Abu-haidar Islamic Da'awa and Relief Foundation

Abu-haidar Islamic Da'awa and Relief Foundation the foundation is for Da'awa and Service to Humanity

02/05/2026
20/03/2026

🌙 Falalar Azumi 6 na Watan Shawwal
✍️ Engr Hamza Aliyu

Godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki, Ubangijin talikai, Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Annabi Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki ɗaya.
Bayan kammala azumin watan Ramadan, Allah Ya shar’anta wasu ibadu da ke ƙara kusantar da bawa zuwa gare Shi. Daga cikin waɗannan akwai azumin kwanaki shida na watan Shawwal, wanda yake da falala mai girma.

📖 Hujja daga Sunnah

An karɓo daga Abu Ayyub al-Ansari cewa Manzon Allah ﷺ ya ce:
"Duk wanda ya azumci Ramadan sannan ya biyo shi da kwanaki shida daga Shawwal, kamar ya azumci shekara ɗaya ne."
(Sahih Muslim)
Wannan hadisin yana nuna girman lada da falalar wannan azumi, domin lada yana ninkuwa har ya zama kamar azumin shekara gaba ɗaya.

📖 Hujja daga Al-Qur’ani

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
"Duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki, yana da lada goma irinsa..."
(Al-Qur'an 6:160)
Saboda haka, azumin Ramadan (kwanaki 30 × 10 = 300), sannan sittu na Shawwal (6 × 10 = 60), jimilla = 360, wanda ya yi daidai da kwanakin shekara.

🕌 Maganganun Malamai

1. Mazhabar Shafi’iyya

Imam al-Nawawi ya ce:
"Wannan hadisi hujja ce karara ga mustahabbancin azumin sittu na Shawwal."

2. Mazhabar Hanbaliyya

Ibn Qudamah ya bayyana cewa:
"Azumi 6 na Shawwal mustahabbi ne, kuma yana da lada mai yawa kamar yadda hadisi ya nuna."

3. Mazhabar Malikiyya

Imam Malik ya kasance yana taka-tsantsan, amma malamai daga baya sun tabbatar da falalarsa bisa hadisi sahihi.

4. Mazhabar Hanafiyya

Ibn Abidin ya bayyana cewa:
"Azumi 6 na Shawwal abu ne mai kyau (mustahabbi), idan babu tsoron mutane su ɗauke shi wajibi."

🌟 Hikimar Azumin Shawwal

Yana cike gibin da ya samu a azumin Ramadan
Yana nuna godiya ga Allah bayan ibada
Yana ƙarfafa ci gaba da ibada bayan Ramadan
Yana daga cikin alamomin karɓuwar aikin bawa

🌸 Yadda Ake Azumin

Za a iya yin su a jere ko a rarrabe
Ana fara su bayan ranar Idi
Wanda ke da bashin Ramadan, ya fi kyau ya fara biya kafin sittu

Azumi 6 na Shawwal wata babbar dama ce ga mumini domin ƙara lada da kusanci ga Allah. Wanda ya yi amfani da wannan dama, hakika ya yi riba mai girma.
Muna roƙon Allah Ya ba mu ikon yin wannan ibada, Ya kuma karɓa daga gare mu. Ameen

Allah ya kaimu lafiya Ameen
16/02/2026

Allah ya kaimu lafiya Ameen

17/01/2026

ABU-HAIDAR ISLAMIC DA‘AWA AND RELIEF FOUNDATION
BUƊE ASUSUN RAMADAN 2026 / 1447AH
Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.
‘Yan’uwa Musulmi, masu hannu da shuni, masu neman lada da rahamar Allah,
Muna miƙa wannan kira gare ku da zuciya ɗaya, domin ku kasance cikin masu tallafa wa marayu da gajiyayyu a wannan watan Ramadan mai albarka.
Kamar yadda aka saba a kowace shekara, Abu-Haidar Islamic Da‘awa and Relief Foundation ta buɗe Asusun Ramadan 2026 / 1447AH, domin gudanar da ayyukan jin-ƙai da tallafi ga marayu da gajiyayyu, waɗanda s**a haɗa da:
Raba kayan abinci domin shirin fara azumin Ramadan
Raba abincin buɗa-baki (Iftar) na tsawon kwanaki 29 a watan Ramadan
Yin kayan sallah domin su ji daɗin ranar sallah kamar sauran yara
Raba kayan abinci ga marayu da gajiyayyu domin bikin sallah
Siyan shanu domin yankawa da raba nama ga marayu da gajiyayyu
Ya ku masu tausayi, wannan wata dama ce ta musamman ta samun lada mai yawa. Domin duk wanda ya ciyar da mai azumi ko ya faranta ran maraya ko gajiyayye, Allah (SWT) yana rubuta masa lada mai girma ba tare da ƙididdiga ba.
Kada mu bari waɗannan marayu da gajiyayyu su shiga watan Ramadan da ranar sallah cikin ƙunci da rashin gata.
Saboda haka, muna roƙonku da ku bayar da gudummawa daga abin da Allah Ya h**e muku — ko kaɗan ne ko mai yawa, domin Allah ba Ya raina kyakkyawar niyya. Haka kuma, muna roƙonku da ku taimaka wajen yaɗa wannan saƙo ga ‘yan’uwa da abokai domin su ma su sami damar bada tasu gudummawar.
Allah Ya saka wa duk masu tallafawa da alheri, Ya kuma ba mu ikon cika wannan aiki bisa yardarSa. 🤲🏽
Bayanan Asusun Banki
Account Name: Abu-Haidar Islamic Da‘awa and Relief Foundation
Account Number: 0005941909
Bank: TAJBank
📞 Domin ƙarin bayani:
08080996571

14/11/2025

ABU-HAIDAR ISLAMIC DA'AWA AND RELIEF FOUNDATION
مؤسسة أبي حيدرة الإسلامية للدعوة والإسعاف

The Ramadan support fund for orphans under the care of this foundation has been opened.

As is the annual practice, this fund is opened before the arrival of the month of Ramadan to ease the process of assisting orphans and the less privileged—by providing them with food and clothing so they can observe Ramadan just like other members of the Muslim community.

We will continue to remind you about this blessed foundation every week, God willing.

Even though we are not certain whether we will be granted the opportunity to observe this year’s fast, we still have the chance to offer our contributions from now, in support of those in need.

Account Name: ABU-HAIDAR ISLAMIC DA'AWA AND RELIEF FOUNDATION
Account Number: 0005941909
Bank Name: Tajbank

Contact:
08080996571

24/10/2025

Dausayin Shiriya 91-95

24/10/2025

Dausayin Shiriya 86-90

Address

Gwava Road Unguwan Dosa
Kaduna

Telephone

+2348080996571

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abu-haidar Islamic Da'awa and Relief Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share