Khalil Media Team Gwale Local Government

Khalil Media Team Gwale Local Government Ibrahim Khalil and the Gwale community at large.

Khalil Media Team Gwale Local Government is a community-focused media and communication platform promoting the vision, activities, and achievements of ADC, Malam.

ZIYARAR SHUGABANCIN JAMI’AR KHAIRUN GA MALAM IBRAHIM KHALILAlhamdulillah! A yau, 5/10/2026, Shugabancin Jami’ar KHAIRUN,...
05/10/2026

ZIYARAR SHUGABANCIN JAMI’AR KHAIRUN GA MALAM IBRAHIM KHALIL

Alhamdulillah! A yau, 5/10/2026, Shugabancin Jami’ar KHAIRUN, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jami’ar, Prof. A. A. Rashid, sun kai ziyara ga Malam Ibrahim Khalil, tare da taya shi murnar samun digirin digirgir (PhD) daga Jami’ar Instiqama da ke garin Sumaila.

Malam Ibrahim Khalil ya nuna matuƙar farin ciki da godiya bisa wannan kyakkyawar ziyara da girmamawa da shugabancin Jami’ar KHAIRUN s**a nuna masa.

Muna miƙa godiya ta musamman ga Shugaban Jami’ar da daukacin shugabancin KHAIRUN bisa wannan ziyara.

Allah Ya ƙara ɗaukaka Jami’ar KHAIRUN, Ya kuma ƙarawa Malam Ibrahim Khalil ilimi, hikima da nasara. Allah Ya sanya wannan mataki na ilimi ya zama alheri ga al’umma.

Khalil Media Team Gwale Local Government

MAGANA TA QARE. 2027  🇳🇬 🤝 💚ATIKU ABUBAKAR — Ɗan takarar Shugaban ƘasaMALLAM IBRAHIM KHALIL — Ɗan takarar Gwamnan Jihar ...
02/10/2026

MAGANA TA QARE. 2027 🇳🇬 🤝 💚

ATIKU ABUBAKAR — Ɗan takarar Shugaban Ƙasa
MALLAM IBRAHIM KHALIL — Ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano
ADC — African Democratic Congress

Makomar Najeriya da Kano na ci gaba da zama muhimmin batu yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Mu cigaba da sanarwa mutane, manufofi da abubuwan da zasu gabatar na alheri idan Allah ya bamu nasara kafa mulki.

Khalil Media Team Gwale Local Government

KO DA NAKA, KA SO NA ƘWARAI! ❤️💚Lokaci ya yi da za mu tsaya tare da Mallam Ibrahim Khalil, ɗan takarar gwamna a ƙarƙashi...
02/10/2026

KO DA NAKA, KA SO NA ƘWARAI! ❤️💚

Lokaci ya yi da za mu tsaya tare da Mallam Ibrahim Khalil, ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Mu tallafa masa, mu yaɗa saƙonsa, mu sanar da jama’a manufofinsa, kuma mu ba shi cikakken goyon baya a wannan tafiya.

Malam Ibrahim Khalil — Tare Zamuyi Nasara!

Khalil Media Team Gwale Local Government

28/09/2026

🎵 GA KARIMIN SARKI — GA KARIMIN GWAMNA! 👑🏛️

Idan aka samu darajar masarauta da kyakkyawan jagoranci a wuri guda, Kano ta samu abin alfahari. ❤️💚
Mai Martaba Aminu Ado Bayero 🤝 Malam Ibrahim Khalil — haɗin kai, mutunci da fatan zaman lafiya ga Kano.

🎶 Ga Karimin Sarki, Ga Karimin Gwamna! 🎶

27/09/2026

Kano na bukatar sabon jagoranci, Najeriya na bukatar sabon alkibla! 🇳🇬
Malam Ibrahim Khalil — Gwamnan Kano.
Atiku Abubakar — Shugaban Najeriya.

Lokaci ya yi na haɗin kai, sabon fata da aiki domin jama’a. 💚

Kano sai Malam Ibrahim Khalil!
Najeriya sai Atiku!
ADC — Alheri-Alheri!

Alhamdulillahi,Halastaccen Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano Na Jam'iyyar ADC Kano
27/09/2026

Alhamdulillahi,
Halastaccen Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano Na Jam'iyyar ADC Kano

Shugaban Jam’iyyar ADC na Jihar Kano, Musa Shu’aibu Ungogo, ya gudanar da wata ganawa ta musamman da tsohon Mataimakin S...
24/09/2026

Shugaban Jam’iyyar ADC na Jihar Kano, Musa Shu’aibu Ungogo, ya gudanar da wata ganawa ta musamman da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar.

A yayin ganawar, an ƙara jaddada matsayin Musa Shu’aibu Ungogo a matsayin Shugaban Jam’iyyar ADC na Jihar Kano, tare da tattauna wasu muhimman batutuwa da s**a shafi tafiyar jam’iyyar.

Kwanannan, za ku ga abubuwa sun ƙara komawa kan hanya daidai, yayin da ake ci gaba da daidaita harkokin jam’iyyar a Kano.

Shugaban ADC a Kano: Musa Shu’aibu Ungogo.
Ɗan takarar Gwamna a Kano: Malam.

22/09/2026

Ya Allah Sa Dukka Su Fadi
🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏 🙏

﴿لَا تَدْرِي لَعَلَّ اللَّهَ يُحْدِثُ بَعْدَ ذَٰلِكَ أَمْرًا﴾“Ba ka sani ba, watakila Allah Ya kawo wani sabon al’amari ...
19/09/2026

﴿لَا تَدْرِي لَعَلَّ اللَّهَ يُحْدِثُ بَعْدَ ذَٰلِكَ أَمْرًا﴾

“Ba ka sani ba, watakila Allah Ya kawo wani sabon al’amari bayan haka.” — Suratul Talaq: 1

Wannan hoto ba hoto ba ne kawai; yana dauke da fata, addu’a da buri na ganin sabon babi a tarihin Kano.

Yau muna ganin Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, tare da Dr. Malam Ibrahim Khalil (Gwamnan Gobe In Sha Allah). Allah ne kadai Ya san abin da gobe za ta zo da shi.

Muna fatan alheri, muna addu’ar Allah Ya zabi abin da ya fi alheri ga Kano da al’ummarta.

Allah Ya kawo mana alheri, Ya shiryar da shugabanni, Ya zaunar da zaman lafiya a Kano. 🤲

Allah Ya Taya RiqoAllah Idda Nufin Alheri Gwamnan Gobe Da Yardar Allah
19/09/2026

Allah Ya Taya Riqo
Allah Idda Nufin Alheri
Gwamnan Gobe Da Yardar Allah

Address

Northwest Kabuga
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Khalil Media Team Gwale Local Government posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share