08/12/2024
08/12/2024
_Burina Shine Al'umma su samu Cigaba domin dorewar zaman lafiya._
Al’ummar Jujin Gobirawa Unguwar Mahauta da ke karamar Hukumar Rimin Gado a Jihar Kano, sun nuna jin dadinsu ga Alhaji Mudassir Adam Danshayi, Shugaban Kungiyar Cigaban Matasan Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa, bisa sadaukarwar da yake yi na ci gaban al’ummarsu.
A ganawar da s**a yi da Shugaban kungiyar, karkashin jagorancin Malam Audu na Babale, al’ummar sun bukaci Shugaban Kungiyar Daya shige musu gaba izuwa Gwamnatin Jiha da Karamar Hukumar Rimin Gado wajen a tallafa musu wajen magance rushewar gidajensu a lokacin damina, da gina musu guraben ajujuwa na makarantun firamare da Islamiyya, da kuma kaura daga mahallin da suke ciki.
Sun yi nuni da cewa al’ummar yankin sun kai dubu daya, inda suke da gidaje kusan dari da hamsin.
Hakazalika sun kara da cewa irin wadannan kungiyoyi sune wadanda Gwamnati ya kamata ta hada hannu dasu ba.
Da yake mayar da martani, Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya jajanta musu halin da suke ciki tare da tabbatar musu da aniyarsa ta warware matsalolin da kuma shige musu gaba wajen cimma abinda aka sanya a gaba.
Ya yi alkawarin bayar da shawarwari ga gwamnati da kuma neman tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu don rage matsalolin da al'umma ke fuskanta.
Shugaban kungiyar Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya kuma bukaci al’umma da su cigaba da yiwa shugabanin kasa, jaha, da kananan hukumomi addu’a domin samun dorewar zaman lafiya da cigaban yankin.
Ya Kuma bukace su dasu kasance masu hakuri da juriya a duk halin da s**a tsinci kansu.
Alhaji Mudassir Adam Danshayi
Chairman Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa Youth Development.