12/09/2026
SIYASAR KUƊI: HANYA CE TA BAUTAR DA AL’UMMA
Fitowa ta ɗaya:
A ilimin siyasa da tattalin arziƙi, ci gaban al’umma ba ya ginuwa kan rabawa mutane kuɗi domin su bayar da ƙuri’a. Ci gaba yana samuwa ne ta hanyar manufofi, tsare-tsare, ilimi, lafiya, aikin yi, ababen more rayuwa da samar da damar dogaro da kai.
Idan ɗan siyasa ya maye gurbin gabatar da manufa da tsare-tsaren ci gaba da rabawa mutane kuɗi, to yana iya zama wata hanya ta ƙarfafa dogaro da kai da kuma bautar da al’umma. Domin idan an kashe kuɗi domin samun mulki, akwai haɗarin a ɗauki mulkin a matsayin jari da dole a dawo da shi tare da riba.
A wannan yanayin, al’umma na iya zama kamar sanuwar tatsa; a tara dukiyar jama’a domin a mayar da jarin siyasar da aka kashe, tare da neman riba.
Misali, a Katsina, me ya sa ba za a fi tattauna yadda za a kammala manyan ayyukan da s**a shafi rayuwar jama’a ba? A shekarar 2024, an bayyana cewa akwai sama da ayyukan tarayya 74 da s**a tsaya ko aka yi watsi da su a jihar, ciki har da Kano–Katsina Road, faɗaɗa filin jirgin Umaru Musa Yar’Adua da Katsina–Daura–Maradi Rail Project.
Haka nan, Funtua Inland/Container Freight Depot na daga cikin ayyukan da binciken ilimi ya nuna cewa an taɓa gabatar da su amma aka yi watsi da su.
Saboda haka, ya kamata mu daina tambayar ɗan siyasa: “Me za ka ba ni?” Mu fara tambayarsa: “Wace manufa kake da ita? Wane tsari kake da shi? Kuma me za ka yi wa al’umma?”
Siyasa ta gari ita ce wadda ke cewa: “Ga abin da zan yi wa al’umma,” ba “Ga abin da zan ba ka domin ka zaɓe ni” ba.
Mu waye. Mu nemi manufa, tsari da sakamako—ba kuɗin zaɓe kawai ba.
✍️ Suleiman Dahiru Kerau