20/03/2026
KWARU YOUTH NETWORK
(RAHOTON CIYARWAR RAMADAN DA DAWAINIYAR MARAYU)
Assalamu Alaikum wa rahmatullah!
Iyayen mu,yan'uwa da abokan arziki Masu albarka,Wanda s**a jajirce wurin ganin mun sauke aikin da muka dauko a wata Mai albarka na Ramadan da ta wuce da kuma wannan bikin sallah karama,lallai hakika gudunmowa da kuka bayar ya bamu daman ciyarwa kamar haka:
1. Baiwa Marayu guda 70 danyen abinci domin ci gaba da azumi
2. Raba Abincin IFTAR wa mutane dubu Daya da Dari Tara da sittin (1,960)a tsawon kwanaki 28
3. Rabawa Marayu 70 kayan sallah
4. Rabawa Marayu 35 Abincin sallah
5. Yanka sa(shanu) da Raba Naman ga Marayu 60
Duka wannan ya samu ne saboda jajircewan Ku da gudunmowar Ku.Allah muke roko yasa wannan ya zama sanadiyyan shiganku al'jannah da mu Baki daya.Allah ya karba mana da Ku Baki daya.
Mun gode!Mun gode!! Mun gode!!!