17/08/2026
MUHADARAR DALIBAI: KUNGIYAR HADIN KAN MAKARANTUN ISLAMIYYUN AHLUS-SUNNAH TA KURMIN MASHI TA SHIRYA TARO NA ILIMANTARWA
Kungiyar Hadin Kan Makarantun Islamiyyun Ahlus-Sunnah ta Kurmin Mashi, Kaduna, ta shirya wata muhimmiyar muhadara ga dalibai, domin wayar da kansu kan muhimmancin neman ilimi da kuma yadda za su yi amfani da ilimin da suke samu wajen inganta rayuwarsu da al’umma.
Shugaban kungiyar, Dr. Muhammad Salis Abdulhamid, wanda aka fi sani da Ustaz Nahda, kuma limamin Masallacin Aliyu bn Usman da ke NDA Road, ne ke jagorantar kungiyar tare da hadin gwiwar sauran malamai.
Kungiyar ta shafe kimanin shekaru takwas tana gudanar da ayyukan ilimantarwa da bunkasa ilimin addini a unguwar Kurmin Mashi, Kaduna.
A yayin muhadarar, babban malamin addini, Malam Aminu Ibrahim Sautus-Sunnah, ya gabatar da karatun ranar Lahadi da safiya, inda ya yi bayani kan muhimmancin neman ilimi, fahimtarsa da kuma wajabcin aiki da abin da mutum ya koya.
Taron ya samu halartar malamai da dama, shugabannin makarantun Islamiyya, da iyaye, musamman iyaye mata daga sassa daban-daban na Kurmin Mashi. Haka kuma, Sarkin Sabon Layi, Malam Abdullahi Rabo, ya kasance cikin manyan bakin da s**a halarci taron.
An gudanar da muhadarar ne a Masallacin Yar Makwallan, Sabon Layi, Kaduna, inda mahalarta s**a samu damar sauraron darussa da nasihohi masu muhimmanci.
Masu shirya taron sun bayyana fatan cewa mahalarta za su amfana da darussan da aka gabatar, tare da daukar nauyin amfani da ilimin wajen kyautata rayuwarsu da al’umma.
Daga Abu Hisham, K-Mashi Voice.