Zazzau Youth Progressive Forum

Directions Website

Zazzau Youth Progressive Forum Aims To Empower Young People and Enhance Their Participation In Governance, Education, and Community

16/09/2026

Abinda aka damu da shi, lallai shi ake damuwa idan an rasa shi 👌

BARKA DA JUMA’A 🕌Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Ƙungiyar Zazzau Youth Progressive Forum (ZYPF) na miƙa gais...
11/09/2026

BARKA DA JUMA’A 🕌

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Ƙungiyar Zazzau Youth Progressive Forum (ZYPF) na miƙa gaisuwar Barka da Juma’a ga daukacin al’ummar Zazzau da Kasa Baki daya. Muna roƙon Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya ƙara mana zaman lafiya, haɗin kai da albarka Ameen

Haka kuma, ƙungiyar na miƙa Sakon ta’aziyya ta musamman ga MAGA ISAN ZAZZAU bisa babban rashi da aka yi. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙan mamacin, Ya gafarta masa, Ya sanya Aljannar Firdausi ce makomarsa, sannan Ya bai wa iyalansa, ‘yan uwansa da dukkan masoyansa haƙuri da juriya wajen jure wannan babban Rashi da aka yi

Zazzau Youth Progressive Forum (ZYPF)
Mu Amfana, Mu Amfanar.

Kukan Kurciya …………..
01/09/2026

Kukan Kurciya …………..

🎉 SAƘON TAYA MURNA 🎉Zazzau Youth Progressive Forum (ZYPF) na taya ɗaya daga cikin jajirtattun membobinta murnar samun ƙa...
31/08/2026

🎉 SAƘON TAYA MURNA 🎉

Zazzau Youth Progressive Forum (ZYPF) na taya ɗaya daga cikin jajirtattun membobinta murnar samun ƙaruwa a rayuwar aure. 💍❤️

ABDULHAKIM ADAMU ABBAS

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya wannan sabon mataki na rayuwa ya kasance mai albarka, farin ciki da zaman lafiya.

Allah Ya haɗa zukatanku a kan alheri, Ya ba ku zaman lafiya da zuri’a ta gari. 🤲

Congratulations! 🎊❤️

ZAZZAU YOUTH PROGRESSIVE FORUM (ZYPF)
Mu amfana, mu amfanar.Zazzau Youth Progressive Forum

ZAZZAU YOUTH PROGRESSIVE FORUM (ZYPF)A cikin ci gaba da ayyukan jin kai da gina al'umma, Zazzau Youth Progressive Forum ...
29/07/2026

ZAZZAU YOUTH PROGRESSIVE FORUM (ZYPF)

A cikin ci gaba da ayyukan jin kai da gina al'umma, Zazzau Youth Progressive Forum (ZYPF) ta kai ziyarar sada zumunci zuwa gidan gyaran hali (Prison/Correctional Centre) domin ƙarfafa gwiwa ga waɗanda ke can tare da nuna musu cewa har yanzu al'umma tana tare da su.
Wannan ziyara ta kasance wata hanya ta nuna ƙauna, tausayi da haɗin kai, tare da ƙarfafa musu gwiwar komawa cikin al'umma bayan sun gyara halayensu.
Muna gode wa dukkan official da mambobin ƙungiyar da s**a ba da gudummawarsu wajen ganin wannan ziyara ta gudana cikin nasara.
PRO 2
BILKISU ABUBAKAR
🌟 ZAZZAU YOUTH PROGRESSIVE FORUM (ZYPF)

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN Allah Ya yi wa Alhaji Zakari Aminu Salihu rasuwa.Marigayin ya kasance Tsohon Ma'ajin...
19/07/2026

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Allah Ya yi wa Alhaji Zakari Aminu Salihu rasuwa.

Marigayin ya kasance Tsohon Ma'ajin Kuɗi na Jihar Kaduna, sannan kuma Tsohon Ma'aikaci a Hukumar Sufuri ta Ƙasa.

Za a sanar da lokacin Sallar Jana'izarsa nan gaba, idan Allah Ya so.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya haskaka masa kabari, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Allah Ya bai wa iyalansa, 'yan uwansa da abokan arziki haƙurin jure wannan babban rashi.

ZAZZAU YOUTH PROGRESSIVE FORUM Ziyarar Girmamawa Ta Musamman.A yau, tawagar Zazzau Youth Progressive Forum (ZYPF), ƙarƙa...
04/07/2026

ZAZZAU YOUTH PROGRESSIVE FORUM

Ziyarar Girmamawa Ta Musamman.

A yau, tawagar Zazzau Youth Progressive Forum (ZYPF), ƙarƙashin jagorancin shuwagabanninta, ta kai ziyarar girmamawa ta musamman ga Hon. Shuaibu Abdullahi (Mai Canter), Sakataren Zaria Local Government Council, domin ƙarfafa alaƙa da tattauna batutuwan da s**a shafi ci gaban matasan Zazzau Dama Jahar Kaduna Baki Ɗaya.

Ziyarar ta ba da dama wajen musayar ra'ayoyi kan muhimman batutuwan da s**a shafi ci gaban matasa, haɗin kai, da yadda za a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin matasa domin samar da cigaba mai ɗorewa.

Mun samu kyakkyawar tarba da karɓuwa daga Hon. Shuaibu Abdullahi, wanda ya nuna goyon baya ga duk wani yunƙuri da zai amfani matasan Zazzau da al'ummar ƙaramar hukumar Zariya baki ɗaya. Hakan ya ƙara mana ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da gudanar da ayyukan da s**a dace da manufar ƙungiyarmu.

Muna miƙa godiyarmu gare shi bisa lokaci da shawarwari masu amfani da ya ba mu. Muna kuma roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya Kara Masa lafiya, hikima, ƙarfin guiwa da nasara wajen gudanar da ayyukansa.

Zazzau tamu ce, ci gabanta alhakinmu ne. Mu haɗa kai domin gina kyakkyawar makoma ga matasanmu da al'ummarmu.

Allah Ya Albarkaci Masarautar Zazzau.
Allah Ya Albarkaci Jihar Kaduna.
Allah Ya Albarkaci Tarayyar Najeriya. 🇳🇬

Sanarwa:

Sheikh Jerfer Aleeyou
PRO
Zazzau Youth Progressive Forum (ZYPF)

RANAR DUNIYA TA SICKLE CELL"Mu nuna ƙauna, mu ba da kulawa, mu ba da fata."A wannan Ranar Duniya ta Sickle Cell, muna mi...
20/06/2026

RANAR DUNIYA TA SICKLE CELL

"Mu nuna ƙauna, mu ba da kulawa, mu ba da fata."

A wannan Ranar Duniya ta Sickle Cell, muna miƙa saƙon ƙauna da tausayawa ga dukkan masu fama da cutar Sickle Cell a cikin al’ummarmu. Ku sani cewa ba ku kaɗai ba ne; muna tare da ku, muna jin ku, kuma muna goyon bayanku.

Sickle Cell ba hukunci ba ne, kuma ba ya hana mutum cimma burinsa. Duk da ƙalubalen da masu fama da wannan cuta ke fuskanta, suna da ƙarfin zuciya, juriya da hakuri. Muna kira ga iyalai, abokai da al’umma da su nuna ƙauna, kulawa da fahimta ga masu fama da cutar.

Ga matasa da iyaye, yana da muhimmanci mu san genotype ɗinmu kafin aure domin rage yawaitar cutar a cikin al’umma. Ilimi da wayar da kai su ne mabuɗin kare rayuwar al’umma ta gaba.

Ga dukkan masu fama da Sickle Cell, muna cewa: Ku ci gaba da kasancewa masu ƙarfi. Kada ku rasa bege. Ku kula da lafiyarku, ku bi shawarar likitoci, kuma ku sani cewa rayuwarku tana da matuƙar muhimmanci.
Mu daina wariya. Mu nuna ƙauna. Mu ba da fata.

"Tare za mu iya gina al’umma mai kulawa da fahimtar masu fama da Sickle Cell."




INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UNCikin alhini da jimami muka samu labarin rasuwar Malam Yusuf Fancy.Muna miƙa ta'aziyy...
19/06/2026

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Cikin alhini da jimami muka samu labarin rasuwar Malam Yusuf Fancy.

Muna miƙa ta'aziyyarmu ga iyalai, 'yan uwa, abokai da duk masu ƙaunarsa bisa wannan babban rashi.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya jiƙansa da rahama, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, Ya kuma bai wa iyalansa da masoyansa haƙurin jure wannan rashi.

Allah Ya jiƙan Malam Yusuf Fancy, Ya sanya Aljanna ce makomarsa. Amin Ya Rabbal Alamin. 🤲🏻

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un.

za'ayimai salatul GA'IB (1:00) a masallaci shiekh Dalhat Assalafy dake Tudun jukun Zaria

Address

Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zazzau Youth Progressive Forum posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share