Hussaini Sani Angale

Hussaini  Sani Angale public service

11/06/2025

SARAKUNAN DA AKA FI TSANA A TARIHIN KANO.

1. Sarki Yusufu (Yusuf) – 1390s
Yusufu ya ci gadon mulki ne bayan da ya kash€ ‘yan uwan sa domin kar su hana shi zama sarki. Wannan k!san da kuma yadda ya sami mulki ya janyo masa ƙ!yayya daga wasu bangarorin. Duk da kasancewar sa mai tsauri da karfi, mutanen sa ba su gamsu da salon mulkin sa ba.

2. Sarki El Kutumbi (1623–1648)
Ya kasance sarki mai karfi, amma an zarge shi da zaluntar jama’a da kuma yin mulki mai tsanani. Ya sha yaki da makwabtan Kano da kuma cikin gida. Yawan fada da rashin kwanciyar hankali a lokacin mulkin sa ya janyo ma sa rashin farin jini.

3. Sarki Aliyu Babba (1894–1903)
An ce ya nuna rashin adalci da karfi wajen mulki, musamman a lokacin da turawa s**a fara samun karfi a Arewacin Najeriya. A zamanin sa ne aka kawo karshen cikakken ikon sarakunan Kano lokacin da Birtaniya ta kwace iko da yankin. Yayin da wasu ke ganin ya yi iya bakin ƙoƙarin sa, wasu kuma na kallon sa a matsayin wanda bai kare masarauta ba.

4. Sarki Sanusi I (1953–1963)
Sarki Sanusi I ya kasance mutum mai ilimi da hangen nesa, an tsane shi daga wasu manyan mutanen Arewa saboda irin gyare-gyaren da yake son kawo wa a harkokin masarauta da addini. Rikicin sa da Premier na Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello, ya kai ga tsige shi daga sarauta a shekarar 1963.

5. Sarki Muhammadu Sanusi II (2014–2020)
Wasu sun tsane shi saboda tsauraran ra’ayoyin sa game da gyara tsarin masarautu, tsoma baki kan sha'anin siyasa da matsalolin tattalin arziki inda ya bada shawarar a cire tallafin mai, a rufe Boda, a karya darajar naira da kuma rikicin sa da gwamnati. An tsige shi daga sarauta a shekarar 2020, abin da ya jawo muhawara da rarrabuwa a tsakanin al'ummar Kano.

10/06/2025
10/06/2025

🚨 If Arsenal complete the signing of Benjamin Sesko, and land Rodrygo too, we’re looking at the birth of one of the most dangerous attacking trios in Europe. 🔥

Šeško x Saka x Rodrygo = speed, power, flair, and ruthless end product. 💣

🔸️ Benjamin Šeško – Arsenal’s answer to Erling Haaland.
At 6'5", he's a physical monster with elite movement, devastating pace in transition, and the killer instinct of a true No.9. Tap him in and he’ll break lines or finish first time pure striker’s mentality.

🔸️Bukayo Saka [Starboy] – The creative engine.
Carries the ball like few others. Creates space, finds gaps, and delivers ice-cold final balls. Šeško will feast off his service and Saka’s gravity frees space for the others.

🔸️ Rodrygo – Direct, unpredictable, and lethal in tight spaces.
He thrives cutting in from the left or floating between lines. With Saka wide right and Šeško pinning defenders, Rodrygo becomes the free man — like a turbocharged second striker.

⚙️ Arteta could build a fluid front three that blends the physicality of Haaland, the dynamism of peak Liverpool, and the flair of Madrid.

🔴 This is not just a rebuild it’s an evolution. Arsenal’s front line could soon be world-class on all fronts.

Thoughts guys ❓🤔

06/06/2025
31/05/2025

YANDA YA DACE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA (10) NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH

Fitowa ta: 1

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da aminci su kara tabbata ga Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, Alayensa da Sahabbansa da dukkan wanda ya biyo bayan su da kyautatawa.

Bayan haka, duba da yanda kwanaki goma na farkon watan Dhul-Hijja suke da matukar muhimmanci, amma mafi yawa daga cikin mutane sun rafkana ga barin cin gajiyan su, ya sanya na ga dacewar in yi tsokaci a takaice dangane da wadannan kwanaki.

Dukkan abun da aka samu na daidai a cikin wannan Rubutu nawa daga Allah ne, abun da kuma aka samu na kuskure daga gare ni ne da Shaidan, Allah Ta'ala da ManzonSa sun barranta daga gare shi.

Da me ya kamata Musulmi ya fuskanci wannan wata da shi?.

1. *TUBA ZUWA GA ALLAH* saboda zunubi shi ne kofa mafi girma da yake sanya Allah Ta'ala Ya azabtar da bawa.

Allah Ta'ala Ya yana cewa: "Kuma wata musiba da take samun ku face sai sakamakon abun da hannuwanku s**a sana'anta". Suratu al-Shuura aya ta 30.

Babban dalilin da zai sa mu fara wannan wata da tuba shi ne, barna da tasirin da zunubai suke yi a rayuwar mutum. Daga ciki:

*Na farko:* Zunubai suna haramta ma mutum samun ilimi mai amfani. Domin shi ilimi haske ne da Allah Ta'ala Yake sanyawa a zuciyar mai shi, kuma zunubai suna kawar da wannan hasken.

*Na biyu:* Zunubai suna sanya talauci su hana bawa samun arziki.

Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: Lallai ana haramta bawa arziki saboda wani zunubi da ya aikata. Imamu Ahmad ya riwaito a cikin al-Musnad 5/282.

*Na uku:* Duhu da da mutum zai rinka ji a zucirya shi.

Abdullahi Bn Abbas, Radhiyallahu Anhu, ya ce: "Lallai kyawawan ayyuka suna sanya ma mutum hasken fuska da hasken zuci da yalwan arziki da karfin jiki da soyayya daga bayin Allah, kamar yadda sabon Allah yake fuska zuciya ya yi duhu da duhun zuciya da raunin jiki da tawayan arziki da kiyayya daga mutane".

*Na hudu:* Zunubai suna sanya daraja da mutuncin mutum ya zube a wurin Allah.

Allah Ta'ala Ya na cewa: "Dukkan wanda Allah Ya wulakantar, to ba shi da wani mai girmamawa. Suratul Hajji aya ta 18

*Na biyar:* Idan mutum yana aikata zunubai zai wayi gari baya ganin girman zunuban, wannan kuma alama ce ta tabewa da halaka.

*Na shida:* Idan mutum yana aikata zunubai za a wayi gari sun lullube zuciyar shi har ta yi tsatsa ta koma bata iya daukan wa'azi da shiriya.

2. *NEMAN TAIMAKON ALLAH A WADANNAN KWANAKI:* Wadannan kwanaki ya dace dukkan musulmi ya dage wurin neman taimakon Allah domin ganin ya ribace su yanda ya kamata.

Allah Ta'ala Ya na cewa: "Kuma wadanda s**a yi kokari ga neman yardanMu, lallai Muna shiryar da su ga hanyoyinMu, kuma lallai Allah Tabbas Yana tare da masu kyautatawa". Suratul 'Ankabut aya ta 69.

*ME YA SA AKA FIFITA YINNAI GOMA NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH AKAN WASUNSU???*

Mu hadu a fitowa ta 2 in sha Allahu Ta'ala

Dan uwanku a Musulunci: ✍
Sheikh Umar Shehu Zaria{Hafizahullah}.
15/08/2017.

Address

K/Dala
Kano
700251

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hussaini Sani Angale posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share