TGT Africa

TGT Africa News Updates

Isra’ila da Amurka sun kai hari ga Jamhuriyar Musulunci, suna nufin zuciyar gwamnatin ƙasar…Isra’ila tare da haɗin gwiwa...
28/02/2026

Isra’ila da Amurka sun kai hari ga Jamhuriyar Musulunci, suna nufin zuciyar gwamnatin ƙasar…

Isra’ila tare da haɗin gwiwar Amurka ta kai hare-hare a Iran a ranar Asabar din nan, inda aka kai farmaki wurare da dama yayin da aka ruwaito fashe-fashe a Tehran da wasu birane.

Daya daga cikin muhimman wuraren da aka kai hari shi ne ofishin jagoran addini na Iran, Ali Khomeini, da ke tsakiyar Tehran. Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ce Khamenei bai kasance a wurin ba yayin harin, duk da cewa ba a tabbatar da hakan kai tsaye ba.

Bidiyoyin da ke yawo a yanar gizo sun nuna hayaki mai duhu yana tashi daga yankin da ake dangantawa da hedkwatar jagoran addinin wurin da ake ɗauka a matsayin cibiyar ikon gudanarwa na gwamnatin Iran.

Bayan hare-haren, rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa an harba makamai daga Iran zuwa yankin Isra’ila, lamarin da ya sa aka kunna kararrawar gargadi a arewacin Isra’ila yayin da ake kallon harin a matsayin alamar farko ta martanin Tehran.

Wani jami’in Iran ya shaida cewa martanin ƙasar zai kasance “mai ƙarfi,” abin da ya tayar da fargabar cewa rikicin na iya fadada zuwa yaƙin yankin gaba ɗaya.

Hukumomi a Iran sun fara takaita sadarwa yayin da hare-haren ke gudana.

Kungiyar lura da yanar gizo ta NetBlocks ta ruwaito cewa karfin intanet ya ragu zuwa kusan kaso 54 cikin ɗari na yadda aka saba, yayin da kafafen yada labarai na Iran s**a ce an samu katsewar hanyoyin sadarwar waya da manhajojin aika saƙo. Haka kuma, wasu shafukan labarai na Iran an ruwaito cewa an yi musu kutse a yayin ayyukan yaƙin yanar gizo.

Wannan tashin hankali ya zo ne makonni kaɗan bayan jami’an tsaro sun gudanar da mummunan kame-kame a fadin ƙasar inda aka kashe dubban Iraniyawa, abin da aka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni a tarihin kasar.

Hare-haren yanzu suna gudana a cikin yanayin fushi na cikin gida da matsin lamba mai tsanani kan gwamnatin da ke mulki.

Yarima Reza Pahlavi ya kira Iraniyawa da su shirya komawa kan tituna, yana bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta kusa rushewa, tare da roƙon jama’a da su kwantar da hankalinsu su jira ƙarin umarni.

Hasumiyar Gobarau KatsinaWannan hasumiya mai tsohon tarihi an gina ta a shekarar 1348, a zamanin sarkin Katsina Muhammad...
24/07/2025

Hasumiyar Gobarau Katsina

Wannan hasumiya mai tsohon tarihi an gina ta a shekarar 1348, a zamanin sarkin Katsina Muhammadu Korau (Kangiwa, 2014). Ita wannan hasumiya wani ɓangare ce ta babban masallacin Juma’a da ke cikin tsohon birnin Katsina. Wannan masallaci ya taɓa zama babbar jami’ar da take a matsayin reshen jami’ar Sankore da ke Timbuktu ta ƙasar Mali. Ko siffar wannan hasumiya na tabbatar da haka. Bayan wannan kuma wannan masallaci shi ne masallacin farko da aka fara yi a garin na Katsina.

Ita wannan hasumiya a wancan lokaci ita ce gini mafi tsawo a garin na Katsina, saboda haka takan zama wata kafa ta leƙen asirin tsaro. Abin nufi shi ne cewa ana hawa kanta a hango nesa, musamman yankin Gobir, dan hango abokan gaba daga nesa idan sun yi nufin kawo wa Katsina hari, wannan kuma takan bawa ita Katsina cikakkiyar damar shirya faɗa da waɗannan abokan gaba.

Address

Farm Centre Road Kano
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TGT Africa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to TGT Africa:

Share