Shinkafi 'B' Consultative Forum - SCF

Shinkafi 'B' Consultative Forum - SCF Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Shinkafi 'B' Consultative Forum - SCF, Nonprofit Organization, Katsina.

28/05/2026

Eid Mubarak

SHINKAFI ‘B’ CONSULTATIVE FORUMSAƘON BARKA DA SALLAHShugabanci da ɗaukacin mambobin SHINKAFI ‘B’ CONSULTATIVE FORUM na m...
28/05/2026

SHINKAFI ‘B’ CONSULTATIVE FORUM
SAƘON BARKA DA SALLAH
Shugabanci da ɗaukacin mambobin SHINKAFI ‘B’ CONSULTATIVE FORUM na miƙa saƙon taya murnar zagayowar Babbar Sallah ta Eid-el-Kabir ga dukkan al’ummar Musulmi, musamman ga mambobin ƙungiyar, Kwamitin Amintattu da Kwamitin Gudanarwa.
Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi ibadunmu da sadaukarwarmu, Ya sanya wannan Sallah ta zama alheri, haɗin kai da ci gaba ga al’ummarmu.
Allah Ya maimaita mana da zaman lafiya, yalwa da ɗorewar zumunci.
Barka da Sallah.
“Voices United. Futures Shaped.”

Sanarwa:
Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa
28 ga Mayu, 2026
11 ga Dhul-Hijjah, 1447

10/05/2026

Report by the Katsina State Television (KTTV) on the inauguration of the leadership of the Shinkafi 'B' Consultative Forum (SCF), held at Abba Saude House today, Sunday, May 10, 2026.
May Allah grant them the strength and ability to successfully carry out their responsibilities. Amin.

10/05/2026

Rahoton Gidan Talabijin na Jihar Katsina (KTTV) na yanda aka ƙaddamar da Shugabannin Ƙungiyar Tuntuɓa ta Shinkafi 'B' watau Shinkafi 'B' Consultative Forum (SCF) a Abba Saude House Birnin Katsina a yau Lahadi, 10 ga Mayu, 2026.
Da fatan Allah Ya basu ikon sauke nauyi. Amin

Masha Allah FALKE PAGE.
09/05/2026

Masha Allah FALKE PAGE.

“Daga Wayar da Kai Zuwa Aminci: Tattara Matasa da Al’umma Domin Manufa Ta Bai Ɗaya ta Ci Gaba”Taken taron kenan a gobe I...
09/05/2026

“Daga Wayar da Kai Zuwa Aminci: Tattara Matasa da Al’umma Domin Manufa Ta Bai Ɗaya ta Ci Gaba”

Taken taron kenan a gobe Insha Allahu

09/05/2026

Awa 24 ya rage Insha Allah

Saura awa 48 Insha Allahu domin ƙaddamar da Ƙungiyar Tuntuɓa ta Shinkafi 'B'.Allah Ya bayar da ikon halarta. Amin
08/05/2026

Saura awa 48 Insha Allahu domin ƙaddamar da Ƙungiyar Tuntuɓa ta Shinkafi 'B'.
Allah Ya bayar da ikon halarta. Amin

Ƙarin Tunatarwa kan Tsarin Shirin CDP ga Al'ummar Shinkafi 'B' - Kambarawa, Kwaɗo, Modoji, Maƙera, Bakuru da Kadafawa JA...
06/04/2026

Ƙarin Tunatarwa kan Tsarin Shirin CDP ga Al'ummar Shinkafi 'B' - Kambarawa, Kwaɗo, Modoji, Maƙera, Bakuru da Kadafawa

JADDAWALIN WAKILAN KWAMITIN GUNDUMA (CLC) DA KUMA TSARIN GUDANARWARSU

A ƙoƙarin da muke tayi na juyo da hankulan al'ummar mu kan wannan shiri na raya Gundumomi (Ward Development) da Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, PhD, CON ya kawo domin kyautata rayuwar al'umma, yau, za mu fitar wa al'umma jerin wakilan da ya kamata kowane kwamiti ya ƙunsa da kuma hanyar tafiyar da aikin shi.

A kowace gunduma/mazaɓa (ward), akwai ma'aikata guda uku (3) na ƙaramar hukuma da aka ɗauka aiki wanda kuma suke cikin tsarin ma'aikatan gwamnati tsawon lokaci, sai dai kusan ayyukan da suke yau da goben tsarin aiki ya haɗiye su. Amma ɓullo da wannan shiri na CDP ya busa masu sabon rai a cikin aikin nasu.

Waɗannan ma'aikata su ne;
1. Community Development Officer (CDO)
2. Community Learning Officer (CLO) sai kuma;
3. Community Support Officer (CSO).

Domin kiyaye ƙa'ida da sharuɗɗan aiki, sai aka damƙa alhakin jagorancin wannan kwamiti a hannun su, musamman shi/ita CDO a matsayin shugaban kwamitin.

Sauran wakilan kwamiti su ne kamar haka;

1. Kansila
2. Maigari
3. Dattawa guda uku
4. Liman Ɗariƙa
5. Liman Izala
6. Wakilin masu buƙata ta musamman
7. Wakiliyar Mata
8. Wakilin Matasa
9. Hedimasta
10. Wakilin 'yan kasuwa
11. Malamin Gona
12. Malamin Asibiti

Idan muka haɗa lissafin gaba ɗaya za mu sami mutum goma sha bakwai (17) a matsayin 'yan wannan kwamiti na gunduma, Community Level Committee (CLC).

Waɗannan bayin Allah su aka ɗora ma alhakin tafiyar da wannan kwamiti, domin gudanar da duk ayyukan da s**a shafi gundumar a ƙarƙashin wannan shiri na CDP.

Duk abinda za a nema ko za a gudanar, to wajibi ne duka sai wannan 'yan kwamiti sun zauna sun cimma matsaya kafin gabatarwa ko gudanarwa. Idan faɗin lamarin ya wuce iyawar su, to sai su tara al'umma a ofishin su na gunduma domin a tattauna a sami matsaya.

Babu wani mutum ɗaya da aka ba damar yin gaban kanshi kan duk wani abu da da ya shafi wannan gunduma ba tare da sauran wakilan kwamitin ba.

Maganar gudanar da ayyuka a cikin shirin Naira Miliyan Goma Goma (N10, 000, 000) da aka aje ma kowace gunduma a asusun ajiyar ta na banki, shirin raba kayan noma na zamani, rabon takin zamani, rabon kayan cimaka da ma duk wani abin da ya shafi gunduma, to a wannan tsarin ake tafiyar dashi, inda kuma al'umma s**a fahimci ba kan haka suke ba, to suyi maza su sanar da babban ofishin gudanarwa na CDP wanda ke ƙarƙashin jagorancin Kamaluddeen Kabir Katsina domin yin gyaran da ya kamata.

CDP (Katsina State Community Development Programme) ɗin nan ta al'umma ce kuma don al'umma aka yi ta. Wajibi ne al'umma su maido hankulan su kan ta domin cin gajiyar alheran da tazo dasu.

Ya Allah Ka iya mana, kai mana maganin abinda ya ishe mu.

Shinkafi 'B' Consultative Forum (SCF)
Litinin, 6 ga Afrilu, 2026
18 ga Shawwal, 1447

Katsina State Community Development Programme
Wakeup Katsina-Youth

Labari cikin Hotuna:Zaman Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Tuntuɓa ta Shinkafi 'B' watau Shinkafi 'B' Consultative Forum (...
06/04/2026

Labari cikin Hotuna:
Zaman Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Tuntuɓa ta Shinkafi 'B' watau Shinkafi 'B' Consultative Forum (SCF) karo na Tara (9) kenan a jiya Lahadi, 5 ga Afrilu, 2026, da ya gudana a Asibitin Mata da Ƙananan Yara da ke Unguwar Kwaɗo.
Taron ya maida hankali kan ci gaba da shirye-shiryen ƙaddamar da membobin Kwamitin Gudanarwa da zasu yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da Babban Daraktan Ƙungiyar da aka tabbatar a shekarar da ta gabata, 2025.
Waɗannan membobi an zaƙulosu ne daga yankunan Mazaɓar Shinkafi 'B' guda shida (6) na Kambarawa, Kwaɗo, Modoji, Maƙera, Bakuru da Kadafawa.
Shirye-shirye zasu ci gaba Insha Allahu.
Da fatan Allah Ya yi riƙo da hannuwan wannan Ƙungiya.
Amin Ya Hayyu Ya Qayyum

Address

Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Shinkafi 'B' Consultative Forum - SCF posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share