02/08/2026
Mabiya addinin Kirista na jami'ar tarayya dake Gashua Sun nemi hukumomin makarantar da su Gina musu wurin Ibada na Dindindin
A yayin ziyarar, wakilan al'ummar Kiristocin sun roƙi mahukuntan jami'ar da su samar musu da ingantacciyar cibiyar ibada ta dindindin. Sun bayyana cewa tun bayan kafa Jami'ar Tarayya ta Gashua, mabiya addinin Kirista suna gudanar da ibadunsu ne a cikin ajujuwa, dakunan karatu da sauran wurare na wucin gadi, lamarin da s**a ce ya kamata a kawo masa ƙarshen ta hanyar samar musu da wurin ibada na dindindin.
Da yake jawabi a madadin al'ummar Kiristocin, Farfesa James Ishaku Dantata ya bayyana cewa naɗin Farfesa Geidam wata ni'ima ce daga Allah, yana mai bayyana fatan cewa shugabancinsa zai kawo sabon zamani na zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa a jami'ar.
Haka kuma, shugaban tawagar, Rabaran Farfesa Johnson Sunday Alao, ya tabbatar wa Mataimakin Shugaban Jami'ar da ci gaba da yi masa addu'a, biyayya da kuma haɗin gwiwa wajen bunƙasa darajojin ilimi, tarbiyya da zamantakewa a jami'ar.
A nasa jawabin, Farfesa Yaqub Ahmed Geidam ya gode wa al'ummar Kiristocin bisa ziyarar, addu'o'insu da kuma goyon bayan da suke bai wa jami'ar. Ya ce ziyarar ta nuna irin haɗin kai, mutunta juna da zaman lafiya da s**a zama ginshiƙan rayuwar jami'ar.
Ya kuma sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta gudanar da shugabanci na adalci da bai wa kowa dama ba tare da la'akari da bambancin addini ko ƙabila ba.
Dangane da buƙatar samar da cibiyar ibada ta dindindin, Mataimakin Shugaban Jami'ar ya tabbatar da cewa mahukuntan jami'ar za su ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da bi hanyoyin gudanarwa da s**a dace domin duba yiwuwar magance wannan buƙata cikin maslahar jami'ar.
Haka kuma, ya buƙaci al'ummar Kiristocin su mara wa shirin kare muhalli na jami'ar mai suna FUGA Green Code (FGC)baya ta hanyar dasa itatuwa, kula da tsaftar muhalli da kuma amfani da albarkatun ƙasa cikin hikima.