Albarka Group 'Yan awaki

Albarka Group 'Yan awaki Motto: Sadar da Zumunci Da Taimakon Juna

A madadin Shugabancin kungiyar Albarka Group 'Yan awaki, Muna mika sakon bangajiya tare da godiya ga dukkanin mahalarta ...
22/01/2023

A madadin Shugabancin kungiyar Albarka Group 'Yan awaki, Muna mika sakon bangajiya tare da godiya ga dukkanin mahalarta taron cikar wannan kungiyar shekaru biyar (5) masu albarka haɗe da bikin yaye ɗaliban da ta ɗauki nauyin horas dasu ilimin na'ura me ƙwaƙwalwa da fasahar zamani (Computer and IT), Tare da raba kyaututtuka ga makarantun da s**a yi nasara a gasar musabakar data shirya. Muna miƙa godiya ta musamman ga dan takarar Majalisar tarayya na kano Municipal Karkashin jam'iyyar NNPP, Engr. Sagir Koki, da manajan gidan rediyon Arewa Radio Shehu Bala Kabara, Da masu unguwanni da sauran manyan baƙi da yan uwa da abokan arziƙi da ƙungiyoyi da s**a samu damar taya mu murnar wannan taro.

Haka zalika muna miƙa godiya ga dan takarar Majalisar tarayya KMC karkashin jam'iyyar PDP, Engr. Yusuf Da'awah ga sako na kyaututtuka da ya aiko dasu na daliban da s**a yi nasara a musabaka da wannan kungiyar ta shirya. Har ila yau muna godiya ga manajan gidan rediyon Arewa bisa ga kudi da ya bayar a rabawa daliban da s**a yi nasara. Allah ya saka da alkhairi ya wuce gajiya.

Haka zalika muna jinjina da godiya ga kafatanin shugabanni da mambobin wannan kungiya na gudunmawa da s**a bata don ganin taron ya gudana cikin nasara.

Kungiya ta bada kyautar injin Generator, Kujeru, Tabarmi, Marker, Rijistoci, Litattafai ga makarantun da s**a yi nasara daga mataki na daya zuwa na uku. Sannan ta raba Yadi da atamfofi ga dalibai da s**a wakilci makarantun su.

Abubakar Abdulrahim
Secretary AGY

Address

Darbejiya Street 'Yan Awaki
Kano
700251

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Albarka Group 'Yan awaki posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Albarka Group 'Yan awaki:

Share