26/01/2023
SHIN KANASON RAYUWARKA DATA AL’UMMARKA TA GYARU?
SHIN KANASON SANIN WANDA ZAI KAWO KARSHEN MATSALOLIN DAMUKE FAMA DASU?
Toh, tabbas kana bukatar sanin SUFFOFIN SHUGABARI NAGARI domin ‘shugaba shi yafe mabiyansa tsawu da ince daya’
AREWACIN NIJERIYA yakasance daya daga cikin yankunan nijeriya wanda ki amfani da mulkin damokoradiyya domin jagorantar al’ummar kasar.
DEMORADIYYA tsarin mulkine da yan kasa ki zabar wasu mutane nagartattu wanda jama’a s**a yarda da dabi’unsu, halayensu, lafiyarsa, iliminsa da fikirarsa wajen jagorantarsu, kawo musu cigaba da kuma dakile matsalolin al’umma.
Saidai kash! wannan yankinamu na AREWA na fama da matsaloli da dama wanda I barazanar tarwatsa dukiyoyi, lafiya da kuma tsoro na wannan al’umma. Hakan yasamu asaline ta dalilin RASHEN SHUWAGABANI NAGARI.
Tambaya a nan itace WAYE SHUGABA NAGARI?
SHUGABA NAGARI mutum ne wanda yayarda ya bada rayuwarsa, dukiyarsa, lafiyarsa da ilminsa wajen kawowa al’umma CIGABA. Shi shugaba nagari mutum ne mai mu’amala, fikirar sarrafa harshe da zurfin tunani.