20/09/2024
Labari Mara Daɗi:
Ba za ka iya gyara hauhawar farashi ba, ba za ka iya gyara tsadar rayuwa ba, ba za ka iya tursasawa shugabanni su yi abinda ya dace wanda zai sauƙaƙa ma ka rayuwa ba.
Labari Mai Daɗi:
Za ka iya bunƙasa samun ka ta gina sabuwar hanyar samun kuɗi, inganta sana'ar ka, gujewa siyan abinda bai zama dole ba. Haka kuma ka na da ikon tsayawa ka nutsu wajen zaɓen shugaba na kirki wanda zai sauƙaƙa ma ka rayuwa ba azzalumi ba.