21/04/2025
HASANATUL ABIDAH (RAH)
***************************
Muhammad bn Qudamah yace : mun samu labarin cewa akwai wata mata wacce ake kiranta da suna Hasanah Al Abidah (mai yawan ibadah) wacce ta guje wa jin dadin ni'imomin duniya, ta fuskanci ibada, ta kasance kullum tana wuni da azumi sannan ta raya darare. Alhali agidanta bata da komai, duk lokacin da taji kishirwa sai ta gangara zuwa wani kogi tasha ruwan da tafin hannunta!!
Ta kasance ita kyakkyawa ce sosai. Don haka watarana sai wata mata tace mata "Yake hasanah, kiyi aure mana!"
Sai tace mata "Ki kawo mun namiji mai gudun duniya, wanda bazai dora mun wata dawainiyar duniya ba. Kuma bana tsammanin zaki iya samo min mai wadannan halayen.... Wallahi ni bana nufin in bauta wa duniya, ko inji wani dadi da mazajen duniya".
"Da ache zan samu namijin da zai rika yin kuka, (wato kukan tsoron Allah) nima ya sanyani kuka, kuma yayi azumi, nima ya umurceni inyi, ya rika yin sadaqah sannan nima ya kwadaitar dani akan haka, to madalla da wannan. Amma idan ba irin wannan na samu ba, to shikenan nayi sallama da maza!!"
Wannan labarin yana nan acikin littafin SIFATUS SAFWA na Abdurrahman Ibnul Jauzee.
Irin wadannan matayen akwaisu da yawa azamanin magabata na kwarai. Kamar irin su Rabi'atul Adawiyyah, su Sayyidah Nafeesah, da sauransu.
Sun tsaya akan ibadah da neman ilimi har s**a samu yardar Allah. Duk da cewar zaifi kyau ga mace tayi aure tayi biyayya ga mijinta ta hidimta masa, tare da kulawaa sosai da ayyukan ibadarta domin samun kusanci da Allah..
DAGA ZAUREN FIQHU 08157968686 07064213990 (20/04/2021)