Naibawa Connect

Naibawa Connect Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Naibawa Connect, Community Organization, Naibawa, Kano.

Ramadan Mubarak 🌙
23/02/2026

Ramadan Mubarak 🌙

04/02/2026

Alhamdulillah

KIRA GA MASU RUWA DA TSAKIMuna miƙa wannan kira cikin girmamawa ga shugabanni da hukumomin da abin ya shafa, dangane da ...
23/01/2026

KIRA GA MASU RUWA DA TSAKI

Muna miƙa wannan kira cikin girmamawa ga shugabanni da hukumomin da abin ya shafa, dangane da lalacewar hanyar Naibawa wadda ke janyo matsala ga zirga-zirgar jama’a da tsaron rayuka.

Hanyar ta zama cikin mummunan hali, musamman a lokacin damina, lamarin da ke jefa mazauna yankin cikin ƙalubale a kullum. Gyaranta zai taimaka matuƙa wajen rage haɗari, sauƙaƙa zirga-zirga, da bunƙasa rayuwar al’umma.

Muna fatan wannan kira zai samu kulawa ta musamman, a kuma ɗauki mataki cikin lokaci domin amfanin jama’a.
Allah ya ba mu shugabanni masu sauraron kiran al’umma

Kasuwar ’Yan Lemo ita ce babbar kasuwar sayar da kayan marmari a Kano, wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da kaya...
22/01/2026

Kasuwar ’Yan Lemo ita ce babbar kasuwar sayar da kayan marmari a Kano, wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da kayan fruit ga jihohi da dama. Cibiya ce ta kasuwanci da rayuwar al’umma

📍 Naibawa, Kano





Na’ibawa Flyover, Kano State Nigeria  🇳🇬📍 Naibawa, Kano
22/01/2026

Na’ibawa Flyover, Kano State Nigeria 🇳🇬

📍 Naibawa, Kano



KALLI HALIN DA HANYAR NAIBAWA TA KOMA!Wannan ba labari ba ne, gaskiya ce a fili. Hanya ta yage, ta rufta, ta zama baraza...
21/01/2026

KALLI HALIN DA HANYAR NAIBAWA TA KOMA!

Wannan ba labari ba ne, gaskiya ce a fili. Hanya ta yage, ta rufta, ta zama barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma. Yara, mata, dattijai da masu abin hawa na fuskantar haɗari a kullum. Wannan ba ruwan sama kawai ba ne ya jawo haka, rashin kulawa da gyara na dogon lokaci ne.
Muna kira ga dukkan shugabanni masu ruwa da tsaki — Gwamnati, Karamar Hukuma, da hukumomin da abin ya shafa — ku dubi Naibawa da idon tausayi. Wannan hanya na da muhimmanci sosai ga zirga-zirgar jama’a da harkokin kasuwanci, kuma lalacewarta na hana cigaban al’umma.
Gyaran hanya ba alfarma ba ne, hakki ne na jama’a.
Muna fatan a dauki mataki cikin gaggawa kafin wani mummunan lamari ya faru.
Naibawa na bukatar gyara, Naibawa na bukatar kulawa, Naibawa na bukatar adalci

NAIBAWA – UNGUWAR ZAMAN LAFIYA DA HAƊIN KAINaibawa unguwa ce da aka san ta da zaman lafiya, fahimta da haɗin kan jama’a....
21/01/2026

NAIBAWA – UNGUWAR ZAMAN LAFIYA DA HAƊIN KAI

Naibawa unguwa ce da aka san ta da zaman lafiya, fahimta da haɗin kan jama’a. Duk da bambancin ra’ayi da rayuwar yau da kullum, mazauna Naibawa suna rayuwa cikin mutunta juna, taimakon juna da tsayawa tsayin daka wajen kare martabar unguwa. Zaman lafiya a Naibawa al’ada ce, ba magana kawai ba, kuma shi ne ginshiƙin cigaban al’umma




20/01/2026

hello 👋

Al'ummar Naibawa
Shiri ya kamata mu fara gabatar wa

ina ne nan a cikin Naibawa
20/01/2026

ina ne nan a cikin Naibawa

Assalamu alaikum Al'ummar Naibawa, fatan kowa yana lafiyaMuna gabatar muku da sabon shafin mu na Naibawa Connect, wanda ...
20/01/2026

Assalamu alaikum Al'ummar Naibawa, fatan kowa yana lafiya

Muna gabatar muku da sabon shafin mu na Naibawa Connect, wanda zai dinga duba abubuwan da suke faruwa a Naibawa da rahoto abin da ke faruwa a yankin

Alhamdulillah Wlh sako yana zuwa inda ya kamata muna matukar godiya ga Allah da ya haɗa mu da mutum mai tsoron Allah da ...
09/05/2024

Alhamdulillah Wlh sako yana zuwa inda ya kamata muna matukar godiya ga Allah da ya haɗa mu da mutum mai tsoron Allah da sanin ya kamata
Allah ya kara lafiya yayi jagoranci

03/01/2024

INA KARA SANAR DAKU IN SHA ALLAH WANNAN SHEKARAR 2024.

=>>>Maigirma Sanata Rufai Sani Hanga zai yin abubuwa kamar haka

1. Sen. Rufai Sani Hanga ya Raba magunguna kyauta a fadin kano Ta Tsakiya√

2. Sen. Rufai Sani Hanga zai bude constituency office.

3. Sen. Rufai Sani Hanga zai bada Jari ga Mata masu kananan sana'oi.

4- Sen. Rufai Sani Hanga zai bada jari mai tsoka ga yara gida sa.

5- Sen. RUFAI SANI HANGA zai raba Tallafin Abinci ga al'ummansa.

6- Sen. Rufai Sani Hanga zai bullo da harkar koyar da sana'o'i kuma zai tallafa ma wadanda s**a koyi sana'o'i da jari.

7- Sen. Rufai Sani Hanga zai raba kayayyakin sana'a ga wadanda rabonsu ya tsaga domin dogaro da kai.

8- Sen. Rufai Sani Hanga zai duba nakasassu da Dattijai wurin basu muhimmaci na musamman.

9- kungiyoyi da dama zasu amfana daga tallafin Sen. RUFAI SANI HANGA


9- Zai duba harkar Ruwan Sha.

10- zai duba harkar noma musamman wurin bada tallafin Taki, Maganin Feshi da sauransu.

12- Sen. Rufai Sani Hanga zai samarma Matasa Aikin yi na din-din-din domin dogaro da kansu.

Da sauransu Insha Allah. Allah ka inganta mashi lafiya don cimma wannan manufa na alkhairi. Amin🙏🙏

✍️✍️
Kashman Usman T Wada
Political Activist for change
3rd Jan. 2024.

Address

Naibawa
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Naibawa Connect posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share