Zaitunah Orphans Association Tulai

Zaitunah Orphans Association Tulai Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Zaitunah Orphans Association Tulai, Nonprofit Organization, Rimi.

18/05/2026

MUHADARAH || MARKAZUTTAUHEED AUWALAN AL ISLAMY GWARINFA ABUJA || 18-05-2026/1446 ||•

010. Raddi Ga Masu Da'awar Sarkin Mayu (Bokanci, Sihiri)
______________________________________

Sheikh Dr. Zayyan Abubakar Haroun.

Domin Neman Karin bayani ko kuma
turo tambayoyin ku: ((08106971779))

14/05/2026

MUHADARAH || MARKAZUTTAUHEED AUWALAN AL ISLAMY GWARINFA ABUJA|| 15-05-2026/1446 ||•

06. Shin Akwai Karama (Mu'ujiza) A Harkan Bokanci
_____________________________________

Sheikh Dr. Zayyan Abubakar Haroun.

Domin Neman Karin bayani ko kuma
turo tambayoyin ku: ((08106971779))

09/05/2026

SEMINAR JIBWIS TORO A GARIN MAGAMA BAUCHI STATE || LEADERSHIP TRAINING || 2026/1447. ||•

Paper Ta Biyu : Wanene Sakatare A Kungiyance Da Ayyukansa.
______________________________________________

Malam Sani Muaz Tama

ZAITUNAH ORPHANS ASSOCIATION TULAI, TAKAI ZIYARAR GAISUWAN SALLAH GA MAI MARTABA HAKIMIN ƘASAR TULAI (ALH. JAFAR IDRIS) ...
16/04/2026

ZAITUNAH ORPHANS ASSOCIATION TULAI, TAKAI ZIYARAR GAISUWAN SALLAH GA MAI MARTABA HAKIMIN ƘASAR TULAI (ALH. JAFAR IDRIS) NA SHEKARAR 1447/2026.
_______________________________

Amadadin kungiyar baki daya bisa Jagorancin (Alh. Murtala Mohammad Balarabe) tare da Rakiyar Abokan gudanar da wannan kungiyar cikin tawaga s**a kai Ziyarar Gaisuwan sallar tare da taya Mai MARTABA Murnar karin girma da ci gaba da wannan Masarautar tasamu.

Bayan haka kungiyar ta gabatar da cikakken BAYANI akan irin gudunmawar da Mai MARTABA yake bawa wannan kungiyar tun zaman Farkon kafata tare da bayyana farin cikin Shuwagabannin ƙungiyar,

Sannan kungiyar ta ci gaba da bayyana irin nasarorin da aka samu tun bayan kafuwar kungiyar tare da kara Jaddada Manufofinta ga Mai MARTABA tare da neman goyon baya kan Ƙudirurin data sanya da tsare-tsaren ta anan gaba.

A Jawabin Godiya tare da nuna farin cikin sa marar misaltuwa ga jagororin wannan ƙungiya mai Albarka, bayan haka, ya kara da tabbatar mana Alkawarin cikakken Goyon bayansa a dukkan Manufar wannan kungiya, ya kara da cewa a gunsa,

Wannan Kungiyar tafi dukkanin kungiyoyi Dubu Muhimmanci a cikin AL'UMMA, Sannan ya tabbatar mana da jin dadinsa bisa BAYANIN da aka gabatar, kungiyar ta samu Mallakar Rejista da Gwamnatin tarayya.

Daga Karshe yayi Nasihu masu Muhimmanci tare da Jan hankali da NUSARWA ga wannan kungiyar sannan yayi jawabai masu tasiri da harshe irin na manya kuma yayi Alƙawarin bata cikakken goyon baya.

Allah ya karawa wannan kungiyar Albarka
Allah ya karawa Jagororin ta Albarka

kuyi Sharring Da Following Domin Tarayya Cikin Lada

Yakubu Dauda Hussaini
Sakataren Watsa labarai
Zaitunah Orphans Association Tulai
16-04-2026/1447.

ZAITUNAH ORPHANS ASSOCIATION TULAI, TORO BAUCHI STATE NIGERIA.
24/03/2026

ZAITUNAH ORPHANS ASSOCIATION TULAI, TORO BAUCHI STATE NIGERIA.

RAHOTON TARON ZAMAN MEETING NA ZAITUNAH ORPHANS ASSOCIATION TULAI An gudanar da taron Zaitunah Orphans Association Tulai...
25/01/2026

RAHOTON TARON ZAMAN MEETING NA ZAITUNAH ORPHANS ASSOCIATION TULAI

An gudanar da taron Zaitunah Orphans Association Tulai karkashin jagorancin Shugaban Ƙungiya, Alh. Muhammad Hussaini wanda ake kira (Alh. Murtala Balarabe).

Taron ya gudana ne inda Malam Dan Bala Polchi (Sakataren Kungiyar ya fara da karanto Ajandoji da buɗe zama da karanta addu’a tare da gabatar da jawabin buɗe taro daga bakin shugaban wannan kungiyar a madadin Ƙungiyar

Daga bisani kuma aka karanto rahoton ayyukan da aka sanya wasu kwamitoci da taron da ya gabata akan wannan ayyukan da aka sanya su daga bakin shugaban Kwamitin (Malam Sunusi Hussaini Ibrahim Yaltin)

Yayi Cikakken bayani akan Aikin da aka dora masu na Bude Account na wannan Kungiyar mai Albarka tun daga farko har aka yi nasarar samun account mallakin wannan kungiyar wanda a wannan zama aka gabatar da Account, da sauran bayanan abubuwan da aka kashe da kuma abin daya saura na dawainiya.

Wanda duk membobin dake cikin Official Group na wannan ƙungiyar dasu shaida wasu Resitin kudi da aka tura cikin a susun wannan kungiyar guda biyu, toh waɗan nan kudi sune kudaden da s**a rage cikin kudaden da aka kashe wajen dawainiya bude account na wannan kungiya.

Hakika dakin taro yayi farin ciki matukar gaske tun daga shi kansa mai girma shugaban wannan kungiyar mai Albarka da sauran Membobinta wanda muka halarci wannan zama baki daya.

Bayan haka, an tattauna kan shirye-shiryen yadda da'a gabatar da wannan kungiyar da mallakin account dinta a fadin duniya baki daya k**a tun daga yankin mu har zuwa wajen ƙasar, wanda aka yi matsaya akan an dauki hanyar amfani da social media domin itace hanya mafi saukin isar da sakon Nan take.

A ƙarshe, an buɗe damar bayar da shawarwari masu amfani domin ƙarfafa harkokin aikace aikacen kungiyar don ci gaban ƙungiya domin ta tsayu da ƙafarta tun daga hanyar shigowar kudi zuwa yadda da'a fadada Ayyukan ta.

Yakubu Dauda Hussain.
Zaitunah Media Directorate
25-01-2026/1447

Address

Rimi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zaitunah Orphans Association Tulai posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share