Gwale LGA Development Association

Directions

Gwale LGA Development Association Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gwale LGA Development Association, Community Organization, 260, Sani Mainagge, Kano.

Sanata Rufa'i Sani Hanga ya bayyana haka ne a hirarshi da ɗan jarida, Yakubu Musa Fagge.
03/08/2026

Sanata Rufa'i Sani Hanga ya bayyana haka ne a hirarshi da ɗan jarida, Yakubu Musa Fagge.

Idan Sanata Rufai Hanga ya koma jam’iyyar APC, shin waye ya fi dacewa da takara kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya?
03/08/2026

Idan Sanata Rufai Hanga ya koma jam’iyyar APC, shin waye ya fi dacewa da takara kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya?

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Yakubu Jang, ɗan tsohon Gwamnan Jihar Filato, Jonah Jang, a matsayin Babban Ma...
02/08/2026

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Yakubu Jang, ɗan tsohon Gwamnan Jihar Filato, Jonah Jang, a matsayin Babban Mataimaki na Musamman (Senior Special Assistant) a Ofishin Shugaban Ƙasa. An bayyana naɗin ne yayin bikin cika shekaru 80 da haihuwar Jonah Jang da kuma ƙaddamar da littafinsa a Jos.

Wannan naɗi na ci gaba da jan hankalin jama'a, musamman saboda Yakubu Jang ya fito daga gidan tsohon gwamnan da ya yi fice a siyasar Filato kamar yada Jaridar Punch da Vanguard S**a rawaito

Masu sa ido na kallon matakin a matsayin wani ɓangare na sabbin naɗe-naɗen da gwamnatin Tinubu ke yi domin ƙarfafa aikin gwamnati.

Daga Gambiza Tv

01/08/2026
Wani jigo a tafiyar Pantamiyyah, Comrade Albishir, ya bayyana cewa al’ummar Gombe za su more ingantaccen tsaro da ci gab...
08/06/2026

Wani jigo a tafiyar Pantamiyyah, Comrade Albishir, ya bayyana cewa al’ummar Gombe za su more ingantaccen tsaro da ci gaba idan s**a bai wa Professor Isa Ali Pantami damar jagoranci.

A cewarsa, Pantami mutum ne da ya nuna kwarewa, gaskiya da kishin al’umma, yana mai jaddada cewa dukiya da rayukan Gwambawa za su samu kariya da kwanciyar hankali a karkashin jagorancinsa.

Comrade Albishir ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi la’akari da irin gudummawar da Pantami ya bayar a fannoni daban-daban, yana mai cewa idan aka ba shi dama, zai kawo ci gaba mai ɗorewa da inganta rayuwar jama’a a fadin jihar.

Rahotanni daga Jihar Zamfara sun nuna cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da dattawa kusan 50 daga kauyen Magamin Diddi da ...
08/06/2026

Rahotanni daga Jihar Zamfara sun nuna cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da dattawa kusan 50 daga kauyen Magamin Diddi da ke yankin Magami/Faru a Karamar Hukumar Maradun.
Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da aka shirya wata tattaunawar sulhu da wani shugaban ’yan bindiga da ake kira Jammo, wanda ake zargin shi ne ya nemi a yi zaman sulhu bayan da wasu daga cikin mabiyansa s**a rasa rayukansu a wani farmakin jami’an tsaro.

Sai dai bayan tawagar dattawan da aka tura domin halartar ganawar ta isa wajen, ‘yan bindigar sun tsare su tare da yin garkuwa da su.

Shugaban Karamar Hukumar Maradun, , ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa dattawan sun shiga tattaunawar sulhu ne ba tare da amincewar ko sahalewar gwamnatin jihar ba.

Ya kara da cewa gwamnatin Jihar Zamfara ba ta goyon bayan duk wani yunkuri na yin sulhu kai tsaye da ’yan bindiga, yana mai jaddada bukatar bin tsarin gwamnati da hukumomin tsaro wajen duk wani matakin tattaunawa ko sulhu.

DOVE NEWS

Mukhtar Abubakar Tafawa Balewa, ɗan marigayi Firaministan Najeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa, ya bayyana yadda ma...
08/06/2026

Mukhtar Abubakar Tafawa Balewa, ɗan marigayi Firaministan Najeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa, ya bayyana yadda mahaifinsa ya gudanar da rayuwa cikin gaskiya da riƙon amana lokacin yana mulki.

A cewarsa, marigayin bai amince a riƙa amfani da kuɗin gwamnati wajen ciyar da iyalinsa ko gudanar da harkokin gidansa ba, domin albashinsa na aiki yake amfani da shi wajen tafiyar da rayuwar iyalinsa.

Address

260, Sani Mainagge
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gwale LGA Development Association posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share