08/05/2026
Kamar Yadda Ɗan Uwa Yayi Tambaya Jiya, Alhamdulillah Ya Gamsu Da Hujjar, Sannan Ya Nemi Ƙarin Bayani Kan Yin Zikirin Anfāsu Da Numfashi.
Ga Ƙarin Hujja Akan Zikirin Anfasu Da Yinsa Da Numfashi:
Faɗin Ubangiji Maɗaukakin Sarki:
﴿وَإِنْ مِنْ شَيْءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمْدِهِ وَلَٰكِنْ لَا تَفْقَهُونَ تَسْبِيحَهُمْ﴾
Ma’ana:
“Babu Wata Halitta Face Tana Tasbihi Da Yabon Ubangijinta, Sai Dai Ku Ba Kwa Fahimtar Tasbihin Nasu.”
Kamar Yadda Wannan Aya Tayi Bayani Cewa Babu Wani Abu Da Baya Ambaton Allah, Sai Dai Ku Ne Ba Kwa Fahimtar Tasbihin Nasu.
Numfashi Ma Yana Cikin Halittun Allah, Saboda Haka Shima Yana Tasbihi, Shi Yasa Ake Yin Zikiri Da Numfashi.
Dalilin Gudanar Da Zikiri A Yanayin Numfashi Kuwa Shi Ne Domin A Yawaita Zikiri, Kamar Yadda Allah Maɗaukakin Sarki Yayi Umarni Da A Riƙa Yawan Ambatonsa.
﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا﴾
Ma’ana:
“Ya Ku Waɗanda S**a Yi Imani! Ku Yawaita Ambaton Allah Sosai.”
Idan An Yi Da Harshe, Sai Kuma A Yi Da Numfashi Domin A Ƙara Yawaita Zikiri, Saboda Yi Da Iya Harshe Yakansa A Gaji Da Wuri, Shiyasa Idan Anyi Da Harshe Sai Kuma Ayi Da Numfashi, Bisa La’akari Da Ayar Da Ta Nuna Cewa Komai Yana Tasbihi Ga Allah.
Abin Da Ake Faɗa Da Numfashi “Lā Ilāha Illallāh” Ita Ce Dai Ake Maimaitawa Da Numfashi, Ba Wani Abu Daban Ba. Duk Zikirin Da Ake Yi Da Harshen Baki Ana Iya Sarrafa Shi Da Numfashi.
Allah Shine Mafi Sani.
__Bashir Musa Mustapah
__Juma'a 8/5/2026.