Karofi Youth Development Association

Karofi Youth Development Association Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Karofi Youth Development Association, Community Organization, Nigeria, katsina, Dutsinma, Karofi.

28/04/2026

Idan ba Eng.. Nalado ba, gaskiya akwai ungulu da kan zabo zamu yi
Noted..

18/04/2026

Zabin gabas, domin ci gaba da taimaka wa jama'a kamar yadda ya saba, siyasa sai dan siyasa, ya dade yana yi wa APC bauta a iya sanina tun yana secondary School a lokacin ana APP, ana kiransa da suna yan dagwai-dagwain APP.

Tabbas ya cancanci wannan damar a wannan jama'iyya mai albarka, sir mai girma Dikko a duba lamarin wannan bawan Allah

29/03/2026
21/03/2026

2027 election karofi first

30/03/2024

Al'ummar wannan gari mai albarka barkanku da shan ruwa RAMADAN DAY 20
Fatan Allah karo albarka a garemu da duk musulmai baki daya

A yau 9/12/2023 cikin hukuncin Allah aka nada Usman Shehu Shagari a matsayin Gazobi watau Dagancin garin karofi Muna fat...
09/12/2023

A yau 9/12/2023 cikin hukuncin Allah aka nada Usman Shehu Shagari a matsayin Gazobi watau Dagancin garin karofi Muna fatan Allah taya riko ya kuma ba da ikon sauke nauyin da ya rataya a kanka.

Bayan haka Usman Shehu Usman shi ne Dagaci na goma sha biyar 15 a wannan garin karofi jahar katsina muna kara dada rokon Allah ya bada ikon sauke nauyin da ya rataya a kanka.

Sakon KYDA.

18/09/2023

WANNAN LABARIN YA BURGE NI

Wani babban mutum da matarsa sun je gidan zoo.

Sai s**a ci karo da wani biri yana wasa da biranya(macen biri) cikin nishaɗi da soyayya. Sai matar nan ta kalli mijin ta ce, "Kai! Kalli wani biri wanda ya iya soyayya."

Mijin dai bai ce komai ba sai ya girgiza kai.

Sai s**a yi gaba wajen wani zaki da zakanya. Zakin ya yi zamansa a gefe guda kamar bai san da zaman zakanyar ba, ya kau da kai ko kula ta ba ya yi. Sai matar nan ta ce, "Wannan wacce irin rayuwa ce ba soyayya!"

A nan ne sai mijin ya dube ta ya ce, "Ɗauki dutsen nan ki jefa wa zakanyar can ki ga abin da zai faru."
Jefawarta ke da wuya, sai zakin nan ya tashi tsaye ya yi ƙaraji ya yo ɓangaren da ta yi jifan – da niyyar ya ba wa matarsa kariya.

Sai mijin ya ƙara neman ta jefa wa biriyar/biranyar nan da s**a ɗan wuce. Da ta cefa kawai sai birin nan, cikin ƙiftawar ido, ya yi tsalle ya hau wata bishiya ya bar matar a wajen – domin ceton kansa.

Sai mijin ya ce, "Kar a yaudare ki a kan abin da kika gani a zahiri a matsayin soyayya. A lokuta da dama, wasu s**an bayyana soyayyar da ba ita ba ce a zuciyarsu.

Amma akwai wasu waɗanda ba sa iya bayyana soyyayarsu a zahiri amma zuciyarsu a cike take da ƙauna, tausayi da jinƙai.

Saboda haka, a yanzu akwai mutane da dama a rigar birin can, wasu kuma a rigar zakin!

Shin hakane?

18/09/2023

Ya Allah ka jaddada rahamarka ga rigayayye uban garin nan (Aliyu Gazobi).
Muna kira ga al'ummar wannan gari da mu ci gaba da addu'a Allah za6a mana mafi alkhairi

08/09/2023

Albarkacin wannan rana mai albarka Allah shafe mana zunubanmu don haka mu kara saka garinmu a cikin addu'o'inmu na yau juma'a bisa kara neman kariyar ubangiji.

08/09/2023

Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un

Allah ya yi da Sheikh Abubakar Giro Argungu rasuwa

Allah ya gafarta masa

Address

Nigeria, Katsina, Dutsinma
Karofi

Telephone

+2348039146336

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Karofi Youth Development Association posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share