Malam Aminu Saleh Garko

Malam Aminu Saleh Garko This page is mainly use for education and knowledge sharing

16/02/2026

Assalamu alaikum Warahamatullah

*RAMADAN TAFSIR 1447AH/2026*

Masjid Imam Darul Hijrah Garko Tana Farin Cikin Sanar Da 'Yan Uwa Musulmi Cewa Za'a Cigaba da Gabatar Da Karatun Tafsirin Al-qur'ani Mai Girma Wanda Aka Saba Gabatarwa a Watan Ramadan Duk Shekara.

Ranar: 01 Ramadan,1447-AH

Alhamis 18th February, 2026

Lokaci: Bayan Sallar La'asar zuwa 5:00pm (1hrs at least)

Wuri: MASALLACIN MASJID IMAM DARUL HIJRA GARKO LUNGON FULANI

Mai Gabatarwa:

MALAM AMINU SALEH GARKO (ABU RUFAIDA)

Allah Ya Bada Ikon Halarta Amin.

Domin Samun Karatuttukan Kai Tsaye

WhatsApp:
https://chat.whatsapp.com/KSp8d9Z3om90OThJOc2oEi
Facebook:
https://www.facebook.com/profile.php?id=10009460896229

SANARWA:
Masjid Imam Darul Hijira Media Team

16/10/2025

Assalamu alaykum wa Rahmatullah wa Barakatuh

Ana gayyatar yan uwa zuwa Walimar daurin auren dan uwa Adamu Ado (malam Bala)

-Rana; Asabar
-Guri; Habib Islamiyya
-Lokaci; Bayan Sallar Magriba zuwa Isha'i
-Mai Gabatarwa; Abu Rufaida Sheikh Aminu Saleh Garko

Allah ya bada ikon halarta🤲🏽

Assalamu alaikum warahmatullah Amadadin Kwamitin Masallacin Masjid Imam Darul Hijrah Garko Lungun Fulani Suna cigaba da ...
15/10/2025

Assalamu alaikum warahmatullah

Amadadin Kwamitin Masallacin Masjid Imam Darul Hijrah Garko Lungun Fulani

Suna cigaba da Neman taimakon Solar.
Abubuwan da ake buƙata sune Kamar Haka

1. Panel 250W Guda (8)
2. Flexible wire Rimg (1)
3. DC/AC Fan guda (10)

Ga wanda Allah Ya Horewa ga details dinmu Nan

Acc No. 1407107457
Acc Name. WAKILI IBRAHIM
Bank Name. ACCESS BANK PLC.

For more information
08068365215,07085023791
08143364943

Fisabilillah
Allah Ya bada ikon Taimakawa

Inna lillahi wa Inna lillahi wa Inna lillahi raji un Allah ya yiwa (Ummi) Matar Malam Aminu Saleh Garko (Abu Rufaida) ra...
11/08/2025

Inna lillahi wa Inna lillahi wa Inna lillahi raji un

Allah ya yiwa (Ummi) Matar Malam Aminu Saleh Garko (Abu Rufaida) rasuwa yanzu ayi jana'izarta in anjima kadan Allah ya jiqanta yaimata rahama yasa aljannatul fiddausi Makoma Ameen.

03/07/2025

(FALALAR AZUMIN TASU'A DA ASHURA)

Manzon Allah ﷺ Yace : Idan Allah Ya Rayani Zuwa Shekara Mai Zuwa Zan Azumci Ranar Tara Ga Wata (Tasu'a).

Sahih Muslim (1162)

Manzon Allah ﷺ Yace : Yin Azumin Ranar (Ashura), Ina Fata A Wajen Allah Zai Kankare Zunubin Shekarar Da Ta Gabace Shi.

Sahih Muslim (1134)

Kuma A Wani Hadisin Manzon Allah ﷺ
Yace: "Allah (Ta'ala) Ya Faɗa A Cikin Hadisi Qudusiy : "Dukkan Ayukkan Ɗan Adam Nasa Ne, Face Azumi, Wannan Nawa Ne, Ni Nake Sakayya Da Shi"

Sahih Al-bukhari (1904)
Sahih Muslim (1151)

Wanda Babu shakka Azumin Ranakkun Tasu'a da Ashura suna ciki.

Hakama!

Manzon Allah ﷺ Yace: Duk Wanda Ya Yi Azumi A Wata Rana Saboda Allah,
Toh, Allah (Ta'ala) Zai Nisanta Fuskar Sa Daga Wuta Tsawon Shekara 70.

Sahih Al-bukhari (2840)
Sahih Muslim (1153)

Wanda Shima Babu Shakka Azumin Ranakkun Tasu'a da Ashura suna ciki.

TASU'A ranar 9 ga Watan MUHARRAM 1447, zai yi daidai da Ranar JUMU'A 4 ga Watan July 2025.

ASHURA ranar 10 ga Watan MUHARRAM 1447, zai yi daidai da Ranar ASSABAR 5 ga Watan July 2025.

Ƴan'uwa musulmi ina mai tunatar da mu, da mu dauki ranakun Tasu'a da Ashura da matuqar Muhimmancin.

Mu yi kokari wajen yin ibadah a wadannan ranaku masu darajja ta hanyar yin azumi da Addu'o'i da bayar da sadaka da sauran ayyukan Alkhairi.

Sa'annan Ina Kara kira ga ƴan uwa musulmi, da mu ci gaba da hada kawunanmu, kuma mu hada karfi da karfe wajen kiyaye addininmu.

Mu taru a matsayin ƴan uwa, domin kare Martaba Da kuma koyarwar addininmu.

Allah Ubangiji Ya bamu ikon Azumtar kwanakin nan na TASU'A da ASHURA Masu Albarka (Ameen).

21/06/2025

Assalamualaikum warah matullah.

Insha Allahu kamar yadda aka saba yauma akwai karatu.

Littafin: Minhaj Al muslim

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh,Alhamdulillah, we thank Allah (SWT) for granting us the opportunity to witne...
01/05/2025

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh,

Alhamdulillah, we thank Allah (SWT) for granting us the opportunity to witness and complete the blessed month of Ramadan. May Allah accept our fasting, prayers, and good deeds. Ameen.

We are pleased to inform you that our weekly *TA'ALIM* sessions will resume on *THURSDAY 08-May- 2025* at [Insert Time], In Shaa Allah. The sessions will continue to be held at our usual

As always, we aim to seek beneficial knowledge, strengthen our faith, and improve our understanding of the deen. We encourage all members to attend punctually and regularly, as the Prophet (SAW) said: “When a group of people assemble in one of the houses of Allah, reciting the Book of Allah and studying it among themselves, tranquillity descends upon them…” (Sahih Muslim).

May Allah increase us in knowledge and guide us to what pleases Him.

Jazakumullahu Khairan.

04/04/2025

Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un.

Allah kajiqan Dr. Idris Abdul'aziz Dutsen tanshi, Allah yayafe kurakurensa yasa aljannah Firdaus makoma gareshi, Allah ya kyauta namu zuwan.

Address

Garko Lungon Fulani
Kano

Telephone

+2347063473744

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Malam Aminu Saleh Garko posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Malam Aminu Saleh Garko:

Share