26/10/2025
Ni da mijina kullum cikin faɗa muke saboda bai cika kawo abubuwan da nake buƙata ba.
In na buƙaci wani abu, ba ya kawowa.
Yana cewa kuɗinsa bai isa ba – amma ni bana yarda da shi. Sai in yi ta gardama da shi, in bar ayyukan gida cikin datt,ba shara ba wanke wanke.
Na kan kulle kaina a ɗaki, in bar shi yana gyaran gida shi kaɗai – ko da ya dawo daga wajan aiki ciki gajiya.
Abin mamaki, ba ya faɗa ko daga murya, kuma wannan ya ƙara sa ni in taƙura masa.
Yayinda zai zo ya sasanta dani – ko da ni ce na yi laifi – sai in gudu, in bar shi shi kadai, in shiga ɗaki, in bar shi yana kwana a ƙasa waje.
Ko da dafa abinci bana masa, inayi da gangan in ƙi kula da shi.
Duk da haka, ni ce kullum cikin baƙin ciki da rashin nutsuwa.
Wata rana na je gidan iyayena.
A can na same babban ɗan uwana da ya dawo daga ƙasashen waje bayan dogon lokaci.
Mun zauna muna hira, ya tambaye ni game da rayuwata da mijina.
Na ce masa mijina baya cika buƙatuna, baya kula dani.
Sai ya ce:
“Koma gida gobe zan zo, mu tattauna da ke.”
Na koma gida. Washegari ya zo.
Na tarbe shi cikin mutunci, na ba shi abin sha.
Ya kalle ni yace:
"Kin san mijinki me yake yi?"
Na ce masa:
“Yana aiki a wani kamfani mai girma, amma duk da haka bana jin daɗi kamar sauran matan aure.”
Sai yace:
“Amma me yake yi a can?”
Na ce masa:
“Ban sani ba.”
Sai ya ɗauko wayarsa, ya kunna wani bidiyo.
Na karɓa na fara kallo...
Gaba ɗaya jikina yayi sanyi, zuciyata ta kusa fashewa – na ga mijina yana can a saman gini mai tsayi sosai, yana riƙe da abin gogewar gilashi yana goge manyan tagogi irin na dogayen gidajen nan.
Na ce:
“Wannan mijina ne? Me yake yi haka? Idan ya faɗo fa? Wannan aiki akwai haɗari!”
Sai ɗan uwana yace:
“Mijinki yana sadaukar da rayuwarsa ne – saboda ke. Yana cikin haɗari kullum domin samun abincin d zakuci. Ina fatan kin gane darasi.”
Na Tuba...
Bayan ya tafi, na zauna ina kuka da zafin rai.
Na share ƙwalla ina gyara gidan, zuciyata cike da nadama.
Da mijina ya dawo, na yi sauri na buɗe masa ƙofa, na roƙe shi d