05/10/2025
Mahaifiyar Attajirin Dan Kasuwa Alh Aliko Dangote, Wato Mariya Sunusi Ɗantata, Kuma ƴar Wan Hamshaƙin Attajirin Wanda YaRasu Kwana Nan, Alh Aminu Alasan Ɗantata {Amin-Dogo}
Da yawa mutane ba su san wacece Mariya Sanusi Dantata ba, kawai dai suna kallon tacne a matsayin mahaifiyar shahararren Attajirin nan na Afrika Aliko Dangote.
Cikakken sunanta shine, Uwar Marayu da Marasa Gata, Domin idan zan yi maka ta babban mahaukaci zan iya rantse maka, duk fadin Afrika babu wanda ke ciyar da al'umma abinci tare da agazawa talakawa sama da ita, wallahil azim, ko Gwamnati ba za ta iya abinda wannan baiwar Allah take yi na ciyar da bayin Allah ba, saboda idan kazo gidan Mariya, sai ka tausayawa kudi, duk jihar Kano, duk Nijeriya, duk Afrika babu inda kudi suke kuka da ihu sama da gidan Mariya Sanusi Dantata, domin Mariya wani kamfani ta kafa na musamman domin ciyar da Bayin Allah tare da farantawa rayuwarsu.
Idan ka je kofar gidanta ka ga yadda ake ciyar da mutane kamar a wasan kwaikwayo, na san duk tsananin kiyayyar ka da Mariya Sanusi Dantata sai ka ce Ubangiji ya gafartawa Mariya.
Gidan Mariya ya zama wata inuwa wacce talakawa suke zuwa su huta, Mariya ta zama wata katanga wacce al'umma ke jingina da ita su sami saukin rayuwa. Abokina Sadik Abdullahi Koki
Tunda a unguwarku take ai zaka bada sheda akanta.
Malam ka zo jihar Kano kofar gidan Mariya a sannan za ka san wacece ita.
Akalla talakawa sama da dubu hamsin kullum suna cin abinci tun daga safe har zuwa dare a jikin Mariya domin da yawansu ba su da wata hanyar samun abinci sai a gidan Mariya.
Kullum ciyarwa ake yi gidan Mariya.
Abincin asibiti daban
Abincin gidan nakasassu daban.
Abincin Alumma na gari daban.
Banda wanda take rabawa mutane ba tare da an kirga ba.
Akalla Mariya tana da ma'aikan da take baiwa albashi sama da mutum dubu a karkashinta, wadanda ta ajiye saboda kawai kula da ciyar da Bayin Allah.
Daga Cikin ma'aikatanta akwai.
Masu saran itacen girki.
Masu nikan garin tuwo.
Masu dauko Itace.
Masu