Arewa Youth Consultative Forum Aycf Lagos State Chapter

Arewa Youth Consultative Forum Aycf Lagos State Chapter Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Arewa Youth Consultative Forum Aycf Lagos State Chapter, Non-Governmental Organization (NGO), Lagos.

15/11/2025

YA KAMATA 'YAN AREWA MU FARKA DAGA BACCIN DA MUKE YI!!!

Don Allah jama'a ku kalli yanda jami'an hukumar Kick Against Indiscipline (KAI) suke farautar masu bara 'yan Arewa a jahar Lagos.

Tabbas bara ba sana'a bane, kaskanci ne kawai da wulakanci, kuma bugu da kari haramun ne a shari'ar musulunci, sai idan akwai wata maslaha wacce ta tilastawa mutum bara zuwa wani lokaci kayyadadde.

Tuni dai shugabannin kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) s**a shiga lamarin, inda s**a garzaya har Alausa Ikeja wajan ganin an yiwa wadannan mutane adalci, ta yanda za'a saki wadanda basu cancanta a k**a su ba, saboda lalular dake tare dasu, kuma a hukunta wadanda s**a cancanta a hukunta saboda laifin su.

Daga karshe muna kira na musamman ga 'yan uwanmu 'yan Arewa akan duk wanda yasan cewa yanada dan uwa mai bara a Legas, yayi kokarin mayar dashi gida Arewa saboda gomnatin Legas ta haramta bara, kuma ta saka kafar wando daya ga dukkanin mabarata a fadin jahar Legas baki daya.

✍️Barr Aminu Imam Salihu
AYCF Lagos State Deputy Chairman & State Legal Adviser.
15/November/2025.

GREAT AREWA!!! GREAT AREWA!!!!!Ziyara ta musamman zuwa ga gidan radion Bond Fm Lagos inda na wakilci kungiyar Arewa Yout...
07/10/2025

GREAT AREWA!!! GREAT AREWA!!!!!

Ziyara ta musamman zuwa ga gidan radion Bond Fm Lagos inda na wakilci kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) reshen jahar Lagos inda muka tattauna muhimman abubuwa da s**a shafi 'yan Arewa mazauna Lagos tareda kokarin da kungiyar AYCF takeyi don taimakon 'yan Arewa da tabbatar da hadin kai tsakanin 'yan Arewa da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jahar Lagos baki daya.

Alhaji Usman Tunau shine dan jaridar ya jagoranci wannan tattaunawa sai kuma ni comrade barrister Aminu Imam Salihu mataimakin shugaba na jahar Lagos kuma lauya mai baiwa kungiya shawara gameda abinda ya shafi harkokin dokokin kasa da constitution da sauransu. Wannan kungiya ta AYCF mai albarka ta shafe sama da shekaru ashirin da biyar tana taimakon 'yan Arewa mazauna jahar Lagos ta hanyoyin daban daban da kuma magance matsaloli daban daban.

Da fatan Allah ya kara mana hadin kai atsakanin al'ummarmu na Arewa, ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jahar Lagos da jahohinmu na Arewa da kuma Nigeria baki daya.

Long live AYCF
Long live Lagos State
Long live Northern States
Long live Federal Republic of Nigeria.πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬πŸ‡³πŸ‡¬

✍️ Barr Aminu Imam Salihu
AYCF Lagos state Deputy Chairman & Legal adviser.

12/04/1447
04/10/2025.

09/09/2025

Rashin hadin kan 'yan Arewa a Lagos shine dalilin da yasa ake raina mu ake wulakantamu wanda hakan shi yayi sanadiyyar rusa kasuwar Alaba rago.

Daga bakin Sheikh Sulaiman Ibrahim shugaban Kungiyar Izalah na Jahar Lagos.


Lagos State Chapter.

KUNGIYAR AREWA YOUTH CONSULTATIVE FORUM (AYCF) TA KAI ZIYARA UNGUWANNIN AMUKOKO DA KUMA ALABA RAGO DON GABATAR DA JAJE G...
08/09/2025

KUNGIYAR AREWA YOUTH CONSULTATIVE FORUM (AYCF) TA KAI ZIYARA UNGUWANNIN AMUKOKO DA KUMA ALABA RAGO DON GABATAR DA JAJE GAMEDA RUSHE RUSHE DA GOMNATIN JAHAR LAGOS TAYI A CIKIN KASUWAR ALABA

Yau Lahadi cikin ikon Allah kungiyar AYCF ta kai ziyara ta musamman zuwa fadar mai martaba Sarkin unguwar Amukoko, da kuma shugabanni da al'ummar Alaba Rago, bisa ibtila'in rushe rushe da gomnatin Jahar Lagos tayi, a cikin babbar kasuwar Alaba rago mai dimbin tarihi.

Mai martaba Sarkin Amukoko ya nuna matukar farin cikinsa da kuma godiya akan wannan ziyarar ta zumunci, inda yayi mana addu'a da fatan alheri da kuma jaddada goyon bayansa ga wannan kungiya mai albarka.

Daga bisani kungiyar ta karasa cikin kasuwar Alaba rago inda anan mukayi sallar Azahar, kuma bayan an gama sallah shugabannin kungiyar AYCF sun gabatar da jawabai masu matukar Muhimmanci da sosa zuciya, inda s**a ja hankalin al'ummar Alaba rago akan Muhimmancin hadin kai da kuma illar rabuwar kai, wanda wannan matsalar ta rashin kai itace ta jawo gomnatin Jahar Lagos tayi abinda tayi na rusau a kasuwar Alaba rago.

Shugannin AYCF da s**a gabatar da jawabai sun hada da comrade Alhaji Kudu Abubakar National Deputy Chairman, da Alhaji Adamu Yahya Haruna Lagos State Chairman, sai kuma Comrade Barrister Aminu Imam Salihu Deputy Chairman Lagos State.

Daga karshe an gabatar da addu'o'i na musamman ga al'ummar Alaba Rago wadanda wannan musiba ta shafe su, akan Allah ya kiyaye gaba kuma ya mayar da mafi alherin abinda s**a rasa.

✍️ Barr Aminu Imam Salihu
AYCF Deputy Chairman/ Legal adviser
14/Rabi'ul Awwal 1447
07/September/2025.

07/09/2025

AREWA YOUTH CONSULTATIVE FORUM (AYCF) LAGOS STATE CHAPTER

07/09/2025

Address

Lagos

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Youth Consultative Forum Aycf Lagos State Chapter posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share