15/02/2026
ℹ BABU MACEN DA TAKE DA WAHALAR SAMU... ITA CE KAWAI BATA RA'AYINKA.
Dan uwa,
Ka daina yaudarar kanka kana cewa: Tana jan aji ne ko Tana so na amma tana nuna min halin mata ne.
Wallahi Karya Ne.
Dokar Soyayya tana da sauki:
Mace da take Sonka, za ta karya kowace Doka don ta kasance tare da kai inda bai sabawa Addini ba.
Ga gaskiyar da zata cece ka daga Heartbreak da Zubar da Kudi:
1. IDAN TANA SONKA, KOFAR A BUDE TAKE:
Macen da take sonka, ba ta Busy.
Ko tana taro ne da Shugaban Kasa, idan ka kira ta, za ta dauka ko ta tura maka "I will call you back" nan take.
Amma idan kullum "Ina wajen aiki", "Wayata ta mutu", "Ban gani ba"...
Abokina, Signal ce ta ce ka k**a gabanka.
Bata Hard to get, kawai dai Bata so ne.
2. KADA KA YI ROKO SOYAYYA:
Babban kuskuren Namiji shine Rokon Soyayya.
Soyayya ba sadaka bace.
Idan ka ga kana yawan kiran ta bata dauka, kana tura Text bata replying, kana kashe kudi bata godiya...
JA JIKINKA.
Duk lokacin da ka nuna mata ka fi son ta fiye da kanka, a lokacin ne darajarka take faduwa a idonta.
3. KA GINA DARAJARKA, ITA ZA TA NEME KA:
Maimakon ka bi t**i kana Hello Baby, Hi Beauty...
Je ka nemi Kudi.
Je ka gina Sana'a.
Je ka gyara Jikinka da Tufafinka.
Namiji mai Manufa k**ar Magnet yake.
Ranar da ka yi nasara, wadanda s**a ki ka jiya, sune za su fara yi maka Comment da Masha Allah yau.
A tsari na 👇
Neman Mata aikin Yara ne.
Neman Nasara aikin Maza ne.
Idan ka bi Mata, za ka rasa Kudi.
Amma idan ka bi Kudi da Nasara, Mata za su bi ka har gida.