JIBWIS Mararaba Gurku

JIBWIS Mararaba Gurku The Islamic Organization For Eradicating Innovations and Establishing Sunnah. Ibrahim Na Alh. Hudu Chikaji.
(2)

Jama’atu Izatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (Jibwis)

Kungiyar kawar da Bidi’ah da tsayar da sunna

Wannan qungiya ta al’ummar musulmi an kafa ta ne tun a shekarar 1978 a Najeriya, kuma shugabanta na farko shi ne Alhai Musa Gandu Muhammad, a qarqashin kulawar Malam Abubakar Mahmud Gumi, tare da Sheikh Isma’il Idris bn Zakariyya, a matsayin shugaban majalisar malamai na farko na kungiyar. Qungiyar it

a ce irinta ta farko a tarihin yada addinin musulunci a Najeriya, hadi da harkar ilmantarwa, tare da daukaka darajar harkokin addinin Musulunci ba tare da wani tsoro ba. Don haka ne sai kungiyar ta sanya wasu ginshiqan manufofi da take so ta cimma domin kai wa ga gaci. Daga cikin muhimman manufofin wannan kungiya sun hada da:

- Kawar da duhun jahilci daga cikin al’umma, wanda ya yi wa al’umma katutu.

- Hada kan al’ummar musulmi a bisa koyarwar Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW),

- Wayar da kan al’ummar musulmi game da al’amuran addini, domin a gudu tare a tsira tare.

- Fadakar da al’ummar musulmi domin a yi watsi da wasu miyagun littattafai da suke tura mutane cikin halaka.

- Tabbatarwa da cewa Annabi (SAW) ya kammala isar da sakon Allah (SWT).

- Duk wanda ya yi da’awar annabta, ko kuma yake riya cewa Annabi (SAW) yana ziyartarsa da wani sako, to wannan zunzurutun makaryaci ne.

- Yada Musulunci a Najeriya da wajen Najeriya.

- Yin da’awa a kan fadin Manzon Allah (SAW) cewa: “duk wanda ya ga abin qi, to ya sauya shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, in ba zai iya ba, to da zuciyarsa, amma wannan shi ne mafi raunin imani.”

- Kar a boye hujja in dai har ta tabbata daga littafin Allah Madaukakin Sarki, ko sunnar Manzon Allah (SAW). Wasu daga cikin ayyukan kungiyar sun hada da:

Kasancewar wannan kungiya ta shahara sosai a kasashe daban-daban na duniya, wannan ya sa aka samar da kwamitoci daban-daban domin gabatar da ayyuka da yawa. Wasu daga cikin kwamitocin kungiyar sun hada da:

- Kwamitin Da’awah.

- Kwamitin Tarurrukan Wa’azi.

- Kwamitin Kula da Marayu

- Kwamitin Ilimi.

- Kwamitin Mutane Goma.

- Kwamitin Taimakon Gaggawa. KWAMITIN ZARTASWA

Shugabanta na kasa a wannan lokaci shi ne Sheikh Abdullahi Bala Lau, khalifa na farko a sashin shugabancin wannan kungiya tun bayan kafa kungiyar, wanda tsohon mataimakin shugaban kungiyar ne a zamanin shugabancin marigayi Alh. Musa maigandu Muhammad, kuma ya gaje shugabancin kungiyar ne bayan rasuwarsa.

- Alh. Azare: Mataimakin Shugaban Kungiya Na Kasa.

- Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe: Babban Magatakardan kungiya

- Sheik Sani Yaya Jingir: Shugaban Majalisar Malamai na kasa

- Sheik Yusuf Sambo Rigachuku: Mataimakin Majalisar Malamai na Kasa

- Alh. Isa Waziri: Shugaban Yan Agaji na Kasa

- Engr Mustapha Imam Sifti: Mataimakin Shugaban Rundunar Yan Aagaji na kasa

kungiyar ta samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya. A Najeriya tana da rassa a dukkanin jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya. Haka kuma saboda irin yadda kungiyar take kokarin ilmantar da al’umma, wannan ya sa har ta sami kutsawa zuwa ga wasu kasashe, kamar su; Nijar da Mali da Sinigal da Togo da Kamaru da Cadi da Burkina da Gini, Saudi Arabia da sauransu. Wasu daga cikin abubuwan da kungiyar ta mayar da hankali wajen yin su, sun hada da:

- Koyarwa a bisa tafarkin Manzon Allah (SAW) ba tare da bin son zuciya ko kuma yin makauniyar biyayya ga wani ba.

- Tsantsar karantar da hakikanin ilimin addinin Musulunci.

- Gabatar da wa’azin kasa a duk makwanni biyu ko uku ko hudu don tunatar da mutane abin da suka manta ko kuma lokutan da suka dace.

- Kafa makarantu domin koyar da ilimin addini da na boko, da sauran fannonin ilimi.

- Kai ziyarori gidajen marayu da gidajen yari da asibitoci, domin tallafar musulmai marasa galihu.

- Samar da taimakon gaggawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. kungiyar ta samar da hamshaqan malamai a sassa wadanda suka sami daukaka ta ilimi a fadin duniya baki daya, saboda jajircewa da kokarin bin tafarkin Manzon tsira, Annabi Muhammad (SAW), sau da kafa. Haka kuma ta ko wacce fuska tarihin izala zaizo , dogo ko gajere, ba za a taba mantawa da irin gudummar da marigayi Sheikh Isma'ila Idris Bin Zakariyya ya bada ba, da irinsu Marigayi Ibrahim Bawa Maishinkafa da Mal. Koda ba manufarmu zayyana sunan kowa ba, amma muna addu'a ga dukkan wadanda suka sadaukar da dukiyoyin su da kuma rayukansu akan wannan harka taci gaban addini, Allah ya saka musu da gidan Aljanna ya hada mu dasu a babban matsayi a lahira. Wannan kadan ne daga cikin irin manufofin da kungiyar Izala ta kafu a kayi, kuma a haka za'a tafi da ikon Allah. Daga Karshe Muna Addu'an Allah ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon binta, ya nuna mana karya karya ce ya bamu ikon guje mata.

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHƘungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), reshen Mararab...
14/08/2026

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUH

Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), reshen Mararaba Gurku, ƙarƙashin jagorancin Mal. Abdulaziz Usman Gusau, ta kai ziyara gidan gyaran hali (Correctional Centre) na Keffi.

A yayin wannan ziyara, Mal. Nura Muhammad Sagir (Abu Fatima), Sakataren Kwamitin Da’awa, ya yi wa waɗanda ke zaman gidan gyaran hali nasiha mai muhimmanci kan gyaran ɗabi’u da kyawawan halaye. Ya ja hankalinsu kan muhimmancin komawa ga kyawawan ɗabi’u, tare da jan hankali da cewa bai kamata mutum ya sake cutar da wani ko zaluntar kowa ba. Ya kuma ƙarfafa musu gwiwa da su yi amfani da wannan dama wajen gyara rayuwarsu da halayensu.

Daga bisani, Mal. Aliyu, wakilin Masallacin Zamani Estate, ya yi ta’aliƙi inda ya ƙara jaddada muhimmancin tuba da komawa ga Allah (SWT). Ya shawarce su da su ɗauki zaman da suke yi a gidan gyaran hali a matsayin wata dama ta gyara rayuwa, su bar munanan halaye, su rungumi kyawawan ɗabi’u da biyayya ga Allah.

A ƙarshen ziyarar, tawagar ta miƙa wa waɗanda ke gidan gyaran halin kayan tallafin da jama’a s**a bayar domin taimaka musu. Kayan tallafin sun haɗa da garri, s**ari, kwali-kwali da sabulun wanki (detergent).

Wakilan da s**a halarci ziyarar sun haɗa da:

1. Mal. Nura Muhammad Sagir (Abu Fatima) – Sakataren Kwamitin Da’awa kuma Shugaban Tafiyar.
2. Safwan Muhammad Musa – Memba na Kwamitin Da’awa, Sakataren Kwamitin Sadarwa, kuma Mataimakin Sakataren Majalisar Agaji ta Jaha.
3. Wakilai daga Masallacin Zamani Estate, waɗanda s**a haɗa da:
- Mal. Aliyu
- Mal. Mustapha
- Mal. Hamza

Muna roƙon Allah (SWT) Ya saka wa dukkan waɗanda s**a bayar da gudummawa da waɗanda s**a taimaka wajen ganin wannan ziyara ta gudana cikin nasara da alheri mai yawa.

Allah Ya kare mu daga shiga gidan gyaran hali, Ya tsare mu daga dukkan nau’o’in laifi da fitina, sannan Ya taimaki dukkan waɗanda suke ciki bisa gaskiya da adalci. Allah Ya ba su ikon tuba, Ya gyara rayuwarsu, Ya kuma sauƙaƙa musu.

Ameen Ya Rabbal Alameen.

Jazakumullahu Khairan.

Safwan Muhammad Musa
Sakataren Kwamitin Sadarwa,
JIBWIS Mararaba Gurku

01/08/2026

Live streaming of Haruna Halilu

RAHOTON ZIYARAR MARASA LAFIYA DA KWAMITIN DA'AWA NA JIBWIS RESHEN MARARABA GURKU YA KAIAssalamu Alaikum wa Rahmatullahi ...
25/07/2026

RAHOTON ZIYARAR MARASA LAFIYA DA KWAMITIN DA'AWA NA JIBWIS RESHEN MARARABA GURKU YA KAI

Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.

Kwamitin Da'awa na Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) reshen Mararaba Gurku, karkashin jagorancin Malam Hussaini Musa Abubakar (Abu Sumayya), ya gudanar da ziyarar marasa lafiya a matsayin daya daga cikin ayyukansa na da'awa da jin kai.

An gudanar da wannan ziyara ne a Medical Centre da ke Mararaba Gurku a yammacin ranar Asabar, 10 Safar 1447AH (25 ga Yuli, 2026).

Tawagar da ta halarci ziyarar ta kunshi:

1. Malam Aliyu Adam Bauchi – Mataimakin Shugaban Kwamitin Da'awa.
2. Malam Muhammad Nura Sagir – Sakataren Kwamitin Da'awa.
3. Malam Iliyasu Abubakar – Mataimakin Shugaban Kwamitin Tafsiri.
4. Alhaji Nasiru Danjindadi – Shugaban Kwamitin Masallacin Sautus Sunnah.
5. Safwan Muhammad Musa – Sakataren Kwamitin Sadarwa.
6. Da sauran 'yan uwa masu albarka.

A yayin ziyarar, an duba marasa lafiyar da ke karbar magani a asibitin, an yi musu addu'o'in Allah Ya ba su cikakkiyar lafiya cikin gaggawa, tare da ba su tallafi gwargwadon iko domin rage musu radadin halin da suke ciki.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya karbi wannan aiki a matsayin ibada, Ya saka wa duk wadanda s**a ba da gudummawa da alheri, Ya kuma ba marasa lafiya lafiya mai dorewa. Amin.

✍️ Safwan Muhammad Musa,
Sakataren Kwamitin Sadarwa
JIBWIS Reshen Mararaba Gurku

*JAMA'ATU IZAALATIL BID'AH WA'IQAAMATIS SUNNAH**MARARRABA BRANCH, KARU L.G.A.**WA'AZI! WA'AZI!! WA'AZI!!!*Assalamu Alaik...
16/07/2026

*JAMA'ATU IZAALATIL BID'AH WA'IQAAMATIS SUNNAH*

*MARARRABA BRANCH, KARU L.G.A.*

*WA'AZI! WA'AZI!! WA'AZI!!!*

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh,

*Shugaban wannan Qungiya mai Albarka Malam Abdul-Aziz Uthman Gusau*

*Shugaban Majalisar Malamai* Malam Yusuf Idris Farin Ruwa da

_*Da Shugaban Majalisar Agaji* Malam Ja'afar A. Usman_

*Da Shugaban Kwamitin Da'awa* _Malam Hussaini Musa (Abu Sumayyah)_

suna farin cikin gayyatarku wajen Wa'azin Sati biyu biyu Wanda aka saba shiryawa.

Wa'azin zai gudana kamar haka;

*Date*: _*Jumma'ah 2nd Safar, 1448 A.H. (17th July, 2026)*_

_1st Venue_: *_Masjid Abu Hurairah, Jiwapye phase 1, after Albarka Plaza, Maraba_*

_2nd Venue_: *Masjid Ɗantata Quarters, after Hamdala Bread, Maraba*

*Time*: _Bayan Sallar Maghrib (Between Maghrib and Isha'i)_

Allah Madaukakin Sarki ya bamu ikon Halarta.

*SANARWA daga Ofishin SAKATAREN Kwamitin Da'awa; Nura Muhammad Sagir (Abu Fatima)*
Ta Hannun: *Sakataren Kwamitin Sadarwa; Safwan Muhammad Musa*
*JIBWIS Social Media Mararaba Gurku_*

_Wassalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh_

28/06/2026

As Salamu alaykum Warahmatul lahi Wabarakatuhu.

*BARAR ADDU'A TARE DA JAJANTAWA*

Shugaban Kungiya Malam Abdul Aziz Usman Gusau.

Ya Umarce ni In Sanar Daku Ku Sanya Malam Idris Yunus (Bin Hazmin) Chairman Na Masallacin Umar Bin Khaddab Filin Idi Rugar Juli.

Cikin Addu'a Bisa Lalura Na Rashin Lafiya.

Allah Ta'ala Ya Ba shi Lafiya Yasa Kaffara Ne.

Was salamu alaykum.

Usman Ibrahim Nadabo Kankara Chairman Jibwis Social Media Mararabar Gurku

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu. *Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!* Shugaban JIBWIS Mararaba Gurku (Ma...
20/06/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.

*Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!*

Shugaban JIBWIS Mararaba Gurku (Mal. Abdulaziz Usman Gusau) yana sanar da al'ummar Musulmi rasuwar 'Yar Uwan Mal. Hussaini Musa, Shugaban Kwamitin Da'awa, wadda ta rasu bayan fama da jinya mai tsawo.

Za'a gudanar da sallar jana'izarta da misalin ƙarfe 9:00 na safe a Masallacin Sautus Sunnah, Ruga Market.

Muna roƙon Allah (SWT) Ya gafarta mata, Ya jikanta da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarta. Allah Ya ba iyalanta da 'yan uwanta haƙurin jure wannan babban rashi.
Ameeeen ya Rahman

✍️
Safwan Muhammad Musa,
Sakatare,
Kwamitin Sadarwa,
JIBWIS Mararaba Gurku.

As salamu alaykum Warahmatul lahi Wabarakatuhu.*SA'KON GAISUWAR SALLAH*Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a, Wa Iqamatis Su...
29/05/2026

As salamu alaykum Warahmatul lahi Wabarakatuhu.

*SA'KON GAISUWAR SALLAH*

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a, Wa Iqamatis Sunnah Garin Mararabar Gurku Karamar Hukumar Karu Jahar Nasarawa.

Karkashin Jagorancin Sheikh Abdul Aziz Usman Gusau.

Tana Taya Membobin ta Da Dukkan Sauran Al Ummar Musulmi Murna Tare da Yi Masu Gaisuwar Barka Da Sallah.

Muna Rokon Allah Ta'ala Ya Karbi Ibadunmu Baki Daya Ya Gafarta Mana Kurakuran mu.

Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.

Usman Ibrahim Nadabo Kankara
Chairman Social Media Jibwis Mararabar Gurku. Amadadin Jibwis Mararabar Gurku.

Assalamu Alaikum,JAMAA'ATU IZALATIL BID'AH WA'IQAMATIS-SUNNAH MARARRABA BRANCH, KARU L.G.A.Ga Jadawalin Wa'azi Sati Biyu...
07/04/2026

Assalamu Alaikum,
JAMAA'ATU IZALATIL BID'AH WA'IQAMATIS-SUNNAH MARARRABA BRANCH, KARU L.G.A.

Ga Jadawalin Wa'azi Sati Biyu - Biyu DA Sauran Ayyukan Kwamitin Da'awa na shekaran 1447AH/1448AH (2026M/2027M) karkashin JIBWIS Mararaba Gurku, Karu LGA, Nasarawa State.

Sanarwa Daga Ofishin Sakataren Kwamitin Da'awa; Muhammad Nura Abu Fatima
Ta Hannun;
Sakataren Kwamitin Yaɗa Labarai(Social Media); Safwan Muhammad Musa

Address

Jum'at Masjid, Unguwar Katsinawa, Maraba Karu LGA
Nasarawa

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when JIBWIS Mararaba Gurku posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to JIBWIS Mararaba Gurku:

Shortcuts

Share