Borno Youth For Progress

Directions

Borno Youth For Progress Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Borno Youth For Progress, Community Organization, Maiduguri.

Jiya Wani ɗan APC ya zage ni, sai na bi shi (DM) da misalin ƙarfe 10 na dare nace ya turamin Opay ɗinsa. Ya turo mini, s...
02/10/2026

Jiya Wani ɗan APC ya zage ni, sai na bi shi (DM) da misalin ƙarfe 10 na dare nace ya turamin Opay ɗinsa. Ya turo mini, sai na ce masa zan tura masa kuɗi kafin ya kwanta, daga baya na tura masa wannan receipt ɗin👇 nace "na tura"
‎
‎Ban tura masa kuɗin ba, kawai ina so ya ɗanɗana yadda alkawuran ƙarya da farfagandar APC ke cutar da Nijeriya ne.
‎
‎Tun jiya yake ta min text, yamin kusan guda 20 yana cewa bai ga kuɗin ba, nikuwa na kyalesa,
‎
‎Saiyau da safe na amsa masa da cewa zai gani sanda 'yan Nijeriya s**a ga amfanin sauye-sauyen Tinubu da yake tallata mana.
👀

Labarin Alhaji Nafiu Isyaku Rabiu: Arziki, Kisa da Shari’ar da Ta Girgiza KanoAlhaji Nafiu Isyaku Rabiu ya kasance fitac...
28/08/2026

Labarin Alhaji Nafiu Isyaku Rabiu: Arziki, Kisa da Shari’ar da Ta Girgiza Kano

Alhaji Nafiu Isyaku Rabiu ya kasance fitaccen attajiri kuma ɗan kasuwa a Kano a shekarun 1970. Shi ne babban ɗan marigayi Sheikh Isyaku Rabiu, kuma babban ɗan’uwa ga hamshakin attajiri Abdul Samad Rabiu, wanda ya kafa rukunin Kamfanonin BUA wato (BUA Group).

A wancan lokaci, Nafiu ya shahara da rayuwar alfarma. An ce yana da motocin Rolls-Royce guda biyu, wasu motocin tsada da kuma jiragen sama masu zaman kansu guda biyu. Rayuwarsa ta alfarma har ta fito a wani shirin BBC da NTA na shekarar 1984 mai suna Nigeria: A Squandering of Riches.
Sai dai rayuwarsa ta sauya gaba ɗaya bayan mutuwar matarsa, Fatima Rabiu, a ranar 10 ga Mayu, 1979.

A daren 9 ga Mayu, Nafiu da Fatima sun shirya liyafar cin abinci a gidansu da ke Dawaki Road, Kano. Baƙi sun bar gidan da misalin ƙarfe 11 na dare, kuma sun ce ma’auratan suna cikin koshin lafiya.

Washegari, an gano Fatima a cikin ɗakinta a mace. An kuma ga alamun raunuka da ake zargin sun shafi shakewa a wuyanta.
Lamarin ya tayar da hankali sosai saboda Fatima ’yar shahararren attajirin Kano, Tijjani Aliyu Dagazau, ce, yayin da Nafiu shi ma yake daga cikin manyan attajiran lokacin.

Gwamnatin Kano ƙarƙashin Gwamna Muhammadu Abubakar Rimi ta matsa sosai wajen ganin an gurfanar da Nafiu tare da neman hukuncin kisa.

Sai dai a shari’ar farko, lauyoyin Nafiu sun yi amfani da wasu kura-kurai a cikin shaidun likitoci, musamman kan ko an tabbatar da cewa shakewa ce ta haddasa mutuwar Fatima. A ƙarshe, Babbar Kotun ta wanke Nafiu.

Hukuncin ya jawo fushi da zanga-zanga daga wasu jama’a waɗanda s**a yi ganin cewa kuɗi da matsayi na iya ba mutum kariya daga doka.
Gwamnatin Kano ta ɗaukaka ƙarar zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara. Kotun ta soke hukuncin wanke Nafiu, ta same shi da laifin culpable homicide, wato kisan kai wanda ba ya ɗaukar hukuncin kisa, sannan ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru huɗu.

Nafiu bai yarda da hukuncin ba, ya garzaya Kotun Ƙoli. Ya ɗauki shahararren lauya Chief F.R.A. Williams, SAN, yayin da gwamnati ta samu wakilcin Kehinde Sofola, SAN.
Babban abin da lauyan Nafiu ya ƙalubalanta ba wai kawai batun kisan ba ne, sai dai ikon gwamnati na ɗaukaka ƙarar mutum da aka wanke daga laifi. Wannan ya haifar da wata muhimmiyar shari’a mai suna Nafiu Rabiu v. The State (1980).

Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa gwamnati tana da ikon ɗaukaka irin wannan ƙara, tare da kafa muhimmiyar ƙa’ida kan yadda ake fassara Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

An kuma samu cewa gwamnatin Kano ta janye ƙarar da take neman a yanke wa Nafiu hukuncin kisa. Saboda haka, Kotun Ƙoli ba ta iya ƙara masa hukunci sama da abin da ke gaban ta ba. Daga ƙarshe, Nafiu ya ci gaba da ɗaurin shekaru huɗu.

Bayan fitarsa daga gidan yari, Nafiu ya janye gaba ɗaya daga rayuwar alfarma da shahara. Ya daina fitowa a tarukan jama’a, ya bar rayuwar motocin alfarma da jiragen sama, kuma ya kasance cikin sirri har tsawon rayuwarsa.

A yau, shari’ar Nafiu Rabiu tana daga cikin shari’o’in da s**a yi tasiri sosai a tarihin tsarin shari’a na Najeriya. Kotun da aka gudanar da shari’ar a Kano har yanzu wasu ke kiranta da “Kotun Nafiu.”

Rahoto TY Hausa

07/06/2026

1. Ko nawa kake samu, idan kana kashi shi gaba-daya, kusan daidai kake da mai ƙaramin samu. Kuma zaka kasance cikin matsalar kudi.

Dalili: Wata bukata zata taso maka wacce baka shirya mata ba, kuma zata fi karfin ka.

2. Komai kankantar abinda kake ajiyewa (Small Savings) sannu a hankali zai zama kudi masu tarin yawa da zaka iya samar da jari ko mallakar kadara.

Hikima: Abinda kake ajiyewa cikin samun ka, shine arzikin ka ba abinda ka kashe ba.

3. Dabarun da kake amfani dasu wajen neman kudi sune babban jarin ka. Don haka kana bukatar cigaba da koyon sabbin dabaru (Skills) domin dorewar kasuwancin ka ko sana'ar ka.
Dalili: Jari (Capital) yana iya lalacewa, amma ilimi da basirar data tara jarin tana nan, kuma zata iya sake tara wani jarin.

4. Dukiya tana taruwa ne sannu a hankali, biyo bayan aiki tukuru tare da dorewa tsahon lokaci (Consistency)

Hikima: Kada kace wane Sa'a ce kawai dashi, a'a akwai wani aiki daya dore a kansa, wanda sakamakon wannan hidimar ne Allah SWT ya taimake shi. Amma kai sakamakon kawai kake gani ba waccen boyayyiyar hidimar ba

5. Wadata (Financial freedom) tana bukatar lokaci, hakuri da juriya (Persistency) kafin ta ginu, ba aikin rana daya bace.

Hikima: Kana bukatar tarbiyyar zuciya (Discipline) da tattali har ka gina wani abu mai girma.

Allah ya bamu sa'a da rabo.

©️ Bello Ado Hussaini

“Tinubu is building Lagos. Tinubu is building his people”Who stopped your brother from building his people? Who stopped ...
01/04/2026

“Tinubu is building Lagos. Tinubu is building his people”

Who stopped your brother from building his people?

Who stopped your brother from building the North?

Tinubu, we are proud of you. Your statesmanship and strategy are worthy of emulation.

PRESS RELEASEZulum Dissolves Borno State Executive CouncilBorno State Governor, Professor Babagana Umara Zulum, has appr...
30/03/2026

PRESS RELEASE

Zulum Dissolves Borno State Executive Council

Borno State Governor, Professor Babagana Umara Zulum, has approved the immediate dissolution of the State Executive Council.

The decision is to provide an enabling environment for any member of the council who may wish to contest elective positions in the forthcoming general elections.

The Governor has therefore directed all Commissioners to hand over the affairs of their respective ministries to the Permanent Secretaries on or before Friday, April 3, 2026.

Governor Zulum expressed his profound appreciation to the outgoing Commissioners for their dedication, commitment, and invaluable contributions to the development and service of the people of Borno State.

Signed:
Bukar Tijani FASN, FSSN, JAAS
Secretary to the Borno State Government

Asirin Pasto Mamman Mamman ya Tonu:Wasu masu binciken Kwakwaf sun yi zurfin bincike akan wannan pasto mai yaɗa daawar Ki...
21/02/2026

Asirin Pasto Mamman Mamman ya Tonu:

Wasu masu binciken Kwakwaf sun yi zurfin bincike akan wannan pasto mai yaɗa daawar Kiristoci. Wanda yake kiran kansa da pastor Mohammed Mohammed.

Ashe dai asalin sunan shi Daniel, ba Mohammed ba kamar yadda ya sanya wa kansa domin ɓata wa Musulmai Rai.

An gano kalandar aurenshi da ya yi da tsohuwar matarshi ta farko mai suna La'atu. Anyi aure tsakanin La'atu da Daniel tun lokacinda bai fara harkar daawar Kiristoci ba.

Dan haka yanzu babu wani ɓoye ɓoye da ya rage, daka wanda ya sake kiransa Mamman, Ballantana kuma Muhammed. Sunan shi Daniel

Wannan bincike ya yi daɗi sosai. Dama su aikin ƴan bazata Kenan. Kullum so suke yi su ɓatar da jahilan Musulmai marasa Ilmi

Idan ya musanta wannan bincike, sai a tamabaye shi, ta yaya ne Daniel ya koma Mohammed?

Address

Maiduguri

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Borno Youth For Progress posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share