Khayry AHB Humanity Aid Initiative

Khayry AHB Humanity Aid Initiative Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Khayry AHB Humanity Aid Initiative, Non-Governmental Organization (NGO), Plateau jos, Jos.

A yau 27 ga watan Ramadan wannan shekarar   tayi rabon abincin iftar na karshe a bana domin mu fuskanci shirin hidimar s...
27/03/2025

A yau 27 ga watan Ramadan wannan shekarar tayi rabon abincin iftar na karshe a bana domin mu fuskanci shirin hidimar sallah. ayau ne kuma Ummu Saleem ta bayar da sadakar ruwan sha aka hada da abincin. Mun yi wannan rabon ne a Unguwar Zinariya karshen kwalta.

Muna miƙa godiya marar misaltuwa ga ɗaukacin al'ummar da suke bamu gudunmawa/taimako ta ko wacce hanya.

Fatan ALLAH Ya karba mana Ya cika mana ladar da Ya ke ba masu ciyar da mutanen da s**a yi azumi. AMEEN.

Alhamdulilah cikin ikon Allah mu samu ziyartar Butcher line da project dinmu na Feed The Needy karkashin kungiyar   , mu...
26/03/2025

Alhamdulilah cikin ikon Allah mu samu ziyartar Butcher line da project dinmu na Feed The Needy karkashin kungiyar , muna mika godiya dayawa da Adam na Ali da Adamu Baba domin kokarinsu na ganin aikin ya tafi lafiya ,harma da kokarin dawo damu gida. Allah yasa mana amizanin lada baki daya.

A ci gaba da rabon abinchinmu na shan ruwa mai taken “Feed The Needy” na ƙungiyar   yau mun samu damar ziyartar anguwar ...
24/03/2025

A ci gaba da rabon abinchinmu na shan ruwa mai taken “Feed The Needy” na ƙungiyar yau mun samu damar ziyartar anguwar Nepa domin ciyar da masu azumi mabuƙata na wannan anguwa

yasa mana a mizanin aikin lada sannan ya sakawa kowa da mafificin alkhairi 👏🏼

Allah cikin ikonsa ya kaimu layin Idi mai Barkono domin rabon abincin sadaka as usual a karkashin    Allah ya kara taima...
21/03/2025

Allah cikin ikonsa ya kaimu layin Idi mai Barkono domin rabon abincin sadaka as usual a karkashin

Allah ya kara taimaka mana cikin nufin Mu da ayyukan mu.

Ziyarar rabon abincin mu na Ramadan Feed The Needy karkashin    yai a Sabon Layi  mukayita muna godiya ga Albani JR Jos ...
20/03/2025

Ziyarar rabon abincin mu na Ramadan Feed The Needy karkashin yai a Sabon Layi mukayita muna godiya ga Albani JR Jos bisa kokarinsa koda yaushe.

Har yanzu kofa abude take domin saka taimako ku ko kuma shawarwari. Masu bada taimako zasu saka a 9025614713 Opay Abdulmumin Ummulkhair ko kiranmu a 09025614713 Allah ya saka da khairan.

  ta ziyarci unguwar tudun fera domin gabatar da shirin RAMADAN FEED THE NEEDY a yammacin Yau. Godiya mai yawa ga matasa...
19/03/2025

ta ziyarci unguwar tudun fera domin gabatar da shirin RAMADAN FEED THE NEEDY a yammacin Yau. Godiya mai yawa ga matasan wannan anguwa domin haɗin kai da s**a bamu.

Muna addu'ar ALLAH Ya datar da mu ciki dukkanin ayukan mu Ya sa muna cikin amintattatun bayin Shi. AMEEN.

Call @ 09025614713 for enquiry

Mun isa unguwar layin lasisi a yammacin Yau da shirin mu na RAMADAN FEED THE NEEDY domin rabon abincin iftar ga mutum 10...
18/03/2025

Mun isa unguwar layin lasisi a yammacin Yau da shirin mu na RAMADAN FEED THE NEEDY domin rabon abincin iftar ga mutum 100 k**ar yadda muka saba.

Muna kara godiya kwarai ga Ukasha Maifada Adamu da sauran tan uwa domin kokari su a yau da kuma gare ku bisa addu'oi, taimako da fatan Alkhairi da kuke mana. ALLAH Ya fi mu yabawa. AMEEN.

Call @ 09025614713

Munyi rabon abinchin iftar da gidauniyar   ke gabatarwa a gidanmu dake kwanar shagari a yau.Hakan na da alaƙa da karanci...
16/03/2025

Munyi rabon abinchin iftar da gidauniyar ke gabatarwa a gidanmu dake kwanar shagari a yau.

Hakan na da alaƙa da karancin kudin da ke a hannunmu da muke biya na NAPEP a kullum idan mun fita. Muna sa ran cigaba da zuwa unguwanni domin rabon da zarar mun ƙara samun damar haka.

Fatan ALLAH Ya karɓa daga gare mu baki ɗaya. AMEEN.

Domin tallafawa zaku iya amfani da 9025614713, Opay ko kuma kira a 09025614713.

IFTAR MUBARAK

  ta ziyarci gidan gyara hali na Jos (JOS PRISON) domin rabon abincin iftar ga ƴan uwan mu da ke tsare a gidan.A ziyarar...
15/03/2025

ta ziyarci gidan gyara hali na Jos (JOS PRISON) domin rabon abincin iftar ga ƴan uwan mu da ke tsare a gidan.

A ziyarar mu ta yau munga yadda mutan gidan ke cike da buƙatu, k**a daga ruwan sha zuwa abinci domin samun gudanar da Wannan ibada ta azumin Ramadana cikin sassauci. Game da haka muke ƙara kiran neman gudunmawar ku domin ci gaba da wannan shirin namu na RAMADAN FEED THE NEEDY dake tanadar abincin iftar ga mutum 100 a kullum.

Domin saka naka jarin yi amfani da 9025614713, opay ko kuma kiran mu a 09025614713.

ALLAH Ya karɓa mana Ya iyyar mana baki ɗaya. AMEEN.

Rabon abincin iftar da   keyi yau an yi shine a unguwar Layin KyanciWannan aiki yana gudana ne da gudunmawarku na taro d...
14/03/2025

Rabon abincin iftar da keyi yau an yi shine a unguwar Layin Kyanci

Wannan aiki yana gudana ne da gudunmawarku na taro da sisi da kuke bamu. Har a yanzu muna ƙara neman wannan gudunmawar domin cikan burin hadafin shirin na kaiwa ga ƙarshen watan Ramadan.

Yi amfani da Opay ɗinmu 9025614713, domin sanya na ka/ki gudummawar komi kankantar shi domin mu hadu a ladar baki ɗaya.

ALLAH Ya karba mana Ya kuma iyyar mana. AMEEN.

Shirin RAMADAN FEED THE NEEDY na gidauniyar   ya ziyarci layin Muhammadu Borno domin rabon abincin iftar a yammacin Yau....
13/03/2025

Shirin RAMADAN FEED THE NEEDY na gidauniyar ya ziyarci layin Muhammadu Borno domin rabon abincin iftar a yammacin Yau.

Muna kara miƙa godiya ga Malama Amina Haruna Miloniya na ƙoƙarinki na yau da ɗaukacin al'ummar dake taimaka mana ta ko wacce hanya domin nasarar wannan aiki. Fatan ALLAH Ya haɗamu a ladan baki ɗaya AMEEN.

For more information call @ 09025614713.

A Unguwar Rikkos kusa da Nababa car wash yau muka yada zongo domin rabon abincin iftar ga mutane 100 da gidauniyar    ke...
12/03/2025

A Unguwar Rikkos kusa da Nababa car wash yau muka yada zongo domin rabon abincin iftar ga mutane 100 da gidauniyar ke gudanarwa cikin watan Ramadan. Mustapha Abdullahi Bebeji Allah saka maka da alkhairi bisa kokarinka.

Muna addu'ar ALLAH Ya karɓa mana ibadun mu Ya sa muna cikin bayin shi da s**a samu Rahamar shi a cikin wannan watan.

Domin tuntubar mu ko saka naka jarin a neme mu a 09025614713.

Address

Plateau Jos
Jos

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Khayry AHB Humanity Aid Initiative posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share