YALWA Development FORUM YDF

YALWA Development FORUM YDF Gamayyar kungiyoyin sa kai na Yalwa dake aiki a dunkule domin kawo cigaba da zaman lafiya mai dorewa

09/02/2026

Jawabin Malam Lawan yayin yaye daliban .

KWARYA KWARYAR BIKIN YAYE DALIBAI A yau Lahadi 8 ga watan February makarantar koyon sana'o'i dake Yalwa Model vocational...
08/02/2026

KWARYA KWARYAR BIKIN YAYE DALIBAI

A yau Lahadi 8 ga watan February makarantar koyon sana'o'i dake Yalwa Model vocational center tayi bikin yaye dalibai wadanda s**a samu horo na musamman na koyon sana'o'i tun bayan dawowar center aiki .

Wadannan dalibai sun koyi sana'o'i da s**a hada da :

Dinki na mata
Leather works ( Hada takalmi da jaka )
Aikin stone na mayafai
Da general courses.

Taron ya samu halartar masu unguwannin Yalwa da Gorondutse da kansilan Yalwa a inda Hon. Councilor ya bada gudunmawar naira dubu hamsin ( N50 000 ).

Muna adduar Allah ya kara shiga lamarin wannan unguwa dama Dala baki daya ya kara karfafar kwamati na Yalwa Development forum .

Ziyara ta musamman da gamayyar kungiyoyin Yalwa s**a kai gidan radion Kanawa domin tattaunawa akan nasarori da kuma kalu...
17/12/2025

Ziyara ta musamman da gamayyar kungiyoyin Yalwa s**a kai gidan radion Kanawa domin tattaunawa akan nasarori da kuma kalubale da wannan kungiya ta hadu dashi tare da wayar kan al'umma akan muhimmancin kungiyoyi wajen kawo cigaba... Muna adduar Allah ya kara shige mana gaba ya daukaka Yalwa da Dala dama Kano baki daya.

A jiya Asabar 8 ga November kwamatin kula da makarantar koyon sana'o'i ta Yalwa model vocational center hadin gwiwa da h...
09/11/2025

A jiya Asabar 8 ga November kwamatin kula da makarantar koyon sana'o'i ta Yalwa model vocational center hadin gwiwa da headmaster s**a gabatar da kwarya kwaryar taron Orientation ga sabbin dalibai da zasu koyi sana'a domin dogaro da kai.
Taron ya samu halartar kansilan Yalwa kuma jagoran gamayyar kungiyoyin Yalwa development forum Hon. Sadeeq Khamis. Muna adduar Allah yasa a fara asa'a ya kuma kara daukaka yankinmu ya kara mana zaman lafiya mai dorewa.

.
9 November 2025.

10/10/2025

SANARWA TA MUSAMMAN

YALWA MODEL VOCATIONAL CENTER

A madadin kwamatin gudarnawa na Yalwa model vocational center na sanar da al'umma (musamman mata) cewa zasu fara bada form na diban dalibai a fannonin koyon sana'o'i domin dogaro da kai a Gobe Asabar 11 ga watan October acikin harabar makarantar dake cikin Yalwa model primary. daga karfe 10 na safe zuwa 1.

13/09/2025

YALWA DEVELOPMENT FORUM ( Y.D.F.)

Wannan gamayya ce ta kungiyoyin sa kai na Yalwa hadin guiwa da duk wani mai fada aji na yankin domin kawo cigaba.

Wannan gamayya ba ta siyasa bace. An samar da ita ne don neman hadin kai babu nuna banbancin raayin siyasa domin Yalwa ce agaba.
Mun samu damar gabatar da ayyuka daban-daban na cigaban yankin musamman a harkar ilimi da rayuwa ta yau da kullum.
Muna rokon Allah ya daukaka Yalwa ya bamu ikon kare duk wani hakki na al'ummar yankin aduk inda yake.

KADDAMAR DA DASHEN BISHIYOYI  Awannan rana ta Asabar 30 ga Agusta kungiyar DA RUWA NA wacce aka fi sani da KANO LEADS ta...
30/08/2025

KADDAMAR DA DASHEN BISHIYOYI

Awannan rana ta Asabar 30 ga Agusta kungiyar DA RUWA NA wacce aka fi sani da KANO LEADS ta kaddamar da dashen bishiyoyi a karamar hukumar Dala cikin mazabar Yalwa a makarantar Anwaru special primary school tare da hadin gwiwar gamayyar kungiyoyin Yalwa (YALWA DEVELOPMENT FORUM ).

Taron ya samu halartar manyan baki daga sassa wadanda s**a hada da Dr. Atika Bala mai yafe Shugabar kungiyar Kano leads ta karamar hukumar Dala da Bala Magawata E.S. na ilimi na Dala da Alh. Alkassim trader shugaban kungiyar Fitilar Dala da tsohon dan majlisar jiha na Dala Hon. Nura Lawan da Hon. Sadiq Khamis kansilan Yalwa tare da sauran iyayen unguwa da wakilcin kungiyoyi.

Muna fatan Allah yasa wadannan bishiyoyi su zama silar alkhairi ga alumma baki daya tare da kawo gudunmawa wajen canjin dumamar yanayi da ake fama dashi . Da fatan Allah yasakawa kowa da alkhairi ya kara daukaka Yalwa da Dala dama Kano baki daya .


30 - 08 - 2025

PUBLIC ANNOUNCEMENT, PLEASE SHARE AND REPOST.JOIN THE NIGERIAN AIR FORCE – DSSC 34/2025 ENLISTMENT OPENS ON 27TH AUGUST ...
26/08/2025

PUBLIC ANNOUNCEMENT, PLEASE SHARE AND REPOST.

JOIN THE NIGERIAN AIR FORCE – DSSC 34/2025 ENLISTMENT OPENS ON 27TH AUGUST 2025.

Are you a graduate seeking an opportunity to serve your nation with pride and professionalism? The Nigerian Air Force is inviting applications into the Direct Short Service Course (DSSC) 34/2025 across various professions. Application is FREE and available online from 27 August – 7 October 2025. Apply now at: www.nafrecruitment.airforce.mil.ng

Take the next bold step in your career, soar with the Nigerian Air Force.

TARON ADDUA  A yau ne dalibai tare da management na makarantar koyon sana'o'i dake Yalwa model s**a gabatar da saukar ka...
24/08/2025

TARON ADDUA

A yau ne dalibai tare da management na makarantar koyon sana'o'i dake Yalwa model s**a gabatar da saukar karatun alkur'ani mai girma tare da addu'o'in Allah yacigaba da shiga lamuran masu taimakawa awajen tare da fatan zaman lafiya mai dorewa a fadin Yalwa da kewaye.

Muna adduar Allah ya amsa ya biya bukatu .

12/08/2025

Manzon Allah SAW yace "Mafi alkhairin cikinku wanda yafi amfanar da al'umma "

25/07/2025

Barka da Juma'a da fatan Allah ya karbi kyawawan ayyukanmu ya yafe mana munana albarkar wannan rana.

SHIRIN FARFADO DA KUNGIYOYIN CIGABAN ALUMMA DAKE  YALWA  Ayau Lahadi 20 ga watan July 2025 wakilcin gamayyar kungiyoyin ...
20/07/2025

SHIRIN FARFADO DA KUNGIYOYIN CIGABAN ALUMMA DAKE YALWA

Ayau Lahadi 20 ga watan July 2025 wakilcin gamayyar kungiyoyin Yalwa s**a gudanar da meeting na musamman domin tattaunawa akan sabbin shirye-shiryen da zasu kawo cigaba a Yalwa da kewaye karkashin jagorancin mai unguwar Yalwa .

A zaman na yau gamayyar kungiyoyi sunyi duba akan waiwayar yan kishi domin samun hadin kai don cigaban unguwa baki daya da kuma dafawa wajen samun cigaba a abubuwan da takeyi tare da dawo da programs da aka fara abaya da s**a shafi bangarori da dama na cigaban yanki wadanda s**a shafi harkar lafiya da ilimi da tsaro da walwalar alumma. Muna adduar Allah ya cigaba da taimakon Yalwa development forum tare da daukaka Yalwa da Dala baki daya. Allah yasa Yalwa sai ta zama zakaran gwajin dafi a fadin jihar Kano wajen samun cigaban alumma da kwanciyar hankali mai dorewa.

Address

Yalwa Dala Local Government
Kano

Telephone

+2347068956659

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when YALWA Development FORUM YDF posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share