07/03/2023
ZABEN GWAMNA: Sheikh Malam Ibrahim Khalil bai taba aikin Gwamnati ba, duk da cewa cikakken dan Boko ne wanda yake da shaidar karatun boko har a Cambridge University.
2. Cikakken dan Kasuwa ne wanda ya kewaya sama da kasashe 60, babu wani yanki na duniyar nan da Malam Khalil bai shiga ba a harkar kasuwanci. Yanzu haka shine Shugaban wasu Yan Kasuwa na Arewacin Nigeria.
3. A bangaren Shugabanci Malam Khalil shine Shugaban Malamai na Northwest ya hade kan kowanne bangare na dariku, babu wanda yake kokawa da shugabancin sa.
4. Yana da experience din shekara 50 a bangaren karantar da ilimin zamani dana Addini. ya taba gayamin cewa bashi da wani abu daya wuce bayar da ilimi. duk inda na ganshi kome yake yi, indai maganar ilimi zanyi masa to in katse shi Kuma zai saurareni, domin harkar ilimi tafi masa komai.
6. Malam Khalil yana da fahimtar rayuwa, idan ya shiga cikin talakawa yana sajewa dasu saboda shigar sa ta gudun duniya, idan ya shiga cikin masu kudi yana sajewa dasu domin sun sanshi a matsayin Attajirin dan Kasuwa, idan ya shiga cikin masu Mulki yana sajewa dasu saboda experience dinsa na zama da masu Mulki tun 1980's, idan ya shiga cikin Malamai kuwa suna girmamashi, suna kiransa da Bijimin Malami saboda iliminsa da gogewarsa.
7. Tun kafin lokacin Siyasa, babu wani lokaci da zakaje office din Malam Khalil baka tarar da akalla mutum 50 ba. Wasu sunzo neman fatawa, wasu zasu aurar da Yaya ba kayan daki, wasu sunzo neman magani, wasu neman abinci wasu neman shawarar rayuwa. Kuma babu Mai zuwa ya taso hannu rabbana.
Idan ana maganar cancanta a kujerar Gwamna banbancin Malam Ibrahim Khalil da sauran Yan takarar, kamar banbancin sama da kasa ne.
Idan Abba zaku zaba ko Gawuna ku zabe su kawai, Amma babu wani mataki na rayuwa da Malam Bai shallake su ba.
Wallahi!
DAGA: Bello Iliyasu