21/04/2026
KARIN BAYANI GAME DA SAYAR DA TAKIN NOMAN DAMINAR BANA (2026 RAINY SEASON)
(1) Ƴan kwamitin CLC na kowace gunduma (Ward) za su raba kawunansu gida ukku, amma kuma CDO, CLO, CSO su kasance ba a hada (gwamawa) su a cikin gida daya ba.
(2) Za a raba daukacin rumfunan da ke a gunduma zuwa gida ukku, sannan kowane gida za su zagaya rumfa bayan rumfa. Akowace rumfa, za su zauna da mutanen da ke wannan rumfar, da Exco da ke rumfar, da masu ruwa-da-tsaki, da kuma shuwagabannin rumfa.
(3) Za su yi bayani cewa mun zo wannan rumfa ne wadda ke WARD KAZA, MAI LAMBA KAZA domin isar da sakon Maigirma Gwamna, Mal. Dikko Ummaru Radda, wanda ya kawo buhu 60 (shiyyar Funtua), ko hamsin (shiyyar Katsina), ko 45 (shiyyar Daura) a sayar ma ku kowa e buhu akan N25,000.
(4) Nan take za su nemi sunayen manoman da za su amfana da takin, sannan a kira su, domin biyan kudi.
(5) Kowace rumfa za ku yi bidiyon jawabin da ke a lamba ta ta ukku, sannan za su turo jawabin ta wastapp ga 07067179541. Sannan za ku sanya bidiyoyin da ba su wuce minti 3 ba guda daya dalga kowace rumfa. Wato Idan kuna da rumfa 35 za ku tura bidiyon minti 3 sau talatin ga waccan lambar.
(6) Kowane Ward za a kawo ma shi takinshi har Ward.
(7) Hakimi (Idan Hakimin a wannan Ward din yake), Maigari, Limamin Jumaa na Izala, Limamin Jumaa na Dariqa, amma idan suna noma, Kansila. Kowane za a sayar ma shi da buhu goma daga cikin takin da aka ware domin manyan manoma. Kenan mutane 4 ko kuma biyar za su kasance cikin wadanda za su amfana (kai-tsaye ba tare da alumma sun za6o su ba) da takin manyan manoma akowane ward. Sauran da ba su cikin ajin mutanen da na zayyano cikin wannan lamba ta biyar, dole ne sai in alummah ta zaɓo su.
(8) Wajibi ne babban manomi ya zamo manomin gaskiya, karanci babban manomi ya kasance yana noma hekta biyar.
(9) Duk wanda ya gaza biyan kudi to a sanar da CDP cewa za a canza suna domin wane da kuma wane sun gaza biya. CDP ce za ta bayar da izinin canza manomi.
(10) Kowace rumfa a lika sunayen wadanda aka dauka domin sayar ma su da takin. Hakan zai baiwa alummar damar tantance sahihancin sunayen.