16/07/2026
Yaya Ake Aika Saฦon Email? Kuma Mene ne Bambanci Tsakanin Email da Gmail?
Nayi mamaki lokacin da na fahimci cewa akwai mutane da yawa masu amfani da wayoyin Android na zamani, amma basu san yadda ake aika saฦon Email ba. Wannan ne yasa zanyi wannan bayanin domin mu amfana gabaษaya.
An kiyasta cewa Gmail yana da sama da mutane biliyan 1.8 masu amfani da shi a duniya. Duk da haka, ana hasashen cewa tsakanin 70% zuwa 80% na masu amfani da shi basu iya aika saฦon Email yadda ya k**ata ba.
Mene ne Email?
Email na nufin Electronic Mail, wato hanyar aika saฦonni ta amfani da internet.
Yana k**a da aika wasiฦa, amma maimakon amfani da takarda ana amfani da waya, computer ko wata na'ura da take amfani da Internet. Ta Email zaka iya aika saฦo, hotuna, takardu, bidiyo da sauran Files ga kowa a ko'ina cikin duniya.
Misali: Idan kana son tura CV, takardar neman aiki, ko wasu muhimman takardu, Email na ษaya daga cikin hanyoyin da ake amfani dasu.
Mene ne Gmail?
Gmail kuwa wani Email Service ne da kamfanin Google ya ฦirฦira domin mutane su riฦa amfani da Email cikin sauฦi.
Misali, idan adireshin Email ษinka yana ฦarewa da:๐
"[email protected]" - To kana amfani da Gmail ne.
Idan kuma yana ฦarewa da: ".com" โ kana amfani da Yahoo Mail.
- ".com" โ kana amfani da Outlook.
- ".com" โ kana amfani da iCloud Mail, wanda aka fi amfani da shi a na'urorin Apple.
Akwai kamfanoni da dama da suke bada services na Email, kuma duk aikinsu iri ษaya ne. Dukkansu suna baka damar aikawa da karษar saฦonni ta hanyar internet.
Wasu daga cikinsu sune k**ar haka:
- Gmail
- Yahoo Mail
- Outlook
- Hotmail
- iCloud Mail
- Proton Mail
- Zoho Mail
Duk waษannan Email Providers ne. Bambancin da ke tsakaninsu bawai ษaya ya fi ษaya zama Email bane, sai dai suna da fasaloli daban-daban. Gmail ya fi shahara ne saboda yawan masu amfani dashi da kuma ฦarfin kamfanin Google.
Saboda haka, Gmail ba shi ne Email ba. Gmail hanya ce ta amfani da Email.
Misali, k**ar yadda akwai motoci iri-iri k**ar Toyota, Honda, Peugeot da Mercedes, duk motoci ne. Haka ma Gmail, Yahoo Mail da Outlook, duk hanyoyi ne na amfani da fasahar Email.
Yadda Ake Aika Saฦon Email Ta Gmail
Idan kana da asusun Gmail, ga yadda zaka aika saฦo:
1. Ka Buษe Gmail App dinka.
2. Danna "Compose" ko "New Message"
3. Ka rubuta abinda kakeso aikawa.
Kuma a nan zaka rubuta adireshin Email na wanda zaka aika wa saฦon.
Misali: "[email protected]"
ko "[email protected]"
Wurin da aka rubuta Subject: A nan zaka rubuta taken saฦonka a taฦaice.
Misali:
- Neman Aiki
- Gaisuwa
- Neman Taimako
Wurin da aka rubuta message: shine wurin da zaka rubuta cikakken saฦonka.
Idan kana son wurin aikawa sakon ka haษa da takarda, hoto ko wani file, sai ka danna alamar paperclip (๐) da ke saman shafin. Daga nan zaka zaษi file ษin daga wayarka, sai kawai ka danna "Send"
Bayan ka gama rubuta saฦonka kuma ka haษa duk abin da kake son turawa, sai ka danna alamar Send (โค).
Shikenan! Saฦonka ya tafi zuwa ga wanda ka aika wa.
Haka ake amfani da sauran Email Services k**ar Yahoo Mail, Outlook, iCloud Mail da sauransu, tsarinsu kusan iri ษaya ne.
- Email fasaha ce ta aikawa da karษar saฦonni ta internet.
- Gmail kuma ษaya ne daga cikin hanyoyin (Email Services) da ake amfani da su wajen amfani da Email.
- Saboda haka, ba duk Email ba ne Gmail, amma Gmail yana cikin Email.
Allah Ya sa wannan bayani ya zama sanadin amfanin mutane da yawa.
ยฉSalisu Abdurrazak Saheel