuyansu.
Wannan abu ba daidai bane, domin yaran nan haƙƙinsu ne akan uba, kuma Allah zai tambayi uba kan yadda ya kula da su.
Abubuwan da ya kamata a fahimta:
1. *Nauyin yara ba ya gushewa don an saki mahaifiyar su.*
Idan ma’aurata sun rabu, alhakin ciyarwa, sutura, kiwon lafiya, da ilimi nauyin uba ne.
2. *Tausayi da goyon baya*
Maccen da aka saki da yara tana bukatar goyon baya na kudi da na zuciya domin kada ta shiga cikin halin kunci tare da 'ya'yan.
3. *Gudanar da zumunci*
Rabuwa da uwa ba ya nufin rabuwa da yara ba ne. Uba yana da hakkin ganin 'ya'yansa, da kuma kula da tarbiyyar su, haka suma Ya'yan suna hakkin ganin Uban su da yin Mu'amula tare dashi.
4. *Alheri ga uwa*
Idan uba yana tausayawa uwa saboda yaran da take riƙe dasu, wannan zai taimaka wajen rage mata damuwa da kuma tabbatar da yaran sun samu kulawa mai kyau.
*Tambaya ga maza:*
Shin muna tunanin yaran da muka bari basu da bukata irin ta sauran yara?
Shin mun san idan muka bar macce wadda muka saki tare da yara ba tare da tallafi ba, muna cutar da yaran mu kai tsaye ne ?
Shin ba ya fi dacewa mu yi hakuri da ɗan sadaukarwa don ganin yaran mu sun tashi lafiya fiye da barin su cikin wahala ba ?
A takaice, bai kamata uba ya ɗauki saki a matsayin hutu daga alhakin daukar dawainiyar yaran shi ba, domin a tsari da ka'idar addini da al’ada, haƙƙin yara yana da Matukar muhimmancin gaske.