30/06/2026
CIKAKKEN RAHOTON ZAMAN KOTUN ƊAUKAKA ƘARA TA JIHAR KANO:
(Shari'ar Ɗaukaka Ƙara Tsakanin Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara da Gwamnatin Jihar Kano)
Ranar Zama: 29 ga Yuni, 2026
Wurin Zama: Kotun Ɗaukaka Ƙara, Miller Road, Kano
1.0 GABATARWA:
A ranar Litinin, 29 ga Yuni, 2026, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Kano mai zama a Miller Road ta gudanar da zamanta domin sauraron shari'ar ɗaukaka ƙarar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya shigar, yana ƙalubalantar hukuncin da Kotun ƙasa ƙarƙashin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta yanke a baya.
Zaman kotun ya gudana ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nasir Saminu da Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji.
2.0 BAYYANAR LAUYOYIN ƁANGARORI:
Bayan kiran shari'ar, Jagoran Lauyoyin Mai Ɗaukaka Ƙara (Appellant), Barrista Adamu Garba, SAN, ya bayyana tare da tawagarsa domin wakiltar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
Sai dai a wannan lokaci, lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano sun nemi alfarma daga kotu na ɗan jinkirta ci gaba da shari’ar har zuwa isowar Jagoran tawagarsu, Barrista Sa’ida, SAN, wanda s**a bayyana cewa yana riƙe da muhimman takardun shari’ar. Kotun ta amince da wannan buƙata tare da ci gaba da sauraron wata shari’a daban a lokacin.
3.0 TARIHIN ABIN DA YA GABATA A WANCAN MAKO:
A zaman da ya gabata, lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano sun bayyana wa kotu cewa ba su kammala shirye-shiryensu ba, tare da neman ƙarin lokaci domin su gabatar da rubutaccen martaninsu ga ƙorafin ɗaukaka ƙarar.
Lauyoyin Sheikh Abduljabbar ba su nuna adawa da wannan buƙata ba, inda kotun ta ba da damar da aka nema.
Daga baya, lauyoyin Mai Ɗaukaka Ƙara sun tabbatar da cewa sun karɓi rubutaccen martanin lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano, sannan su ma sun gabatar da nasu martanin bisa tanade-tanaden doka. Dukkanin ɓangarorin sun tabbatar da hakan a gaban kotu.
4.0 CI GABAN SAURARON SHARI’AR:
Bayan kammala shari’ar da aka saurara a lokacin da aka jinkirta wannan shari’a, kotu dai ta sake kiran shari’ar domin ci gaba da sauraron ta.
A wannan karo, Jagoran Lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano, Barrista Sa’ida, SAN, ya hallara tare da tawagarsa. Dukkanin ɓangarorin biyu sun tabbatar wa kotu cewa sun shirya tsaf domin ci gaba da shari’ar.
Kotun ta bai wa Mai Ɗaukaka Ƙara damar gabatar da ƙorafinsa da hujjojinsa.
5.0 MUHIMMAN BATUTUWAN ƊAUKAKA ƘARAR:
Da yake gabatar da ƙarar, Jagoran Lauyoyin Mai Ɗaukaka Ƙara, Barrista Adamu Garba, SAN, ya roƙi kotu da ta soke tare da rushe gaba ɗaya hukuncin da Kotun Ƙasa (Lower Court) ƙarƙashin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ta yanke.
A cewar lauyoyin Mai Ɗaukaka Ƙara, hukuncin da ake ƙalubalanta ya ƙunshi kura-kurai masu yawa ta fuskar doka da kuma yadda aka gudanar da shari’ar, wanda hakan ne ya sanya s**a nemi kotun ɗaukaka ƙara ta sake nazari tare da yanke hukunci bisa ƙa’idojin adalci.
6.0 GABATAR DA TAKARDU DA HUJJOJI:
Babban abin da zaman kotun ya mayar da hankali a kai shi ne gabatarwa tareda amincewa da takardun shari’a (Adoption of Written Briefs and Processes) da ɓangarorin biyu s**a miƙa wa kotu.
Lauyoyin Sheikh Abduljabbar sun gabatar da dukkanin takardu da hujjojin da suke dogaro da su wajen neman rushe hukuncin kotun farko.
Haka nan, lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano sun gabatar da nasu takardu da hujjoji domin kare matsayin hukuncin da aka yanke a kotun farko.
Kotun ta karɓi dukkanin takardun ɓangarorin biyu domin yin cikakken nazari a kansu.
7.0 MATSAYAR KOTU
Bayan karɓar takardun da hujjojin da aka gabatar, kotun ta bayyana cewa zata nemi wasu littattafai waɗanda an ambacesu a Shari’ar baya. Samun litattafan zai baiwa wannan kotu dama da hujjoji domin nazarin hukuncin kotun farko, duba da cewa mai Mai Ɗaukaka Ƙarar ya yi shahidi da su a yayin kare kansa tun a kotun ƙasan.
Kotun ta bayyana cewa za ta yi cikakken nazari a kan waɗannan littattafai tare da sauran takardun da aka gabatar kafin ta yanke hukuncin ƙarshe a wannan shari’a.
8.0 KAMMALUWAR RAHOTO:
A ƙarshe, kotun ta kammala sauraron gabatarwar ɓangarorin biyu tare da ɗaukar dukkanin takardu da hujjojin da aka gabatar a gabanta domin yin nazari.
Kotun ta sanar da cewa za ta bayyana ranar da za ta yanke hukuncin ƙarshe ga dukkanin ɓangarorin a wani lokaci na gaba bayan kammala nazarin dukkanin bayanai da hujjojin da ke gabanta.
Wannan rahoto ne wanda Channel (daga sashin REPORTERS) domin Bayar da Sahihin Bayani Kan Yadda aka Gudanar da Zaman Kotun Ɗaukaka Ƙara na Ranar 29 ga Yuni, 2026.
Kada a manta, wannan Shari’ah ce wacce Manyan Ƙungiyoyin Fararen Hula na Ciki da Wajen wannan ƙasa (Nigeria) suke sanyawa idanu, domin tabbatar da anyi adalci. Duba da yadda Shari’ar ta gudana a baya.
~ AKAFSAN Reports (30/06/2026)