AREWARMU DUNIYARMU ASSOCIATION OF NIGERIA

AREWARMU DUNIYARMU ASSOCIATION OF NIGERIA Arewarmu Duniyarmu Association of Nigeria is a regional non-governmental organization

*RANAR HAUSA TA DUNIYA 2026*Ina taya daukacin al’ummar Hausawa a Najeriya, Afirka da duniya murnar Ranar Hausa ta Duniya...
25/08/2026

*RANAR HAUSA TA DUNIYA 2026*

Ina taya daukacin al’ummar Hausawa a Najeriya, Afirka da duniya murnar Ranar Hausa ta Duniya, wadda za a gudanar a ranar 26 ga Agusta 2026 a fadar Mai Martaba Sarkin Hausawan Najeriya, Amb. Alh. Sani Adamu Geza Garkuwan Hausawan Duniya, a Kano.

Wannan rana tana da matukar muhimmanci, domin ba biki kawai ake yi ba; rana ce ta nuna muhimmancin harshen Hausa, tarihinsa, al’adunsa da kuma irin gudunmawar da Hausawa suke bayarwa wajen ci gaban Najeriya da Afirka.

Ina kira ga daukacin Hausawa, shugabannin al’umma, sarakuna, malamai, matasa da mata da su dauki wannan rana da muhimmanci, su halarci taron, domin kasancewa tare a irin wannan gagarumin taro na kara dankon zumunci da hadin kanmu.

Ina kuma kira ga kafafen yada labarai da su ci gaba da tallata muhimmancin harshen Hausa da al’adunmu, domin abin da ba mu kare ba, tarihi zai iya karbe shi.

A matsayina na Shugaban Majalisar Masarauta ta AREWARMU DUNIYARMU African Chiefdom and Council, ina goyon bayan duk wani shiri da zai hada kan Hausawa, ya kare al’adunmu, ya inganta harshen Hausa, tare da samar da kyakkyawar makoma ga matasanmu.

Ina taya Mai Martaba Sarkin Hausawan Najeriya murna da godiya bisa wannan babban shiri. Allah Ya sanya taron ya zama sanadin hadin kai, zaman lafiya da ci gaban Hausawa a Najeriya da duniya baki daya.

*Amb. Alh. Ibrahim Haruna*
Shugaban Majalisar Masarauta
AREWARMU DUNIYARMU African Chiefdom and Council

SANARWA TA MUSAMMAN GA DUKKAN HAKIMAIAssalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Ina roƙon dukkan Hakimai da su taimaka ...
25/08/2026

SANARWA TA MUSAMMAN GA DUKKAN HAKIMAI

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Ina roƙon dukkan Hakimai da su taimaka wajen yaɗa sanarwar Taron Ranar Hausa ta Duniya, wanda za a gudanar gobe Laraba, 26/08/2026, a Fadar Mai Martaba Sarkin Hausawan Nigeria.

Don Allah kowa ya yi amfani da dukkan kafafen sadarwar da yake da su—WhatsApp, Facebook, TikTok, X, Instagram da sauran kafafen sada zumunta—domin sanar da jama’a da kuma jawo hankalin Hausawa su halarta.

Haka kuma, ina roƙon kowane Hakimi ya sanya sanarwar a Status ɗinsa, tare da nuna goyon baya da haɗin kai ga Mai Martaba Sarkin Hausawan Nigeria da wannan muhimmin shiri na raya harshen Hausa, al’adunmu da haɗin kan Hausawa.

Wannan ba taro ne na mutum ɗaya ba ne; taro ne na dukkan Hausawa da masu kishin harshen Hausa. Don haka mu nuna haɗin kai da goyon baya ta hanyar yaɗa sanarwar da kuma halartar taron.

Allah Ya sa taron ya kasance mai albarka, Ya ƙara ɗaukaka harshen Hausa da al’adunmu, Ya kuma ƙara haɗa kan Hausawa a duniya.

Na gode da haɗin kai da goyon bayanku.

Amb. Alh. Ibrahim Haruna
Sarkin Hausawan Tukulma
Shugaba, Majalisar Masarautar Arewarmu Duniyarmu African Chiefdom and Council

25/08/2026
Muna gaiyata kowa da kowa
08/08/2026

Muna gaiyata kowa da kowa

27/07/2026

MAI GIRMA YARIMAN AFRICA A WAJEN SAUKAN KARATU ALKURA'ANI MAI GIRMA A JIHAR KANO RANAN ASABAR 25/07/2026

ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHUZuwa ga Sarakunan Hausawa, Shugabannin Ƙungiyoyin Hausawa, masu ruwa da ts...
21/07/2026

ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU

Zuwa ga Sarakunan Hausawa, Shugabannin Ƙungiyoyin Hausawa, masu ruwa da tsaki da kuma ɗaukacin al'ummar Hausawa a duniya.

Da farko, ina miƙa uzuri tare da neman afuwar kowa dangane da sauya wurin da aka tsara gudanar da Taron Hausawa na Duniya. Wannan sauyi ya biyo bayan wasu muhimman dalilai masu ƙarfi da s**a taso, waɗanda s**a sa muka ga ya dace mu sake duba tsarin gudanar da taron domin samun nasara da sauƙin halartar baƙi.

Bayan tattaunawa da yin nazari, mun cimma matsayar cewa za a gudanar da taron, da yardar Allah, a Fadar Mai Martaba Sarkin Hausawan Najeriya, da ke Kurna, Ƙaramar Hukumar Dala, Jihar Kano.

Muna roƙon kowa da ya karɓi wannan sauyi da zuciya ɗaya, tare da ci gaba da ba da haɗin kai da goyon baya kamar yadda aka saba. Wannan sauyin ba ya canza manufar taron, illa dai yana ƙara mana damar gudanar da shi cikin tsari, mutunci da nasara.

Muna gayyatar Sarakunan Hausawa, shugabannin ƙungiyoyi, malamai, masana, 'yan kasuwa, matasa da mata, da kuma duk masu kishin Hausa daga sassa daban-daban na duniya, da su halarci wannan babban taro domin haɗa kai da tattauna hanyoyin ci gaban al'ummar Hausawa.

Muna gode wa kowa da kowa bisa haƙuri, fahimta da goyon bayan da yake ba mu. Allah Ya saka da alheri, Ya haɗa kanmu, Ya albarkaci wannan taro, Ya kuma ɗaukaka Hausawa da harshen Hausa a duniya baki ɗaya.

Wassalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.

Naku:

*Amb. Alh. Ibrahim Haruna*
*(Sarkin Hausawan Tukulma)*
*National Chairman, Arewarmu Duniyarmu Association of Nigeria*
*Shugaban Majalisar Masarauta, African Chiefdom.*

13/07/2026

PRESS RELEASE
FOR IMMEDIATE RELEASE
13 Jul, 2026.

ONE YEAR REMEMBRANCE OF LATE PRESIDENT MUHAMMADU BUHARI, GCFR: SSG PAYS TRIBUTE TO A STATESMAN

The leadership and entire members of the Sardauna Support Group (SSG), on behalf of Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna (Sardaunan Gombe), solemnly commemorate the first anniversary of the passing of Late General Muhammadu Buhari, GCFR, former President of the Federal Republic of Nigeria.

As we remember his life and service to our nation, we reflect on his dedication to Nigeria and the sacrifices he made during his years in public office. His contributions to national development and public service remain an important part of Nigeria's history.

We extend our heartfelt condolences once again to the Buhari family, the Government and people of Katsina State, and all Nigerians who continue to cherish his memory.

Though he is no longer with us, his place in the history of our nation will not be forgotten.

May Almighty Allah (SWT) forgive his shortcomings, expand his grave, grant him Aljannatul Firdaus, and continue to comfort his family and loved ones.

Signed:
Rt. Comrade Muhammad Al-amin Murtala, CISSP, GCGSS
State Secretary General
Sardauna Support Group (SSG)

For:
Hon. Ali Mohammed Inuwa
Director General
Sardauna Support Group (SSG)

SANARWA ZUWA GA DUKKAN MAGOYA BAYA DA AL'UMMAR NIGERIAAssalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.A madadin Kungiyar ...
12/07/2026

SANARWA ZUWA GA DUKKAN MAGOYA BAYA DA AL'UMMAR NIGERIA

Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.

A madadin Kungiyar Arewarmu Duniyarmu Association of Nigeria, muna miƙa godiya ta musamman ga ɗaukacin magoya bayanmu da al'umma bisa irin goyon baya, ƙauna da haɗin kai da kuke ci gaba da ba mu.

Muna sanar da jama'a cewa har zuwa wannan lokaci, ƙungiyarmu ba ta tantance ko amince da wani ɗan takara ba a kowane matakin zaɓe. Don haka, duk wani labari da ake yaɗawa cewa mun goyi bayan wani ɗan takara ko mun ce a zaɓe shi, ba gaskiya ba ne, kuma ba ya wakiltar matsayar ƙungiyarmu.

Da zarar mun kammala tantance 'yan takara bisa nagarta, gaskiya, riƙon amana da kuma manufofin da za su amfani al'umma, za mu fito a hukumance mu sanar da jama'a wanda ƙungiyarmu ta amince da shi. Bayan haka, za mu gudanar da cikakken yaƙin neman goyon baya da wayar da kai a gare shi a duk inda ya dace. Haka kuma, idan mun amince da 'yan takara a matakan jihohi da sauran mukamai, za mu sanar da jama'a tare da ba su cikakken goyon baya.

Muna roƙon al'umma da su yi watsi da duk wata jita-jita, su riƙa jiran sanarwar hukuma daga shugabancin ƙungiyarmu.

Allah Ya saka muku da alheri bisa irin kulawa, goyon baya da haɗin kai da kuke ci gaba da ba mu. Muna addu'ar Allah Ya ba Najeriya zaman lafiya, haɗin kai da shugabanni nagari.

Na ku har kullum,

Amb. Alh. Ibrahim Haruna
(Sarkin Hausawan Tukulma)
Shugaba, Arewarmu Duniyarmu Association of Nigeria
Shugaba, Majalisar Masarauta ta African Chiefdom

☎️ 08035004217
☎️ 08026876477

🌍🤝 KU SHIGO MU GINA AL'UMMARMU TARE! 🤝🌍AREWARMU DUNIYARMU ASSOCIATION OF NIGERIA tana gayyatar duk masu kishin haɗin kai...
12/07/2026

🌍🤝 KU SHIGO MU GINA AL'UMMARMU TARE! 🤝🌍

AREWARMU DUNIYARMU ASSOCIATION OF NIGERIA tana gayyatar duk masu kishin haɗin kai, zaman lafiya, da ci gaban al'umma su shiga wannan babbar ƙungiya.

MANUFOFINMU:
✅ Haɗa kan al'umma.
✅ Ƙarfafa zumunci da taimakon juna.
✅ Tallafa wa mabukata da bunƙasa rayuwar al'umma.
✅ Haɗa hannu da sarakunan gargajiya, shugabanni, matasa da mata wajen kawo ci gaba.

💳 Kudin Fom ɗin Shiga: ₦10,000 kacal.

Haka kuma, idan kana da wani mutum mai muhimmanci, mai taimakon al'umma, ko shugaba nagari da ya cancanci karramawa, za ka iya gabatar da shi domin shiga AFRICAN CHIEFDOM.

A AFRICAN CHIEFDOM babu tsayayyen kuɗin fom. Gudummawar da mutum zai bayar tana bisa ƙarfinsa da niyyarsa ta tallafawa ayyukan ci gaban al'umma.

📍 Muna da wakilai da ofisoshi a kowace jiha a Najeriya domin sauƙaƙa rajista da tuntuɓa.

📞 Domin ƙarin bayani ko yin rajista, a kira:
☎️ 08035004217
☎️ 08026876477
☎️ 07019414448

Ka shiga yau, ko ka gayyaci wani. Haɗin kai shi ne ginshiƙin ci gaban al'umma.

AREWARMU DUNIYARMU ASSOCIATION OF NIGERIA

"Haɗin Kai • Taimakon Juna • Ci Gaban Al'umma."

Address

Magadushu
Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AREWARMU DUNIYARMU ASSOCIATION OF NIGERIA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to AREWARMU DUNIYARMU ASSOCIATION OF NIGERIA:

Shortcuts

Share