11/10/2026
SANARWAR NUNA GOYAN BAYA GA KWAMITIN SHIRYA TATTAKIN LUMANA DOMIN TABBATA DA NADIN MAI MARTABA SARKIN HAUSAWA IBADANLAND MUHAMMAD DIKKO.
Majalisar zartarwa wannan Kungiya mai albarka, karkashin jagorancin Nafiu M. Abdallah, tana mai kara jaddada mubaya’arta tare da nuna goyon bayanta, ga kwamitin da gamayyun kungiyoyin wannan gari na coalition of youth for social development s**a kirkira, domin suyi hobbasa, tare da daukan sabbin matakai wanda dokar kasa ta Aminta da su , don tabbatar da anyi adalci an kuma tabbatar da gaskia , da adalci a gurbin su.
Kamar yadda muka sani, wadan nan gamayyun Kungiyoyi sun hade da curewa waje daya , domin tabbatar da cigaban al’umma, zaman lafiya , yalwatuwar arziki , dakuma cigaban garin Sabo ibadan , dama al’ummar Hausawa mazauna kudanci gaba daya.
Akan magana danbarwa sarauta wannan masarauta kuwa, kungiyar ta na kara tabbatar da matsayarta cewa tana nan akan bakanta na tsayawa dari bisa dari tare mai martaba muhammadu Dikko, ba saboda komai ba ,sai dan kasancewar shi zabin Allah , zabin al’umma, kuma wanda Kungiyar ke mishi kyakkyawan zato , tare da natijar da yake da shi na dattako, da kuma yakinin ciyar da wannan masauta dama dukkanin al’ummar dake karkashin ta gaba.
Muna kara tunatar da al’umma cewa wannan Kungiya bata nuna kiyayya ko bangaran ci ga wani sashe, face, duba maslahar al’ummar da kuma maslahar gari gaba daya, domin ba mu da garin da muke tutiya da Fariya da shi bayan maka da madina, sai wannan unguwa ta mu ta (SABO).
Akarshe muna kara kira ga dukkanin wadan da suke da ruwa da tsaki akan wannan danbarwa, cewa, su yi wa Allah da Annabinsa, su duba maslahar gari da kuma zaman lafiyar garin da cigaban al’ummar dake karkashin wannan masarauta, fiye da son zuciyar su. Sannan muna kara jinjinawa dukkanin malaman mu da s**a dau lokaci suna ta kokari ganin an samu maslaha akan wannan lamari, fatan Allah ya kara musu lafiya ya kuma saka musu da mafifici alheri.
Signed
NAFIU M. ABDALLAH.
chairman, Sabo youth Alliance.
Sunday , 11, October 2026.