Angarar Bahaushe

Angarar Bahaushe Shafine domin shawo kan matsalar dake addabar Hausawa

01/05/2025

Shin kuna ganin akwai bukatar bude kungiyar Hausawa Zallah ko kuwa babu?

01/05/2025

Hausa, a matsayin yare ko kabila, sha-kundum ce!

A iya yin wata gidauniya ko kungiya domin bunkasa yare, al’adu da kabilar Hausa. Amma yin wani abu wai Kungiyar Hausawan Nigeria, ci baya ne ga Hausa da Hausawa. Musamman a matsayin kasa Nigeria ko Arewa inda Hausawa s**a fi kowa yawa da karfi.

Su kuma masu yiwa jama’a register da kokarin basu ID card na shaidar zama Hausawa, yan kasuwa ne kawai.

Hausa yare ne kuma kabila mai hadiye yaruka da kabilu ta yadda da dama daga wadanda ba Hausawa ba uslan, yanzu sun rikide sun zama Hausawa kuma suna alfahari da hakan. Duk da a zahiri hakan ci baya ga wadancan kabilun. A yanzu haka, Hausa ta kashe yaruka da dama.

Wannan ya bawa yaren wani irin tasiri fiye da sauran yarukun Afrika ta yamma. Saboda haka kayyade wannan kabila da yare mai albarka, da kokarin fitarda wasu daga cikinta abu ne wanda bana jin zai yiwu.

Daga Barr Abba Hikima

Address

Kano

Telephone

+2348027260260

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Angarar Bahaushe posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share