27/03/2026
ABUN KUNYA NE, ABUN BAN HAUSHI! GA JARIMI ALI NUHU
Abin takaici ne ganin wasu mutane har yanzu ba su fahimci illar kashe ɗan ta’adda ba—ba wai don tausayi ba, sai don hikima da tsaro na ƙasa.
Ina magana ne kai tsaye ga Ali Nuhu da duk wanda yake da irin wannan ra’ayi.
Eh, gaskiya ne—Human Rights ba ta goyon bayan kashe ɗan ta’adda ba.
Amma tambaya ita ce: shin kun fahimci DALILI?
Kashe ɗan ta’adda k**ar kashe maciji ne ba tare da sare kansa ba. Ka kashe guda ɗaya, amma tushen matsalar yana nan daram!
Tambaya ga masu hankali:
Shin waɗannan ‘yan ta’adda suna aiki ne su kaɗai?
Ko akwai MANYAN MUTANE a bayan su‘yan siyasa, masu kuɗi, masu iko—waɗanda ke cin gajiyar wannan ta’addanci?
Idan aka kashe ɗan ta’adda, wa zai tona asirin waɗanda ke ɗaukar nauyinsa?
Ku tuna tarihi: lokacin da aka k**a shugaban Boko Haram, ya fara tona wasu asirai masu girma… amma me ya faru? An kashe shi kafin ya gama magana.
Shin wannan ya kawo ƙarshen Boko Haram ne? Amsar ita ce A’A!
Saboda matsalar ba a sama take ba—a ƙasa take, a ofisoshi take, a hannun masu iko take!
A Nigeria akwai nau’ikan ‘yan ta’adda guda biyu:
Na daji – masu bindiga, masu garkuwa da mutane, masu kashe rayuka.
Na ofis – masu kujeru, masu bada umarni,
masu cin ribar jini da hawaye.
Wadannan na ofis su ne tushen matsala!
Shi ya sa idan aka k**a ɗan ta’adda, sai ka ga an sake shi.
Me yasa?
Saboda ubannin gidansa suna zaune a ofis suna bada umarni!
Amma ina matsalar take?
Mu ne matsalar! Ni da kai!
Ba ma bin diddigi, ba ma tambaya, ba ma neman gaskiya.
Sai mu yi shiru, mu zama bayi cikin ƙasarmu.
Saboda haka: Ina kira ga Ali Nuhu da ya sake duba wannan magana nasa, ya janye ta, domin irin wannan bayani na iya rikitar da jama’a da raunana fahimtar yaki da ta’addanci.
Yaki da ta’addanci ba kashe mutum kawai bane—yaki ne da tsari, da masu daukar nauyi, da masu cin moriya!