10/09/2025
Shin kun san menene yaƙi?😭💔 Inna lillahi Wa Inna ilaihi Raji'un,
Jama'a mu guji duk abunda zai sabbaba mana yaƙi a garuruwan mu ko a ƙasar mu, yaƙi yana sauya duk wani tarihin jin daɗi yana rusa farin ciki ya dasa baƙin ciki mara misaltuwa mara ƙarshe a zukatan waƴanda annobar yaƙi ta afka musu,
Miloniya zai zama talaka fitik mai rufin asiri ya koma sansanin gudun hijira, shagon ka motar ka da wasu abubuwan more rayuwar ka zaka wayi gari ka rasa su duk katsiyace Malam, magidanci da iyalansa zasu iya wayar gari tare zuwa yammaci zasu iya yin wata rabuwa wacce wani bazai ƙara ganin wani ba, makarantu asibitoci ɗakunan Shari'a (Kotu) ofisoshin ƴan sanda da cibiyoyin gudanar da ayyukan al'umma duk zasu zama kufai, wlh duk naga wannan da ido na na zauna da waƴanda s**a watse daga gidajen su har yanzu basu haɗu da wasu ƴan uwan nasu ba.
Talaka zai iya kwantar da mai mulki ya masa yankan rago a ƙone gidan mai mulki a ɗebi ganima in dama ta samu, Wlh duk waƴannan misallan Ni mai rubutun naga makamantansu a cikin jihar Borno da kewaye, a shekarar 2016 bayan Sojojin Chadi da haɗin gwiwar na Nigeria sun ƴanto garin Dikwa daga hannun mayaƙan Boko Haram da s**a shafe kusan shekaru biyu a cikin garin an bawa wasu tsirarun mutane damar zuwa garuruwan da suke yankin tare da rakiyar manyan makamai da motocin yaƙi da tawagar sojoji polisawa Immigration Customs Civil Defence ƴan gora dss nau'ikan jami'an tsaro kala kala,
Ina cikin tawagar a lokacin da mukaje garin Dikwa babu kowa garin ya zama kufai LGA ne mai zaman kansa, muna neman ruwa babu ruwa sai wani Free Flow irin ruwan da yake zuba baya yankewa a cikin fadar Shehun Dikwa sarki mai daraja daga Shehun Borno sai shi a darajar sarauta, da muka shiga fadar domin ɗiban ruwa mun tarar an babbake fadar a ƙone komai motocin alfarma da kayan alatu da kujerun sarauta masu tsada da kayan amfanin gidan duka,
A cikin fadar mun zaɓi inda muke so munyi wanka mun ɗau hotuna wasu sun zauna akan ƙonannun kujerun sarki wanda yake zaman Fada akan su wasu a cikin dakin da sarki yake zaman Fada s**ayi wanka babu inda bamu leƙa ba a cikin gidan domin ya zama kufai saboda bala'i sarki ya gudu ya bar kyakkyawar fadar sa da kayan alatu tsawon shekaru biyu da watanni,
Wannan tafiyar da mukayi abunda muka gani na tashin hankali a garuruwa mabanbanta wlh ko a video cikin awa ɗaya bazan iya bada lbrn duka abunda na gani na tashin hankali ba, tun lokacin nake Respecting ɗin zaman lfy bana son abunda zai hargitsa zaman lfyr mutane, a wannan gaɓar ina jan hankulan mutanen mu na Arewa wlh mu girmama zaman lfy kada mu yadda da duk wani abu da zai zama sanadiyar yaƙi a yankin mu, muyi duk wani yunƙuri koda na saida rai ne domin tsare zaman lfyr al'ummar mu, mu tona asirin ƴan ta'adda mu bada bayanan sirri akan su babu tsoro ko shakku,
Maciya amana daga cikin shugabannin mu masu cin amanar mu waƴanda s**a siyasantar da tsaron rayukan mu da mutuncin mu a kullum suna mana sharar fage domin gwara kan mu musamman masu Control ɗin Banditry a Arewa maso yamma tabbas bamuda maƙiyan da s**a kai su, abunda suke haddasawa na ƙiyayya da gaba tsakanin Hausawa da Fulani yanzu yafi komai muni a Arewacin Nigeria, Result ɗin da zai haifar in bamuyi hankali ba mun kawo ƙarshen duk masu hannu a cikin sa to wataran abunda hakan zai haifar sai yafi yaƙin Boko Haram illata mu Allah ya kiyaye,
Allah yana gani sunfi ƙarfin mu ta ɓangarori da dama Allah ya mana maganin su ya wulakanta su ya ɗaiɗaita su ya bamu ikon share su daga cikin mu.
✍️
Isa Mohammad (Abu Sadiq Al'Nigeria) shugaban kungiyar Arewa Youths Concern Media Forum